✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Addu’ar rasuwar Halifan Tijjaniyya da aka yi a Legas cikin hotuna

Zawiyar Darikar Tijjaniyya ta shaikh Mukhtar Danlami Imamul Faila da ke Agege a Legas ta shirya addu’a ta musamman ga Halifan Tijjaniya Shaikh Ahmad Tijjani…

Zawiyar Darikar Tijjaniyya ta shaikh Mukhtar Danlami Imamul Faila da ke Agege a Legas ta shirya addu’a ta musamman ga Halifan Tijjaniya Shaikh Ahmad Tijjani Ibrahim Inyass  wanda Allah Ya yi wa rasuwa a makon jiya, tare da kaninsa Shaikh Mukhtar Ibrahim Inyass wanda ya rasu mako guda da rasuwar yayan.

An gudanar da saukar karatun Alkur’ani Mai Girma tare da addu’oi da ambaton Allah domin nema masu rahamar Allah tare da addu’ar zaman lafiya ga Jihar Legas da ma kasa baki daya.

Aminiya ta kawo muku hotunan yadda addu’ar ta gudana a unguwar Gwagulori da ke Agege, a Legas.