Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana Sanata Ademola Adeleke na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Osun.
Babban Baturen Zaben INEC, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe ya bayyana cewa, Adeleke da jam’iyyarsa sun yi nasarar ce da kuri’a 403,371 a zaben na ranar Asabar.
- ’Yan Najeriya kukan dadi suke yi —Buhari
- Zaben Osun: Masu zanga-zanga sun taru a matattara sakamako
- Yadda mutane ke neman masu sayen kuri’unsu a zaben Gwamnan Osun
Babban abokin hamayyarsa kuma gwamna mai ci, Gboyega Oyetola na Jam’iyyar APC, shi ne ya zo a matsayi na biyu da kuri’a 375,027.
Karo na biyu
Karo na biyu ke nan da manyan ’yan takarar suke yin karon battar neman kujerar Gwamnan Jihar Osun.
A 2018, sun fafata da juna, inda dan takarara APC, Gboyega Oyetola, ya kayar da dan takarar PDP, Ademola Adeleke.
Zakaran gwajin dafi
Ana ganin zaben a matsayin wanda zai nuna irin farin jinin jam’iyyun siyasa gabanin zaben 2023.
Zaben dai shi ne na farko bayan jam’iyyu sun tsayar da ’yan takararsu na shugaban kasa gabanin zaben 2023.
Haka kuma, yana gudana ne yankin dan takarar shguaban kasa na Jam’iyyar APC mai mulki, Sanata Bola Tinubu, wanda ke da karfin fada a ji a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
Bugu da kari, daga Jihar Osun Sakataren Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Iyola Omisore, ya fito.
Ga shi kuma tsohon gwamnan jihar, Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, yana zaman doya da manja da bangaren Gwamna Oyetola da kuma Tinubu.
A bangare guda kuma, Sanata Adeleke na neman huce haushinsa na darewa kan kujerar, bayan kayen da ya sha a hannun Oyetola a 2018, duk kuwa da cewa zagayen farko na zaben shi ne a kan gaba.
Zaben nasu su na 2018 shi ne ya fara kafa tarihin zaba mai wanda bai kammalu ba, sai da aka kai ga zagaye na biyu.
Haka kuma ana ganin jama’ar jihar sun gaji da kamun ludayin gwamnatin Oyetola da APC a matakin jiha da ma kasa baki daya.