✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ADP ta kori dan takararta na Gwamna a Jigawa, ta bukaci a zabi PDP

ADP ta kuma bukaci 'yan jihar su zabi dan takarar PDP

Jam’iyyar ADP a Jihar Jigawa ta kori dan takararta na Gwamna, Muhammed Gumel, saboda zargin cin amanar jam’iyya.

Mai rikon mukamin shugaban jam’iyyar a Jihar, Kabiru Hussaini ne bayyana haka lokacin da yake jawabi ga manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar.

Ya kuma roki magoya bayan jam’iyyar tasu da su zabi dan takarar Gwamna na jam’iyyar PDP, Mustapha Sule Lamido, saboda ya ce shi ne kadai zai iya ceto Jihar daga durkushewa.

“Muna umartar magoya bayanmu da su zabi dan takarar PDP, saboda jam’iyyar kadai ce za ta iya ceto Jiharmu,” in ji shi.

Rahotanni dai sun ce dan takarar jam’iyyar ta APC ya sanar da yin watsi da takarar tasa, inda ya koma goyon bayan jam’iyyar APC mai mulki.

Sai dai da yake mayar da martani a kan lamarin, dan takarar ya ce sam Shugaban jam’iyyar ba shi da hurumin korarsa daga ADP.

Muhammed Gumel ya kuma ce shi kansa Shugaban sai da uwar jam’iyyar ta kasa ta sanar da korarsa a ranar 22 ga watan Satumban 2022, kuma hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da jami’an tsaro ba su san da zamansa ba.