✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Addu’a (5)

Addu’ar yabo ga Ubangiji Yabo da godiya sun tabbata ga Ubangiji Allah Mahaliccinmu. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, inda za mu ci…

Addu’ar yabo ga Ubangiji

Yabo da godiya sun tabbata ga Ubangiji Allah Mahaliccinmu. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, inda za mu ci gaba da nazarinmu kan addu’a. A wannan makon za mu ga yadda za mu mika wa Ubangiji Allah yabo ta wurin yin addu’a.

Misali na farko shi ne addu’ar yabo da Hannatu ta yi ga Ubangiji domin Ya amsa mata addu’ar da ta yi don ta samu da (Sama’ila). 

1 Samaila 2:1-10

“Hannatu kuwa ta yi addu’a ta ce, “Ubangiji Ya cika zuciyata da murna. Ina farin ciki da abin da Ya yi. Ina yi wa maƙiyana dariya, Ina matuƙar murna domin Allah Ya taimake ni. “Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji, Babu wani mai kama da Shi, Ba mai kiyaye mu kamar Allahnmu. Kada ku kara yin magana ta girman kai, Ku daina maganganunku na fariya, Gama Ubangiji Allah Shi ne Masani, Yana kuma auna dukan aikin da mutum ya yi. An kakkarya bakunan karfafan sojoji, Amma rarrauna ya zama mai karfi. kosassun mutane suna kwadago saboda abinci, Masu fama da yunwa kuwa sun daina jin yunwa. Bakarariya ta haifi ’ya’ya bakwai, Wadda ta haifi ’ya’ya da yawa kuwa ta rasa su duka. Ubangiji ne Yake kashewa, Ya kuma rayar, Yana kai mutane kabari, Ya kuma ta da su. Yakan sa wadansu mutane su zama matalauta, Wadansu kuwa attajirai. Yakan kaskantar da wadansu, Ya kuma daukaka wadansu. Yakan ta da matalauci daga cikin kura, Yakan daga mai bukata daga zaman bakin ciki. Ya sa su zama abokan ’ya’yan sarki, Ya dora su a wurare masu mukami. Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne, A kansu Ya kafa duniya. Zai kiyaye rayukan amintattun mutanensa, Amma miyagun mutane za su lalace cikin duhu, Ba karfin mutum yake sa ya yi nasara ba. Za a hallakar da makiyan Ubangiji, Zai yi musu tsawa daga sama. Ubangiji zai hukunta dukan duniya, Zai ba sarkinSa iko, Zai sa zababben sarkinSa ya zama mai nasara.”

A nan mun ga yadda Hannatu ta nuna farin cikinta ga Ubangiji ta wurin nuna maSa yabo cikin addu’arta. Lokuta da dama mukan dauki lokacin yin addu’a da Mahaliccinmu lokaci ne na roko, lokacin neman biyan bukata. Addu’a ta fi haka, ta wurin yin addu’a mukan mika wa Ubangiji godiya da yabo da roko da kuma yin zumunta da Shi. 

Mukan iya yin addu’ar yabo ga Ubangiji don girmanSa.

Ishaya 40: 28, 55:9: “Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba? Ubangiji Madauwamin Allah ne? Ya halicci dukan duniya. Bai taba jin gajiya ko kasala ba. Ba wanda ya taba fahimtar tunaninSa.Kamar yadda sammai suke can nesa da kasa, Haka al’amurana da tunanina suke nesa da naku.”

 Sannan mukan iya yabonSa don alherinSa da jinkanSa don jinkirin fushinSa da kauna: Fitowa 34:6, “Ni ne Ubangiji, Ubangiji Allah Mai jinƙai, Mai alheri, Mai jinkirin fushi, Mai yawan kauna, Mai gaskiya.” 

Bari mu ga me Zabura 89:8-16. 146 ke fadi: “Ya Ubangiji Allah, Mai runduna, Ba wani mai iko kamarKa, Kai Mai aminci ne a kowane abu. Kai kake mulkin haukar teku, Kakan kwantar da haukar raƙuman ruwa. Ka ragargaza dodon nan Rahab, Ka kashe shi da karfin ikonKa ka cinye maƙiyanKa. Duniya taKa ce, haka ma samaniya taKa ce, Kai ne Ka halicci duniya da duk abin da yake cikinta. Kai ne Ka yi Kudu da Arewa, Dutsen Tabor da Dutsen Harmon suna rera waƙa gare Ka don farin ciki. Kai kake da iko! Kai kake da karfi! A gaskiya da adalci aka kafa mulkinKa, Akwai kauna da aminci a duk abin da Kake yi. Masu farin ciki ne jama’ar da suke yi maKa sujada, suna rera waƙoƙi, Wadanda suke zaune a hasken alherinKa. Suna murna duk yini saboda da Kai, Suna kuwa yabonKa saboda alherinKa.

Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ka yabi Ubangiji, ya raina! Zan yabe Shi muddin raina. Zan rera waƙa ga Allahna duk kwanakina. Kada ka dogara ga shugabanni, Ko kowane mutum da ba zai iya cetonka ba. Sa’ad da suka mutu sai su koma turɓaya, A wannan rana dukan shirye-shiryensu sun kare. Mai farin ciki ne mutumin da Allah na Yakubu ne Yake taimakonsa, Yana kuma dogara ga Ubangiji Allahnsa, wanda Ya halicci sama da duniya da teku da dukan abin da yake cikinsu. Kullum yakan cika alkawaranSa. A yanke shari’arsa takan ba wanda aka zalunta gaskiya. Yana ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji Yakan kuɓutar da ɗaurarru. Yakan ba makafi ganin gari. Yakan daukaka wadanda aka wulakanta. Yana kaunar jama’arsa, adalai. Yakan kiyaye baƙi wadanda suke zaune a kasar. Yakan taimaki gwagware, wato matan da mazansu suka mutu da marayu. Yakan lalatar da dabarun mugaye. Ubangiji Sarki ne har abada! Ya Sihiyona, Allahnki zai yi mulki har dukan zamanai! Yabo ya tabbata ga Ubangiji!”

To, ’yan uwa cikin Yesu Almasihu, me za mu ce wa Ubangiji Allah? In da muka karanta cikin Zabura ya kara tunatar da mu kan abubuwan da muka sani game da girman Ubangiji. Don haka, ba mu da wata hujja da za mu ce zai hana mu yabon Ubangiji Allah. 

Bari Ubangiji Allah Ya taimake mu, amin.