✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON U-17: An kori Kyaftin din Golden Eaglets saboda yawan shekaru

A kokarin hayewa gasar cin Kofin Afirka na ’Yan kasa da shekara 17, Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta dakatar da Kyaftin din kungiyar…

A kokarin hayewa gasar cin Kofin Afirka na ’Yan kasa da shekara 17, Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta dakatar da Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Golden Eaglets saboda samunsa da laifin yin coge a shekarunsa.

A wani binciken na’ura da hukumar ta gudanar a ranar Talatar da ta gabata lokacin da Najeriya ke gab da yin wasa da Burkina Faso, an gano dan kwallon ya yi karyar shekaru, kuma bayan an yi amfani da na’urar da ke tantance yawan shekarun ’yan kwallo (MRI) ne aka gano shekarun Kyaftin din sun wuce ya buga wa kungiyar Golden Eaglets kwallo.

Nan take hukumar ta bayar da umarnin a cire sunan dan kwallon daga jerin wadanda za su fafata a gasar.

kasar Nijar ma mai masaukin baki da Jamhuriyyar Benin da Burkina Faso duk sun rasa wadansu dga cikin ’yan kwallonsu bayan an yi musu gwaje-gwajen shekaru.

Wasannin za su gudana ne a Niamey da ke Jamhuriyyar Nijar.