Hukumar Kula da Ma’aikata a Buea, babban birnin yankin Kudu maso Yamma na Kasar Kamaru, ta tilasta wa ma’aikatan gwamnati da su rika halartar gasar cin kofin kasashen Afirka da ke gudana yanzu haka a kasar.
Hakan dai ya biyo bayan umarnin da gwamnan yankin ya bayar, kamar yadda magajin garin ya nuna cewa halartar filin wasan wajibi ne ga kowa.
- Matar Aure: Rahama Sadau za ta saki sabon shirin mai dogon zango
- An bude makarantu a Zamfara bayan wata hudu
Matakin ya zo ne bayan an buga wasanni da dama a garin Limbe inda mutane kadan ne suka shiga filin domin kallon wasan.
BBC ya ruwaito cewa, mazauna yankin na Buea da dama na fargabar samun arangama tsakanin ’yan aware da sojoji.
’Yan awaren wadanda suka kaddamar da yaki da gwamnati shekara biyar da ta gabata sun yi barazanar kawo tsaiko a wasannin, amma gwamnati ta tabbatar da samar da tsare.
Birane da dama sun samar da motocin bas-bas da kananan motoci don ba wa mutane da yawa damar halartar wasannin.
Ana iya tuna cewa tun a ranar Asabar ce gwamnatin kasar Kamaru ta rage sa’o’in da za a shafe a wuraren aiki.
Ma’aikata a ofisoshin gwamnati da ma’aikatu sun fara tashi daga aiki daga karfe biyu na rana daga ranar Litinin, yayin da ake tashi daga makarantu da karfe daya.