Da daddare bayan Sallar Isha, sai Annabi (SAW) ya mike tsaye ya yi huduba ga wadanda suka hadu.
“Allahu Akbar!” ya fara da cewa: “Al’umma da yawa a gabaninku sun yi rauni ne kuma aka hallaka su sakamakon irin wannan mummunan kuskure: Wato idan babba ko dan babba ya aikata laifi sai a kyale shi, amma idan talaka ko karami ya aikata irin wannan aiki sai a hukunta shi. To na rantse da Wanda rayuwata ke hannunSa (Allah) da Fatima ’yata za ta yi sata, wallahi da na yanke mata hukuncin gutsure hannunta!” Wane mutum!
Wallahi ya Ma’aikin Allah ba ya ga addininka babu wani addini da ya zo da irin wannan ka’ida a tsakanin addinan duniya. Baya ga addininka babu wani tsari da ya zo da irin wannan adalci a tsare-tsaren dokokin duniya! Wannan daidaito da adalci a bangaren shari’a da Ma’aikin (SAW) ya assasa ne, sahabbai da wadanda suka biyo bayansu suka rika kokarin bi a harkokin mulki da rayuwarsu. Kuma wannan ne yake sa Musulmi ke bambanta da duk wani mahaluki a bayan kasa wajen kwatanta adalci da tabbatar da daidaito a yayin gudanar da ayyukansa. Za mu ga haka a ’yan misalai kadan na halifancin Amirul Muminina Umar bin Khaddabi (Radiyallahu Anhu) da za mu shiga yanzu.
Kai munafuki!
Amru cike da fushi ya ce, “Kai wawa! Kai munafuki!”
Yayin da wadannan kalmomi suka fito a tsakanin taron jama’a, sai kowa ya yi tsit mamaki ya kama jama’a, mutane suka kadu kan wannan zargi. Shin Amru zai iya yin wannab zargi ga Al-Tajibi wanda bai dade da Musulunta ba, ya jingina shi da munafunci ba tare da wata hujja ba? Amru bin Al’As, Janar ne na soja kuma yanzu an nada shi Gwamnan Masar. A fagen daga jarumi ne, amma galibi yakan kasa danne fushinsa idan lamari ya shiga tsakaninsa da wasu, kuma hakan ne ke sanya shi fadin abin da bai yi niyya ba. A Musulunci munafunci babban zunubi ne, don haka zargin wani Musulmi da munafunci babban cin zarafi ne da cin fuska, saboda hakan yana zubar da girma da mutunci.
To kuwa ya yi tsit yana jiran ya ji abin da Al-Tajibi zai ce. Fuskarsa ta murtuke, muryarsa ta kama rawa a daidai lokacin da ya juyo sai ya ce: “Amru na rantse da Allah kuma a gaban wadannan shaidun tunda na zama Musulmi ban taba aikata wani abu na munafunci ba. Kuma wallahi daga yau ba zan sake wanke kaina ba, ba kuma zan sanya masa turare ba, har sai na isa ga Umar na gaya masa irin cin mutuncin da ka yi min.”
Sai Al-Tajibi ya bar Masar ya nufi Madina, bayan kwanaki yana tafiya ya isa Masallacin Annabi (SAW) inda ya shiga aka yi Sallah tare da shi. Sannan ya nemi ya gana da Umar (RA). Al-Tajibi ya bayyana abin da ya faru da rashin adalcin da Amru ya yi masa. Ba tare da bata lokaci ba Umar (RA) ya rubuta wasika cew:
“Ya Amru! Al-Tajibi ya gaya min cewa ka ci mutuncinsa ka kira shi munafuki a bainar jama’a. Idan ba ka kawo shaida biyu da za su tabbatar da zarginka ba na ya aikata munafunci to ka bata masa suna. Kuma a bisa dokar Musulunci ya cancanji ya yi maka bulala 40.”
Umar ya ba da wasikar ga jakadansa wanda ya raka Al-Tajibi zuwa Masar. Da suka isa masallacin Masar sai su biyun suka tsaya har sai da kowa ya zo ciki har da Amru.
Sai Al-Tajibi ya mike tsaye ya yi magana cewa: “Ina rokonku ku ba da shaida cewa gwamnanmu Amru bin Al-As ba tare da wata hujja ba ya bata min suna ta hanyar kirana munafuki a gaban taron jama’a.”
Kasancewar kowa yana wurin, ya san lokacin da aka yi wannan zargi sai duka aka mike alamar sun san an yi haka. Sai Al-Tajibi ya karbi wasikar daga jakadan Umar ya mika wa sakataren Amru wanda ya karanta ta da karfi. Lokacin da ya iso kan horon da aka yanke wa Amru, sai hankalin Amru da sakatarensa da jama’arsa ya yi matukar tashi. Me yake faruwa ne yanzu? Shin wani sabon musulunta –mutumin Masar – zai yi bulala ga Gwamnan da ya ci Masar da yaki, shugaba daga cikin muhimmiyar kabila ta kuraishawa?
Sai sakataren Amru ya matsa kusa da Al-Tajibi yana murmushi. Ya ce, “dan uwana, hakika ba ka son yin bulala ga gwamnanka? Kuma yana da kyau ka fahimci cewa idan Amru ya fusata yakan fadi magana mai zafi ba tare da sanin illar abin da ya fada ba. Hakika kai ba munafuki ba ne. Ka ba mu dama mu biya ka diyya kan sanya ka a halin damuwa da kaskanci da muka yi. Ina ba ka tabbacin za mu kasance mafiya kyautatawa…”
Sai jama’ar da suka taru suka fara gajen hakuri
Ran Al-Tajibi ya riga ya yi matukar baci, ya ki amincewa da neman afuwar. Ya fadi da karfi cewa, “Ba na son diyyarku. Koda za ku cika gida da zinari ba zai biya ni wannan cin mutunci ba. Don haka kai nake jira Amru!”
Sai jama’ar da suka taru suka fara fusata. Me ya samu wannan mutumi ne? “Ya isa haka Al-Tajibi,” suka ce. “Mun ga kana neman wuce gona da iri. Amru ya nemi gafara ta hannun sakatarensa, amma kuma yanzu kana neman bullo da wata hanya ta tozartawa a bainar jama’a domin ka huce hushinka. Wane irin daukar fansa ne wannan kake nema?”
A wannan lokaci Amru dai ya yi zugum ya kasa cewa komai yana zaune tare da mukarrabansa. A karshe ya bayyana ga Al-Tajibi cewa ba zai samu adalcin da yake nema ba. Sai ya ce, “Na lura babu wani daga cikinku da yake shirye domin aiwatar da umarnin Umar (RA).” Ya fadi haka yana nuni ga jakadan Umar, sai ya juya ya fita daga masallacin.
Sai Amru ya fara tunanin halin da zai shiga idan Al-Tajibi ya koma ga Umar (RA), a lokacin ya san zai hadu da hukuncin da ya fi wannan muni. Ya kama gemunsa ya rike ya yi kasake na wnai lokaci, sannan ya juya zuwa ga daya daga cikin mutanensa ya ce, “Ku kira Al-Tajibi da jakadan nan su dawo.”
Da mutanen biyu suka dawo, sai Amru ya mike tsaye ya cire rawaninsa cikin kankan da kai, ya durkusa a gaban Al-Tajibi ya mika masa bulala ya ce, “doke ni! Amru ba ya tsoron bulalar wani mutum ko wulakancin mutum.”
Sai kowa ya yi tsuru-tsuru numfashin jama’a ya dauke suka cika da mamaki. Me, Amru, Babban Kwamnadan Askarawan Masar, kuma Gwamnanta, wanda ya samu nasarori, babban mutum daga kabilar kuraishawa, kuma sahabin Annabi (SAW) ne zai mika kansa ga wani baubawa daga mutanen Masar sabon musulunta ya yi masa bulala?
Al-Tajibi bai ko kula jama’ar da ta taru ba, sai ya ce: “Ya kai Amru! Ina ikonka da karfinka da fada-a- jinka suke su zo su cece ka daga kuskurenka?”
Amru bai ko yi gizau ba ya ce, “Ka daina bata lokaci. Ka yi abin da aka umarce ka da yi.”
Al-Tajibi ya tsaya ya dubi wannan babban mutum durkushe a gabansa, sai ya kada kansa ya jefar da bulalar gefe, sannan ya ce: “Na yafe maka ya kai Amru! Kuma ba na bukatar wata diyya. Na yi haka ne kawai domin in nuna a Musulunci martaba da mutunci mutum komai talakansa daidai take da ta kwamandan ko sarki ko gwamna kamar kai.”
Yana fadin haka, sai ya bar masallacin!
Adalcin Musulunci: Wasu misalai daga rayuwar Umar dan Khaddabi (2)
Da daddare bayan Sallar Isha, sai Annabi (SAW) ya mike tsaye ya yi huduba ga wadanda suka hadu.“Allahu Akbar!” ya fara da cewa: “Al’umma da…