Janar Abdulsalami Abubakar, shi ne tsohon Shugaban Kasa na mulkin soji, wanda ya mika mulki ga farar hula a shekarar 1999. Abdulsalami ya hau mulki ne bayan rasuwar tsohon Shugaban Kasa Janar Sani Abacha.
A wannan tattaunawa ta musamman da ya yi Aminiya, ya bayyana irin dambarwar da ta faru a Fadar Shugaban Kasa bayan rasuwar Janar Abacha kafin a sanar da rasuwar, da kuma abubuwan da suka sa shi Abdulsalamin ya zabi ya sauka daga mulki ya mika wa farar hula bayan wata shida kacal da hawansa.
- Gada ta karye a Amurka ana daf da ziyarar Shugaban Kasa a wajen
- Mutumin da ya fara tattaki daga Ingila zuwa Makkah don sauke farali ya isa Turkiyya
Aminiya: Yallabai, ko za ka yi mana bitar ranar da Abacha ya rasu da tataburzar da ta faru da yadda ka zama Shugaban Kasa?
Abdulsalami: Abubuwa da dama sun faru a ranar da Janar Abacha ya rasu.
Ina jin ya rasu ne a ranar da aka shirya zai je Togo, don halartar taron ECOWAS ko AU. Sai na samu kira daga Fadar Shugaban Kasa, cewa Janar Abacha yana son gani na.
Nan take na fara tunani cewa ina fata ba dai ya canja ra’ayinsa na zuwa Togo ba ne, yana shirin tura ni saboda a lokacin, ni ne mutum na biyu a gwamnatin domin a lokacin Janar Diya da sauransu suna fama da matsalar zargin juyin mulki.
Don haka sai nake tunanin Janar ya canja ra’ayinsa ne zai tura ni, domin a lokuta da dama akan kira ni, in je in wakilici Shugaban Kasa.
Lokacin da zan shiga wanka, sai na fada wa matata cewa, “Ina jin zan tafi taron AU, ki taimaka ki kintsa min jakata,” amma kafin in gama sai ga wani kiran.
Shin da safe ne?
Eh, da safe ne. Sai kuma ga wani kiran cewa; “Shugaban Kasa yana jiran ka.”
Na ce, “To gani nan zuwa.” Sai kawai na sa rigar motsa jiki, tunda babu lokacin sa yunifom da sauransu, domin an matsa cewa ana bukata ta da gaggawa.
Na je da kayan motsa jiki, ina jin ina sanye da silifas. Lokacin da na shiga sai suka ce, “Janar yana cikin ofis.”
To na saba idan na je ofishin ko wa ke tare da Janar Abacha nakan shiga ne in same shi, yana iya cewa “Ka jira in gama da wannan bawan Allah ko ya bukaci wancan ya bar mu.”
To abin mamaki lokacin da na zo, ina hawa benen, sai wani ya ce, “A’a ya ce ka jira a dakin karbar baki.”
Kuma abin mamaki na zauna a dakin karbar bakin har minti 30 ko 40, sai na rika mamakin abin da ke faruwa.
Duk lokacin da na yi niyyar zuwa sama sai su ce a’a Janar ya ce, in jira. Bayan kamar minti 40 ina jira sai marigayi [Ibrahim] Coomassie, wato Sufeto Janar na ’Yan Sanda ya zo inda nake ya ce, “Yallabai ka zo.”
Kuma maimakon zuwa ofishin sai muka fita, ya ce, “Za mu je gidan ne.” Muna cikin haka ne ya shaida min cewa, “Wato wani abin bakin ciki ne, Janar Abacha ya rasu da dare.”
To a haka muka shiga inda Abacha yake, kuma muna shiga suka nuna min inda gawarsa take, na shiga na yi masa addu’ar neman gafara da sauransu.
Sannan muka shiga falo inda na iske wadansu mutane ciki, Coomassie na wurin da Babban Jojin Najeriya, ina jin da Ambasada Babagana Kingibe da jami’in tsaro daya ko biyu ba zan iya tuna kowa da kowa ba.
Shin mutuwar ta Allah ce saboda akwai zarge-zarge da dama?
To a lokacin da aka shaida min ya rasu, babu wadannan zarge-zarge, daga baya suka taso. Damuwarmu a lokacin ita ce Shugaban Kasa ya rasu, yaya za mu sanar da kasa da sauransu.
A lokacin Babban Joji ne ya jagorance mu ya ce, “Kun gani an dauki lokaci akwai bukatar a sanar da ’yan Najeriya kan rasuwar Shugaban Kasa, ba za a bar gibi ba, wajibi ne a samu Shugaban Kasa kafin ku ci gaba da gudanar da sauran abubuwa.”
Ina jin wannan ne ya aza harsashin sauran abubuwan. Don haka nan take a matsayina na Babban Hafsan Tsaro na lokacin na hanzarta kiran taron Majalisar Kasa.
Kana cikin tufafin motsa jikin ko ka canja a lokacin?
Ina sanye da tufafin motsa jikin, saboda babu lokaci, kuma saboda mun samu kanmu a cikin kaduwa da tashin hankali.
Daga baya ne bayan mun shirya taro na koma gida na sa yunifom.
A lokacin an cimma matsaya ce ko an yi takaddama kan wanda zai zamo Shugaban Kasa?
Lokacin da na dawo na sa tufafi sosai, a lokacin wakilan Majalisar Mulkin Soja sun fara isowa, da muka hadu, sai muka shiga taro.
Muka fada musu abin da ya faru duk da cewa duk mambobin sun san Mai Girma Janar Abacha ya rasu. Muka sanar da majalisar rasuwarsa da shawarar da Babban Joji ya bayar kafin mu yi komai cewa wajibi ne a samu wanda zai karbi ragamar mulki.
An dauki lokaci mai tsawo kafin wakilan majalisar su samu matsaya. A zauren an samu muhawara sosai. A karshe aka ce muna da Janar Useni wanda a lokacin shi ne hafsa mafi girma, to amma shi yana bangaren gudanarwa ce, shi ne Ministan Birnin Tarayya, ni kuma ni ne Babban Hafsan Tsaro, don haka dayanmu ne zai zama Shugaban Kasa.
Aka kasa cimma matsaya, sai wani ya ce, “Kun gani, dole mu shaida wa duniya cewa Janar Abacha ya rasu, tun kafin lokaci ya kure, mu je mu binne shi kafin mu dawo mu daidaita tsakaninmu.”
A lokacin da hakan ke gudana iyalansa sun yanke shawarar a binne shi a Kano, don haka muna tattaunawa ana tsara yadda za a binne shi a Kano.
Ina jin wannan ya kai mu har dare, lokacin da dukkanmu muka bar wannan batu muka ce a je a yi masa jana’iza mu dawo, wannan shi ne abin da ya faru.
Sai muka tafi Kano muka yi masa biso muka dawo kan batun wanda zai karbi mulki.
Hakika a matsayina na Babban Hafsan Tsaro ni ne nake shugabantar taron; to a karshe bayan kada kuri’a da sauransu mambobin majalisar suka yanke shawarar in karbi mulki a matsayin Shugaban Kasa.
Kuma kana mulki ne rasuwar MKO Abiola mai cike da takaddama ta auku. Har yanzu akwai masu ganin akwai wasu boyayyun abubuwa da suka faru. Ko za ka fayyace hakikanin lamarin, ka shaida mana abin da ka sani?
Eh, akwai zarge-zarge da dama cewa wai mu muka kashe Abiola. Kamar kullum duk lokacin nake magana a kan marigayi Abiola, nakan gode wa Allah da Ya nuna min wasu abubuwa a lokacin da Ya ba ni mulkin kasar nan.
A ranar da Moshood (Abiola) ya rasu, Allah Ya jikan sa, abu biyu zuwa uku suka sa a kullum nake gode wa Ubangijina.
Na daya na karbi bakuncin wani ayari daga Amurka a karkashin jagorancin Pickering (Jakada Tom Pickering) wanda a lokacin, ina tsammanin shi ne Sakataren Wajen Amurka ko wani abu kamar haka.
A cikin ayarinsa ina tunawa akwai Susan Rice. Na tuna da ita sosai saboda rawar da ta taka daga baya.
To bayan ziyarar da tattaunawar da muka yi, lokacin da za su bar ofishina, Pickering ya ce, “Mai girma Shugaban Kasa mun nemi ganin Moshood Abiola amma an hana mu.”
Sai na ce “Me ya sa aka hana ku? Wa ya hana ku?” Sai na yanke shawara cewa, “Za ku ga Moshood, na soke umarnin duk wanda ya ce ba za ku iya ganinsa ba.”
Na kira Babban Jami’in Tsarona, na ce, “A shirya wa wannan ayari su gana da Abiola,” wannan ke nan.
Sannan a lokacin da ake tsare da Moshood Abiola, baya ga likitansa a sanina, babu wani daga iyalansa da ya gan shi.
Don haka lokacin da na zama Shugaban Kasa, bisa tuntuba da ganawa tare da Ambasada Babagana Kingibe, na ba iyalan wata rana da za su zo ganin sa.
To kwana daya kafin ya rasu, iyalansa sun zo Abuja don ganin sa. Saboda wasu dalilai ba dukkan iyalin ne za su iya ganin sa a lokaci guda ba, don haka aka amince cewa idan wannan rukunin iyalan sun gan shi yau, gobe wani rukunin ya gan shi.
Don haka sun gan shi kamar a jiya, yau kuma wannan ayari daga Amurka ya zo don ganawa da ni, kuma na ce su za su iya ganin sa.
A ka’ida da yamma ’yan uwan suke zuwa ganin sa. Don haka saboda na ba wa wannan ayarin daga Amurka izinin ganin sa, hakan ya sa daya rukunin iyalan suka jira don su gan shi.
To a daidai lokacin ganawa da ayarin Amurka, Abiola ya kama rashin lafiya, nan take jami’an tsaro suka kira ayarin likitoci su zo su duba shi, kuma da suka ga halin da yake ciki, sai suka ce ya yi tsanani don haka akwai bukatar a kai shi cibiyar lafiya.
Don haka ayarin likitocin da na Amurka ne suka kai shi asibitin, abin takaici a asibitin rai ya yi halinsa. Sai Babban Jami’in Tsarona ya kira ni ya ce, “Ga wani bakin labari.” Na ce mene ne? Ya ce “Abiola ya rasu.”
Sai abin ya kada ni. Ya ce mini yana can tare da ayarin Amurka, a lokacin ina zaune a cikin bariki, ban koma fadar Shugaban Kasa ba, sai na ce to, ya taho da ayarin Amurkawan gidana, zan gana da su a gidan.
Don haka na tashi daga ofis, na tafi can. Abin da ya saura yanzu shi ne yadda zan sanar da rasuwar Abiola ga iyalansa da yadda za mu shaida wa duniya Abiola ya rasu.
Dole ne in yi godiya ga Allah, sannan ga Jakada Kingibe saboda mun kira shi muka ce ya taho da iyalan Abiola. To da suka zo sai na ba su labarin abin bakin cikin da ya faru.
Kamar yadda za ka yi tsammani, sai iyalan suka kama kuka, ban iya tuna wace ce a cikin matan ba, sai na rike ta, tana ta rusa kuka, tana burwaya, sai Susan Rice, shi ya sa nake tunawa da ita koyaushe, ta ce, “Mai girma Shugaban Kasa wannan ba aikinka ba ne, bari in karbe ka,” don haka ta rike wannan mata har ta dan natsu.
Sa’an nan muka kira mataimakina da sauran mutane muka tsara yadda za mu bayyanar da labarin ga duniya.
Shi ya sa koyaushe nake cewa na gode wa Allah da Ya yi mini jagora. Ba don na ce ayarin Amurka su je su gana da Abiola ba, tabbas ban san yadda zan bayyana wa duniya cewa Abiola ya rasu ba, shin ayarin Amurkar za su yarda cewa ba mu muka kashe Abiola ba a lokacin da suke neman ganin sa?
Kana hawa mulki, ka ce za ka mika mulki ga farar hula, hakan ya ba mutane da dama mamaki, saboda mun san ko a yanzu masu yin juyin mulki a Afirka suna nemo hanyoyin ci gaba da zama a kan mulki. Mene ne hakikanin abin da ya sa ka yanke shawarar ka bar mulki da gaggawa?
To, har wa yau ina kara godiya ga Allah wanda tun farko Ya dora mini nauyin shugabancin kuma Ya taimake ni wajen tattaunawa da abokan aikina har muka samu yanke wannan shawara.
A lokacin da karbi mulki, Najeriya tana cikin tsaka-maiwuya.
An yi ta samun kiraye-kiraye daga fararen hula cewa sojoji su mika mulki, idan ka tuna, a lokacin an yi ta samun zanga-zanga da tashe-tashen hankula har da barnata kadarorin gwamnati da sauransu.
Abin da ke faruwa a fagen siyasa sai ya samu shiga cikin aikin soja. Mu sojoji ya kamata mu kare kundin tsarin mulkin kasa tare da martabar kasa ce.
To lokacin da na hau mulki, rundunar sojin ta shiga matsala ita kanta. Na farko, girman matsayi a aikin soja yana ta sukurkucewa, za ka ga karamin jami’i yana ba da umarni ga wanda ke gaba da shi a mukami, saboda yana cikin shugabannin siyasar kasar.
Na biyu, a lokacin za ka samu maimakon mu kasance muna maganar hadin kan Najeriya, sai muka koma tattauna batun yankunanmu; muna goyon bayan ’yan uwanmu fararen hula.
A cikin sojojin?
A cikin sojojin, kuma wannan babban hadarin ne da na tsinci kaina a aikin soja.
Wani abin kuma shi ne, wadansu daga cikinmu da suka fafata a Yakin Basasar Najeriya don tabbatar da dorewar kasar a matsayin kasa guda mun fara tunanin yaya a gabanmu za mu bari aikin da muka yi na tabbatar da wanzuwar kasar nan a ruguza shi a kan idonmu?
To wadannan ne abubuwan da suka auko mana a harkokin shugabanci; sai muka ce bari mu tabbatar kasar nan ba ta wargaje ba, bari mu yi kokarin dawo da kimar sojoji sa’annan mu dawo da abin da aka sani a baya, a rika bin girman matsayi a aiki tare da kishin kasa.
Sai muka zauna muka yanke shawarar abin da ya fi dacewa a cikin kankanin lokaci shi ne mu ba fararen hula abin da suke muradi kawai; a ba su damar jan ragamar mulkin kasar, sojoji su koma bariki su ci gaba da aikinsu na soja.
To wadannan su ne wasu daga cikin abubuwan da suka sa muka yi abin da muka yi. Ba abu ne mai sauki ba, akwai shawarwari da dama, cewa mu bari mu dauki lokaci mai tsawo, ba abu ne mai sauki a shirya zabe ba, ga wannan da wancan, amma a karshe wadansu daga cikinmu tare da taimakon wadansu da suke tare da ni, muka kekasa kasa muka ce a’a lallai mu mika mulkin cikin kankanin lokaci.
A kashin gaskiya mun so mu yi haka a kasa da wata shida ne, amma sai aka ja kunnenmu cewa shirya zabe ba karamin aiki ba ne, zai dauki lokaci kafin a yi wa jam’iyyun siyasar rajista, sa’annan bayan zabubbukan akalla za a dauki kwana 60 don tabbatar da an kammala shari’o’i da sauransu.
Don haka da muka yi dukkan wadannan lissafe-lissafe kama daga kafa jam’iyyun siyasa da shirya zabubbukan da shirya wa duk wani kalubalantar sakamakon zaben a kotuna; a karshe muka yanke shawarar cewa bari mu yi dukkan abubuwan nan a cikin wata tara.