✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Addu’a (9)

Yin fushi Godiya ga Ubangiji Allah domin yawan kaunarSa zuwa gare mu. Barkanmu da sake saduwa a cikin wannan mako inda za mu tattauna a…

Yin fushi

Godiya ga Ubangiji Allah domin yawan kaunarSa zuwa gare mu. Barkanmu da sake saduwa a cikin wannan mako inda za mu tattauna a kan halin fushi.

Fushi wani hali ne a cikin rayuwar dan Adam da ke nuna tsananin bacin ran mutum game da wani abu, yanayin da ya tarar da kansa a ciki, ko wani abin da wani ya yi masa da ba daidai ba. Fushi abu ne da kowannenmu ke yi a lokuta da dama. Mukan tambayi kanmu sau da dama cewa ko fushi zunubi ne? Bari mu ga abin da Littafi Mai tsarki ke fadi game da wannan batu. 

“In kun fusata, kada ku yi zunubi, kada ma fushinku ya kai faduwar rana, kada kuma ku bar wa Iblis wata kofa. Kada barawo ya kara yin sata, a maimakon haka sai ya motsa jiki yana aikin gaskiya da hannunsa, har da zai samu abin da zai ba matalauta. Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganar da ta kyautu domin ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, domin ta sa alheri ga masu jin ta. Ku kuma kula, kada fa ku bata wa Ruhu Mai tsarki na Allah rai, wanda aka hatimce ku da shi, cewa ku nasa ne a ranar fansa. Ku rabu da kowane irin dacin rai da hassala da fushi da tankiya da yanke da kowane irin keta. Ku yi wa juna kirki, kuna tausayi, kuna yafe wa juna kamar yadda Allah Ya yafe muku ta wurin Almasihu.” Afisawa 4:26-32. 

Lokuta da dama mukan gani ko mukan ji labaran wadansu da aka kona da wutar taya a Jihar Legas da wasu garuruwa cikin wannan kasar, domin an zarge su da sata ko sane da makamantansu. Wannan yakan faru ne cikin fushi da jama’a ke yi har ya kai ga kisan wanda aka zarga. Wani a ciki ma bai gan lokacin da wanda aka zarga ke aikata wannan hali ba, amma sai ka ga ya fi wanda aka yi wa laifin fushi, me ya sa haka? Dalili kuwa shi ne mukan yi fushi har mu bai wa Iblis zarafi ya haddasa abin da ya ga dama da mu, kamar yadda Littafi Mai tsarki ke fadi, “In kun fusata, kada ku yi zunubi, kada ma fushinku ya kai faduwar rana, kada kuma ku bar wa Iblis wata kofa.” 

Wadansu kan yi fushin da har ta kan kai su ga kisa ko kisan kai, “Me yake haddasa gaba da husuma a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku ne suke yaƙi da juna a zukatanku ba? Kukan yi marmarin abu ku rasa, sai ku yi kisan kai. Kukan yi kwadayi, ku kasa samu, sai ku yi husuma da fada. Kukan rasa don ba kwa addu’a ne”. Yakubu 4:1-2

A zamanka na mai bin Yesu Almasihu, ya kamata ka san yadda za ka bi da rayuwarka har ka kiyaye kanka daga irin wannan halin fushin, gama duk mai bin Yesu da gaskiya sabuwar halitta ce. 2 Korintiya 5:17. “Saboda haka, duk wanda yake na Almasihu sabuwar halitta ce, tsohon al’amari duk ya shuɗe, ga shi, kome ya zama sabo”. Sai ka binciki kanka a yau, wane irin abu ne kan saka yin fushi? Yaya kake yi idan ka tarar da kanka cikin irin wannan halin fushi, kana bidar jagorancin Ubangiji ne ko taka zuciyar? “Wawa yakan nuna fushinsa koyaushe, amma mutum mai hikima yakan kanne fushinsa,” in ji maganar Ubangiji a Karin Magana 29:11. “Kada ka yi fushi, kada ka hassala! Kada ka damu! Gama ba zai yi maka amfanin komai ba. Wadanda suka dogara ga Ubangiji, za su yi zamansu lafiya a kasar, amma za a kori mugaye.” Zabura 37:8-9. Haka kuma cikin Littafin Yakubu 1:19-21 “Ya ’yan uwana kaunatattu! Ku san wannan, wato kowa ya yi hanzarin kasa kunne da jinkirin yin magana da kuma jinkirin yin fushi, don fushin mutum ba ya aikata adalci. Saboda haka, sai ku yar da kowane irin aikin kazanta da keta iri iri, maganar nan da aka dasa a zuciyarku, ku yi na’am da ita a cikin halin tawali’u, domin ita ce mai ikon ceton rayukanku.” 

Abin lura a nan shi ne, mu juyo ga Ubangiji, mu nemi jagorancinSa cikin komai domin nufinSa ya tabbata a cikin rayuwarmu gama ba yadda nufin Ubangiji zai bayyana cikin rayuwarmu idan har muna cike da halin fushi.  

Bari mu ga abin da Yesu Almasihu ya fada a kan fushi a cikin Littafin Matiyu 5:21-24, “Kun dai ji an fada wa mutanen da, ‘Kada ka yi kisan kai, kowa ya yi kisa kuwa, za a hukunta shi.’ Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da dan uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da dan uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ Hakkinsa shiga Gidan Wuta. Saboda haka, in kana cikin mika hadayarka a kan bagadin hadaya, a nan kuma ka tuna dan uwanka yana da wata magana game da kai, sai ka dakatar da hadayarka a gaban bagadin hadaya tukuna, ka je ku shirya da dan uwanka, sa’an nan ka zo ka mika hadayarka.”

Bari Ubangiji Allah Ya ba mu hikimar kame kanmu domin kada mu yi zunubi ta dalilin yin fushi da junanmu, amin.