✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adebayor ya gina sabuwar hanya a garinsu

Tsohon dan kwallon kulob din Arsenal da ke Ingila dan asalin Togo Emmanuel Adebayor ya gina wata sabuwar hanya a garinsu da ke Togo. |dan…

Tsohon dan kwallon kulob din Arsenal da ke Ingila dan asalin Togo Emmanuel Adebayor ya gina wata sabuwar hanya a garinsu da ke Togo.

|dan kwallon ne da kansa ya sanar da haka a shafin sadarwarwa na Instagram a ranar Litinin da ta gabata, inda ya tura wani faifan bidiyo mai dauke da sako da ke nuna yadda Adebayor tare da wasu abokansa suke bin kan hanyar a kasa suna tika rawa saboda murna.

Adebayor wanda ya ce tun yana karami yake da burin gina wannan hanya, ya yi matukar murna yanzu da burin nasa ya cika.

dan kimanin shekara 33 Adebayor, yanzu haka yana kwallo ne a kulob din Istanbul Basaksehir da ke Turkiyya bayan ya koma kulob din tun a shekarar 2016,  kawo yanzu ya samu nasarar zura wa kulob din kwallaye 21 a kakar wasa ta bana.

Sai dai Adebayor yana neman shawarar jama’a ne a game da sunan da ya dace ya sanya wa sabuwar hanyar da ya gina.

“Ina neman shawararku a game da sunan da ya fi dacewa na sanya wa sabuwar hanyar da na gina a Togo”, inji shi.

Sai dai Adebayor bai bayyana nisan hanyar ko yawan kudin da ya kashe wajen ginata ba, amma dai alamu sun nuna hanyar za ta kai nisan kilomita biyu da hakan ya nuna ba karamin kudi ya kashe wajen ginata ba.

Idan za a tuna a kwanaki ma Adebayor ya baza hoton katafaren gidan da yake zaune tare da iyalansa a Togo, kuma gida ne da aka kashe masa makudan kudi.