Gwamnatin Senegal ta bai wa ’yan wasan ta da suka lashe gasar cin Kofin Afirka ta AFCON 2021 kyautar kudade da kuma filaye domin nuna farin cikin ta da nasarar da suka samu.
Yayin wani biki a fadar shugaban kasa, Shugaba Macky Sally a bayyana cewar kowanne dan wasa zai karbi Dala 87,000 tare da fili mai murabba’in mita 200 a birnin Dakar da wani mai murabba’in mita 500 a birnin Diamniadio.
- Matsalar kashe-kashe don yin tsafi ta fusata Majalisar Wakilai
- Matsalar tsaro: Fintiri ya hana hawa babura a kananan hukumomi 2
Shugaba Salla ya ce babu yadda za su iya bayyana farin cikinsu ga ’yan wasan, yayin da ya roki jagoransu, Aliou Cisse da ya kai kasar matakin kusa da na karshe na gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a Qatar a badi.
Haka kuma Shugaba Macky Sall ya kuma girmama tawagar da lambar yabo ta Order of the Lion.
Tawagar Senegal dai ta doke ta Masar da ci 4-2 a bugun finareti, wanda hakan ya ba ta damar lashe kofin a karon farko a tarihi.