✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

AFCON: Muna neman gafarar ’yan Najeriya —Ahmed Musa

Mun yi kokarin mu dari bisa dari, amma tasirin kokarin bai kai ga mun samu nasara ba.

Dan wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya, Ahmed Musa ya nemi gafarar ’yan Najeriya dangane da gazawar da tawagarsu ta yi wadda ta janyo musu ficewa daga gasar cin kofin Afirka da ke gudana a kasar Kamaru.

Musa wanda ke goya goma da kyaftin, ya nemi ’yan Najeriya da su dauki rashin nasarar da tawagar Super Eagles ta yi a karawa da kasar Tunisia a matsayin kaddara.

A sakon da ya aike wa ’yan Najeriya a shafinsa na Twitter, Musa ya ce a rayuwa ba koda yaushe ake samun abinda ake so ba, saboda haka ya dace a yi hakuri a kai.

Musa ya ce dama a rayuwa ba kowanne lokaci mutum ke samun yadda ya ke so ba, yana mai cewa sun yi iya kokarinsu a wasan sai dai duk da haka hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
“A rayuwa, ba kowanne lokaci bane muke samun abin da muke so kuma wannan lamari ne da ya kamata mu yarda da shi komai dacinsa.
“Mun yi kokarin mu dari bisa dari, amma tasirin kokarin bai kai ga mun samu nasara ba,” a cewar Musa.

Musa ya ce ba za suyi kasa a gwiwa ba a gasa ta gaba, yayin da ya godewa ’yan Najeriya a kan irin goyan baya da addu’oin da suka yi ta musu.

Kazalika, dan wasan Najeriya mai buga tsakiya, Alex Iwobi shi ma ya wallafa sako a shafinsa na Twitter yana bawa magoya bayansa hakuri kan cire su daga gasar AFCON.

Bayan kammala wasan, wasu magoya baya sun rika nuna bacin ransu a dandalin sada zumunta suna cewa laifin Iwobi ne da golan tawagar Super Eagles, Maduka Okoye.

An dai rika jingina wa Iwobi laifi saboda karbar katin sallama bayan alkalin wasan ya dauki tsokane idon da da ya yi wa Youssef Mskani da hannunsa na dama a matsayin keta.

Kasar Tunisia dai ta doke Najeriya da ci 1-0 a zagaye na biyu na gasar cin kofin Afirka da ke gudana a Kamaru, abinda ya yi sanadiyar fitar kasar daga gasar.

Yadda Najeriya ta fice daga gasar AFCON 2021

A ranar Lahadin da gabata ce dai aka y waje-rod da ’yan wasan tawagar Najeriya ta Super Eagles bayan karawar da suka yi da Tunisia a gasar cin Kofin Afirka ta AFCON da ke gudana a Kamaru.

Ci daya mai ban haushi da tawagar Carthage Eagles ta Tunisia ta yi wa Super Eagles ta hannun Youssef Msakni a minti na 47 ne ya ba ta damar samun nasarar wucewa zagaye na gaba a gasar AFCON 2021.

Sai dai a yayin wasan, Alex Iwobi mai buga tamaula a kungiyar Everton da ke buga gasar Firimiyar Ingila, ya karbi katin sallama bayan ketar da alkalin wasan ya yanke hukuncin cewa ya yi a daidai lokacin da bai wuce minti biyu ba da shigarsa wasan, bayan ya canji Kelechi Iheanacho a minti na 59.

Da wannan sakamako, Tunisia ce za ta fafata da tawagar The Stallions ta Burkina Faso a ranar Asabar, 29 ga watan Janairu wadda ita ma ta yi nasarar tsallakawa zuwa zagayen gab da na biyun karshe a gasar bayan ta kora tawagar Gabon gida a bugun fenareti.

Ana iya tuna cewa, Najeriya ce ta jagoranci rukuni na hudu da maki tara, yayin da Tunisia ta tsallake da kyar wadda aka yi gata bayan ta zo matsayi na uku da maki uku a rukuni na shida.

Kasashen biyu sun hadu a wasan neman na uku a gasar AFCON da aka fafata a kasar Masar a 2019, inda Najeriya ta yi nasara da ci 1-0.

Sau shida ke nan a tarihi Najeriya tana haduwa da Tunisia a gasar, kuma bata taba shan kaye ba sai a wannan karo da wasu ke ganin cewa Tunisian ta yi wa Najeriya abin da masu iya magana kan ce raina kama ka ga gayya.

A yanzu dai Tunisia ce za ta buga wasan Quater Final a Garoua tare da Burkina Faso ranar Asabar.