Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa Ministan Kudi, Misis Kemi Adeosun ta dauki matakin dakatar da shugaban hukumar hada-hadar hannayen jari, Mounir Gwarzo saboda ya nemi Ministar ta bashi ummarnin dakatar da binciken kamfanin mai na Oando a rubuce.
Takardun da Aminiya ta samu daga majiya mai tushe jiya cewa Adeosun ta ce ta ba shi ummanir ne a matsayinta na memban zartarwar hukumar kuma shi kan shi shugaban kasan da ya nemi ta datakar da binciken bai ba ta ummarni a rubuce ba.
Amma da Gwarzo ya dage sai ta bashi ummarnin a rubuce sai Ministar ta ce shi ma tana da zarge-zargen cin hanci da rashawa da aka rubuta a kansa kuma idan bai bi ummarninta ba za ta dakatar da shi don a samu damar bincikensa.