✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Addu’a (2)

Addu’ar Ubangiji Godiya ta tabbata ga Ubangiji Sarkin sarakuna domin kaunarsa zuwa gare mu. A wannan makon za mu fara ne da addu’ar Ubangiji.  Ubangiji…

Addu’ar Ubangiji

Godiya ta tabbata ga Ubangiji Sarkin sarakuna domin kaunarsa zuwa gare mu.

A wannan makon za mu fara ne da addu’ar Ubangiji. 

Ubangiji Allah Yana bukatar mu zama masu zumunta da Shi ta wurin yin addu’a.

Yin addu’a hanya ce ta sadarwa a tsakanin mutum da Ubangijinsa, ta wurin yin haka ne mukan iya nuna godiyarmu ga Allah, mu kuma mika bukatunmu gare Shi. Mutane da dama ba su fahimci mene ne manufa da kuma hanyar yin addu’a ba. Masu bi da dama suna yin addu’a ne a addinance, wato yin addu’a don haka muka tarar ake yi, ko haka majami’armu ta koya mana da dai dalilai da dama. Amma mene ne Littafi Mai tsarki ke fadi game da wannan? Da farko bari mu ga abin da Yesu Almasihu ya bayyana mana game da yin addu’a. 

“In za ku yi addu’a, kada ku zama kamar munafukai, don sun cika son yin addu’a a tsaye a majami’u da kan hanyoyi don dai mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun samu iyakar ladansu. Amma in za ka yi addu’a, sai ka shiga lollokinka, ka rufe kofa, ka yi addu’a ga Ubanka wanda yake boye, Ubanka kuwa da Yake ganin abin da ake yi a asirce, zai saka maka. “In kuwa kuna addu’a, kada ku yi ta maimaitawar banza, kamar yadda al’ummai suke yi, a zatonsu za a saurare su saboda yawan maganarsu. Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku Ya san bukatarku tun kafin ku roke shi. Saboda haka sai ku yi addu’a kamar haka:  

“Ya Ubanmu, wanda Yake cikin sama, A kiyaye sunanKa da tsarki.

MulkinKa ya zo, A aikata nufinKa a duniya kamar yadda ake yi a sama.

Ka ba mu abincinmu na yau.

Ka gafarta mana laifuffukanmu, Kamar yadda mu ma muke gafarta wa wadanda suke yi mana laifi.

Kada Ka kai mu wurin jaraba, amma Ka cece mu daga Mugun.”

Domin in kun yafe wa mutane laifyffkansu, Ubanku na sama zai yafe muku. In kuwa ba ku yafe wa mutane laifuffukansu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku naku ba.” (Luka 11:1-13).

Alal-misali, me za ka kira mutumin da ke yabon matarsa, yana nuna mata kauna a cikin jama’a amma kuma ba haka ne yake ba a cikin gida? Mu ce ba ya ma kula ta ko tanka mata, a takaice yana yin wannan don idon mutane ne kawai amma ba don kaunar gaskiya ba. Shi ya sa Yesu Almasihu ya ce mu guji yin abu don ganin idon mutane, ko kuwa don mutane su yabe mu, musamman wajen yin addu’a. Haka kuma maimaicin kalamai wajen yin addu’a ba wannan ne Ubangiji Allah ke bukata a wurinmu ba, Yana bukatar sadarwa mai ma’ana da gaskiya tsakaninSa da mu mutane. 

Yesu Almasihu ya ba mu misalin yadda za mu yi addu’a, masu bi da dama sun san shi a ka, wato addu’ar Ubangiji. Cikin yin addu’ar mukan fara da kira bisa sunan Ubanmu Wanda Yake cikin sama, wato muna ba shi girmanSa da kuma nuna cewa a gare Shi kadai muke wannan roko. A takaice, abu na farko wurin yin addu’a shi ne girmama Ubangiji Allah, tsarkake sunanaSa, ka yabe Shi don Allantakarsa, ka kuma bidi mulkinSa cikin rayuwarka don ka aikata nufinSa a duniya kamar yadda take a can sama, wato, ‘Ya Ubanmu, wanda yake cikin sama, A kiyaye sunanKa da tsarki. MulkinKa ya zo, A aikata nufinKa a duniya kamar yadda ake yi a sama.’ Sannan sai ka mika bukatunka gare Shi, ka gaya maSa matsalolinka, kai kadai ka san bukatunka, Ubangiji Allah kuma zai ji Ya biya maka bukatunka domin “Kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta, daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sakewa a gare shi faufau.” (Yakubu 1:17). Shi ya sa Yesu Almasihu ya ce kada ka yi shi don ganin idon mutane amma tsakaninka da Mahaliccinka kadai, domin Shi ne Mai biya mana bukata. 

Na biye da wannan, neman gafara daga wurinSa. Mukan saba wa Ubangiji Allah ta hanyoyi da dama, cikin sani da rashin sani, don haka yana da kyau mu nemi gafara a wurinSa domin Ubangiji Allah Mai tsarki ne Yana kuma bukatar mu zama da tsarki cikin rayuwa a duk lokacin da za mu zo gabanSa. Haka kuma Yana son mu zama masu koyi ta wurin gafarar zunubanmu, mu ma mu gafarta wa juna. Shi ya sa kafin ka zo gaban Ubangiji cikin addu’a, sai kai tabbata ba ka rike da wani a zuci don Ubangiji Ya ji addu’arka Ya kuma gafarta maka. 

Jarrabawa na ko’ina kewaye da mu, idan ba ka nema ba, za ta neme ka, saboda haka sai mu nemi bishewar Ubangiji ta wurin alherinSa don mu samu kubuta daga jarabawa iri-iri da suke kewaye da mu.

Ubangiji Ya alkawarta Ya albarkace mu idan muka zo gabansS da gaskiya.

“Adalai sukan yi kira ga Ubangiji, Yakan kuwa kasa kunne, Yakan cece su daga dukan wahalarsu.

Ubangiji Yana kusa da wadanda suka karai, Yakan ceci wadanda suka fid da zuciya.” (Zabura 34:17-18)  

Za mu ci gaba mako mai zuwa da yardar Ubangiji. 

Shalom.