Gwamnan Jahar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar ya bayyana cewa barazanar ‘yan adawa ba za ta tsorata shi ba, bisa yada makarkashiyar cewar bai yi aikin komai ba tun da ya amshi ragamar mulkin jahar, bai yi wani abu sabo ba, sai tsofaffin ayyukan da ya gada kawai ya karasa.
Badaru ya fadi haka ne a wajen bikin raba kayayyakin da dan majalisa mai wakiltar Kirikasamma da Guri da Birniwa ya raba Alhaji Abubakar fulata da kuma bude ofishinsa na siyasa a garin Kirikasamma a makon jiya.
Ya ce “Saboda mun gaji gyare-gyaren makarantu masu yawa daga tsohuwar gwamnatin Lamido da suka lalace da asibitoci da muka samu ba sa cikin hayyacinsu da kuma ayyukan hanyoyi da aka yi watsi da su na biliyoyin naira wadanda muka dauki alkawari zamu kammala su kafin mu fara yin sabbin ayyuka a jahar, amma duk da irin kokarin da muke yi hakan bai sa sun daina yin adawa da mu ba.”
Badaru ya ci gaba da cewar jama’ar jahar Jigawa shaida ne bai ma kamata su rika sauraran ‘yan adawa ba, sannan sai kuma ya ci gaba da baiwa jama’ar jahar hakuri ya na mai cewar da zarar sun kammala ayyukan hanyoyin da ba su karasa ba, za su bude sabbin ayyukan raya kasa a fadin jahar gaba daya.
Da yake nasa jawabin, Alhaji Dakta Abubakar Hassan Fulata, ya ce kayan da ya raba ga mutanen mazabarsa da nufin inganta rayuwar al’ummarsa, ya kai na naira miliyan 40 wadanda suka hada da Babura da motoci da keken dinki da injinan walda da sauransu.
Dakta Fulata ya ci gaba da cewar ya yi haka ne domin ya taimakawa marasa karfi dake yankunan karkara, a daukacin mazabarsa, ta hanyar ba su kayan sana’a wadda za su dogara da kansu domin ya daga darajar rayuwarsu.