A ranar Lahadi da ta gabata ce aka fara fafata Gasar Cin Kofin Afirka a birnin Yaounde na kasar Kamaru, inda mai masaukin baki, Kamaru ta doke Burkina Faso da ci biyu da daya a wasan farko.
A ranar Talata ce Najeriya za ta fara buga wasa a gasar, inda za ta goge raini da kasar Misra a wani da ake ganin mai zafi ne.
Wannan ya sa Aminiya ta zakulo ’yan wasan Najeriya da asalinsu ‘yan Arewa daga cikin ’yan wasan kasar da suke Kamaru a yanzu haka.
Zaidu Sanusi: Kungiyar FC Porto
Zaidu dan asalin Jihar Kebbi ne da ke wasa a kungiyar FC Porto da ke Portugal, inda yake buga baya ta gefen hagu.
Dan asalin garin Jega ne, kuma shekarunsa 24.
Sadiq Umar: Kungiyar UD Almeria
Sadiq dan asalin Jihar Kaduna ne da ke wasa a yanzu haka a kungiyar UD Almeria da ke rukuni na biyu na kasar Spain.
Yana cikin ’yan wasan Najeriya da suke lashe tagulla a gasar Olympic ta shekarar 2016. Shekarunsa 24.
Ahmed Musa: Fatih Karagümrük
Ahmed Musa fitaccen dan wasan Najeriya da a yanzu yake wasa a kungiyar Fatih Karagümrük ta Turkiyya.
Dan asalin Jihar Kano ne da ya taso a garin Jos da ke Jihar Filato. Shi ne kyaftin din tawagar Super Eagles a yanzu haka.
Simon Moses
Moses wanda aka fi sani da Ajala a Jihar Kaduna, dan asalin Jihar Binuwei ne da aka haifa a Jos, amma ya girma a Kaduna.
Ya fara taka leda ne a Jihar Kaduna, a barikin NDA. Yanzu haka yana wasa ne a kungiyar Nantes da ke Faransa.