Shugaban Jam’iyyar Action Democratic Party (ADP) na kasa, Alhaji Yabagi Yusuf Sani ya yi watsi da kiran da tsohon Shugaban Kasa Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya yi na tsarin kafa jam’iyyu biyu a Najeriya.
Ya bayyana tsarin jam’iyyun biyu a matsayin hanyar da ba za ta bayar da damar sharbar romon dimokuradiyya ba a kasar.
A rabar Asabar ce tsohon shugaban kasar yayin wata hira da gidan talabijin na ARISE ya ba da shawarar cewa tsarin jam’iyyu biyu zai fi dacewa ga dimokuradiyyar Najeriya.
A wani taron manema labarai a Kaduna, Yabagi wanda ya yi takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar ADP a shekarar 2019, ya ce dole ne a kyale jam’iyyun siyasa marasa rinjaye su fadi ra’ayinsu a dimokuradiyyar Najeriya.
“Ban aminta da tsarin kafa jam’iyyu biyu ba saboda dimokuradiyya mu ke yi.
“Shugaba Babangida yana magana ne kan wani tsarin mulki na daban wanda ya gudanar a lokacinsa.
“Ya dai bayyana ra’ayinsa game da tsarin, amma game dimokuradiyya ba shi da gurbi.
“Ana kyale ‘yan kasa ne su yi tarayya tare da damar fadin albarkacin baki.
“Bai kamata a yi tunanin kawo irin wannan tsari ba don baya daga cikin abin da dimokuradiyya za ta aminta da shi,” in ji shi.
Sai dai dangane da yadda jam’iyyar APC da PDP suka mamaye manyan kujeru a zabuka, ya ce kowa zai iya kallon tsarin a matsayin na jam’iyyu biyu amma abun ba haka ya ke ba
Yabagi ya ce an kafa ADP ne don kubutar da Najeriya da ‘yan Najeriya daga matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro da ta ke fama da su.
A cewarsa, nan ba da jimawa ba jam’iyyar za ta karbi manyan ‘yan siyasa a cikin jam’iyyar domin kawo mafita a 2023.
Daga karshe ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su bi kadin masu rika da madafan iko kan yadda suke gudanar da mulkin kasar.
Ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi kokarin kare martabarsa kafin cikar wa’adin mulkinsa saboda ‘yan Najeriya ba su yi tsammanin abin da suke gani daga gare shi ba, inda ya ce Allah bai halicci ‘yan Najeriya don su wahala ba.