Zaben shugaban kasa da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa da aka gudanar ranar Asabar ta zo da wasu abubuwan ba zata.
Ga 10 daga cikinsu:
Cin zaben zaben shugaban kasa babu Kano da Legas:
Kafin yanzu, an yi amannar cewa duk mai son lashe zaben shugaban kasa, wajibi ne ya ci zabe a jihohin Kano, Legas, Kadu, Katsina da Neja, wadanda su ne suka fi yawan al’umma da masu rajistar zabe a Najeriya.
Sai dai a wannan karon, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya fadi a duk jihohin da aka ambata amma kuma a karshe ya lashe zaben shugaban kasa bayan ya samu mafi rinjayen kuri’u.
Yobe ta yi PDP
Kusan tun da aka dawo tsarin dimokuradiyya a 1999, jam’iyyar PDP ba ta taba yin rinjaye a jihar ba.
Amma a wannan karon, jam’iyyar ce ta samu kuri’u mafi yawa a zaben shugaban kasa, duk da cewa ita ce jihar Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan.
Bugu da kari, Gwamna Mai Mala Buni na jihar shi ma dan jam’iyyar APC ne, kuma tsohon shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar.
Atiku ya kayar da APC a Katisna
A jihar Shugaba Muhammadu Buhari ta Katsina, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya kayar da Tinubu na APC.
Atiku ya ci zaben a Katsina da kuri’a 489,045 a yayin da Tinubu ya samu kuri’u 482,283 duk da cewa Buhari ya bayyana a fili cewa Tinubu ne dan takararsa, kuma zai yi duk mai yiwuwa don ganin dan takarar nasa ya kai bantensa a zaben shugaban kasa.
APC ta ci Binuwai
Gwaman Jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya tsaya kai da fata wajen yakar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa ta PDP, Atiku Abubakar da kuma shugaban jam’iyyar ta kasa, Iyorchia Ayu.
Uwa uba, kiyayyarsa ga jam’iyyar APC da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari; Don haka ya bayyan goyon bayansa a fili ga dan takarar LP, Peter Obi.
Amma a zaben shugbana kasa da aka gudanar a jihar, dan takarar APC, Bola Tinubu ne ya yi nasara. Shi kansa Ortom, da ya tsaya takarar kujerar sanata, ya sha kaye a hannun dan jam’iyyar APC.
Duk da Abdullahi Adamu, LP ta lashe Nasarawa
Kallo ya koma sama bayan Peter Obi ya kayar da a Jihar Nasarawa, mahaifar Shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Sanata Abdullahi Adamu.
Dan takarar LP, Peter Obi, ya kayar da Tinubu a jihar, duk kuwa da cewa kafin nan, ba a yi hasashen cewa Obi zai tabuka wani abin a-zo-a-gani ba.
Baya ga haka, jam’iyyar LP ta kayar da tsohon gwamnan jihar, Umar Almakura, da ya nemi kujerara sanata ya sha kaye a hannun dan jam’iyyar adawa, duk da cewa gwamnan jihar, AA Sule, dan jam’iyyar APC ne.
PDP ta fadi a Delta
Jam’iyyar PDP ’yar gida ce a Jihar Delta da ma daukacin yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, kuma babu wanda ke tababar hakan kafin yanzu.
Duk da wannan cewa karon an yi hasashen cewa Peter Obi na Jam’iyyar LP zai lashe yankin, ba a yi hasashen za a kayar da PDP a jihar dan takararta na mataimakin shugaban kasa ba, Ifenayi Okowa.
Sai dai kuma duk da cewa Okowa ne gwamna mai ci a Jihar Delta, shi da shi da jam’iyyarsa sun sha mamaki a hannun jam’iyyar LP.
Dan takarar LP, Peter Obi, ya samu kuri’u 341,866, a yayin da ya ninka kuri’un Atiku da Okowa da suka samu 161,600, sai Tinubu na APC ya samu 90,183.
LP ta kayar da Tinubu a gidansa
Peter Obi na LP ya ce zabe a karamar hukumar Ikeja da dan takarar APC, Bola Tinubu, ya fito.
Tinubu ya sha kaye a Jihar Legas, duk da cewa shi ne ya yi nasara a 11, Obi na da nada, amma ya fi Tinubun yawan kuri’u a jihar.
Hakan kuwa ta faru ne duk da karfin Tinubu a matsayin mai fada a ji a Legas kuma tsohon gwamnan jihar.
Abin da ya faru ya sauya lissafin siyasar Legas da ake ganin shi ke juya siyasar jihar kuma shi ne uban gidan yawancin manyan ’yan siyasa.
Tinubu ya kayar da Obi da Atiku a Ribas
Kasancewar kamar, Ortom, Gwamna Wike na Jihar Ribas na rikici da Atiku, an yi zaton Wike zai goyi bayan Peter Obi, ko kuma Obi ya kawo jihar, saboda kasancewarsa dan asalin yankin Kudu, da kuma yawan karbuwar Kudu maso Kudu da kuma Kudu maso Gabas.
Amma da aka kammala zaben shugaban kasa, Tinubu na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben da kuri’a 231,591 a yayin da Obi ya samu kuri’a 175,071.
An doke El-Rufai a kananan hukumomi 22
Gwamna Nasir El-Rufai, dan a-mutum Tinubu, kananan hukumomi biyu kacal daga cikin 23 da ke jihar ya iya kawo wa dan takararsa.
Jam’iyyar adawa ta PDP ta lashe kananan hukumomi 14, LP ta ci bakwai ka yayin da APC ta El-Rufai ke da biyu a zaben shugaban kasa.
A zaben Sanata kuma, PDP ta kwace duk kujerun sanatoci biyu da APC ke da su a jihar sannan PDP ta doke shi a karamarsa ta Zariya.
An kayar da kodinetan