✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ademola Adeleke: Bayanai game da zababben Gwamnan Osun

Adeleke ya lallasa dan takarar jam'iyyar APC kuma gwamna mai ci a Osun.

Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP, shi ne dan takarar da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan Jihar Osun.

A ranar Asabar ne aka gudanar da zaben gwamnan mai cike da tsauraran matakan tsaro.

Babban Baturen Zaben Jihar, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, ya ce Sanata Adeleke ya samu kuri’u 403,371, yayin da Gwamna mai-ci, Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC ya zo na biyu da kuri’u 375,027.

Bayanan da INEC ta fitar na kananan hukumomi 30 da ke jihar sun nuna cewa PDP ta yi nasara a 17 daga cikinsu yayin da APC ta samu kananan hukumomi 13.

A 2018, sun fafata da juna, inda dan takarar APC, Gboyega Oyetola, ya kayar da dan takarar PDP, Ademola Adeleke.

Zababben gwamnan, mai shekara 62, dan asalin Karamar Hukumar Ede ne.

Ya wakilci yankin Osun ta Yamma a Majalisar Dattawan Najeriya karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party daga 2017 zuwa 2019.

Ya tsaya takarar Sanata ne bayan rasuwar dan uwansa Sanata Isiaka Adeleke.

A shekarar 2018 ya tsaya takarar gwamnan Jihar Osun amma ya sha kaye a hannun Mista Oyetola.

Adeleke ya fara karatun firamare ne a makarantar Methodist Primary School da ke Surulere a Jihar Legas; Daga nan ya koma Tsohuwar Jihar Oyo ya halarci makarantar firamare ta Nawarudeen da ke Ikire.

Ya ci gaba da karatunsa a Makarantar Sakandare ta The Seventh Day Adventist, Ede a tsohuwar Jihar Oyo sannan ya koma Ede Muslim Grammar School, inda ya kammala karatunsa na sakandare kafin komawarsa Amurka.

Ya kammala Digirinsa na farko ne a fannin nazarin aikata laifuka a Kwalejin Atlanta Metropolitan State College da ke Amurka.

Adeleke dan kasuwa kuma ya yi aiki a tsakanin 2001 zuwa 2016, inda ya kasance Babban Darekta a kamfanin yayansa, Pacific Holdings Limited. Kafin ya soma aiki a Pacific Holdings Limited, Ademola ya yi aiki tare da Kamfanin Quicksilver Courier da ke garin Atlanta na Jihar Jojiya a kasar Amurka, a matsayin dan kwangila.