✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Abubuwan da ya kamata ku sani game da yakin basasar Najeriya

An yi yakin basasa a Najeriya wanda ake kira yakin Biyafara a tsakanin shekarar 1967 zuwa 1970.

A ranar Juma’a, 15 ga watan Janairun 2021 Najeriya aka yi bikin ranar tunawa da dakarun kasar na 2021, rana guda da aka kebe domin tunawa da gwarazan mazan jiya da suka kwanta dama wajen kare martabar kasar a filin daga.

Ranar 15 ga watan Janairun kowace shekara ce aka kebance domin tunawa da dakarun sojin kasar da sadaukar da rayuwarsu wajen kare martabar kasar da kuma al’ummarta musamman wadanda suka mutu a yakin basasar da aka kai karshensa a shekarar 1970.

Haka kuma an zabi ranar kasancewar ita ce ranar da aka yi wa Firimiyan Arewa na farko, Alhaji Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, da kuma Firaiministan farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa gisan gilla.

Da wannan ne Aminiya ta bankado shafuka na tarihi inda ta kawo muku wasu abubuwa da ya kamata ku sani game da yakin basasar kasar:

An yi yakin basasa a Najeriya wanda ake kira yakin Biyafara a tsakanin shekarar 1967 zuwa 1970 tsakanin dakarun gwamnatin tarayya da na ’yan awaren Biyafara.

Janar Yakubu Gowon ne Shugaban Kasar Najeriya a wancan lokaci yayin da marigayi Laftanar Kanar Odumegwu Ojukwu ya kasance Shugaban masu fafutikar neman kafa yankin na Biyafara bayan ya yi Gwamnan mulkin soja a yankin Gabashin Najeriya a shekarar 1966.

Yakin basasar ya wakana ne a sakamakon rigingimu na kabilanci, albarkatun kasa da banbancin addini da siyasa wanda hakan ya sanya ’yan kabilar Ibo wanda galibi suka fi rinjaye a yankin Gabashin Najeriya suka nemi ballewa tare da neman cin gashin kasar.

An fara yakin ne a ranar 6 ga watan Yulin 1967, yayin da sojojin Najeriya suka tumke damarar kwato yankin Gabashin Kasar da har an yi masa lakabi da Biyafara.

An yi kiyasin cewa mutum dubu dari biyar zuwa miliyan uku ne suka rasa rayukansu a yakin wanda aka kwashe shekaru biyu da rabi ana gwabzawa.

Rashin jituwa da gwargwarmayar nuna fifiko tare da neman mallake albarkatun kasa sun kunno kai a tsakanin kabilun kasar yawanci Hausawa da Fulani a Arewa, Yarbawa a Kudu maso Yamma sai kuma Ibo a Kudu maso Gabas.

An yi juyin mulki har sau biyu a shekarar 1966 – Na farko manyan sojoji da ke tare da Jonhnson Aguiyi Ironsi dan kabilar Ibo ne suka yi wa Firaiminista Abubakar Tafawa Balewa juyin mulki saboda kasancewarsa dan Arewa.

Bayan watanni shida aka sake yin wani juyin mulkin wanda ya dakile na farko, inda galibi manyan sojoji daga Arewa suka yi a ranar 30 ga watan Mayun 1967.

An samu wasu kasashen ketare da suka yi ruwa da tsaki a yakin basasar wajen marawa Najeriya baya da suka hadar da China, Isra’ila, Faransa, Masar, Canada, Amurka da Tarayyar Soviet, dangartakar da har yanzu take ci gaba da wanzuwa.

A ranar 16 ga watan Janairun 1970 ne masu gwagwarmayar kafa yankin Biyafara suka saduda tare da mika wuya wajen maido su cikin Tarayyar Najeriya.

Bayan yakin ne, Janar Yakubu Gowon ya ayyana cewa babu wanda ya yi nasara tsakanin Najeriya da Biyafara, wata magana mai harshen na dattako domin dakile radadi da jin haushi juna.