Ya kamata mu san daga ina muke, a ina muke yanzu, ina muka dosa!
Daga shekarar 1999 zuwa yanzu mun ga musifu da bala’o’i iri-iri, idan za a yi aiki da hankali da ilimi lokaci ya yi da za a tantance dukkan azzalumai da wadanda aka zalunta a Najeriya, domin a kwato wa kowa hakkinsa sannan a hukunta azzaluman.
Kusan kowa ya san tarihin Janar Olusegun Obasanjo, tun a lokacin Janar Murtala Mohammed aka zargi Obasanjo da zama dan kungiyar asiri har Janar Murtala ya sa ranar da za a kore shi daga soja.
Kafin ranar aka kashe Janar Murtala a matsayin Obasanjo na mataimakinsa ya zama Shugaban Kasa, aka bi shi haka, har ya sauka.
Bayan shekara 20 aka fito da shi daga kurkuku ya zama Shugaban Kasa na farar hula, alhali yana zaman daurin rai-da-rai kan laifin cin amanar kasa a lokacin Janar Sani Abacha.
Bayan ya shekara takwas yana mulki don samun dama sai ya nemi ya canja Tsarin Mulkin Najeriya domin ya ci gaba da mulki.
Ni Abdulkarim Daiyabu da na san wancan tarihi, da zan yi takarar dan Majalisar Dattijai mai wakiltar Kano ta Tsakiya a 1983 sai da Hukumar Zabe ta lokacin ta tura ni kotu da wurin SSS da ’yan sanda suka yi min binciken kwakwaf, suka tabbatar ban taba aikata kowane irin laifi ba, sannan suka bubbuga sitamp suka sa hannu, kafin hukumar ta yarda in yi takarar.
Wannan ne ya sa na tashi haikan na yi ta yakar Obasanjo da jam’iyyarsa PDP har muka yi alaka da jam’iyyata ta AD da APP muka yaki PDP da Obasanjo da wadanda suka fito da shi daga kurkuku.
Bayan sun ce shi ne ya lashe zaben, wanda muka tsayar takara a AD/APP, Cif Olu Falae, ya je kotu ya yi rantsuwa a kan lallai Olusegun Obasanjo dan kungiyar asiri ne.
Ya ce, kada a kuskura a rantsar da Obasanjo a matsayin Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Sojojin Najeriya domin dan kungiyar asiri ne (Don’t dare swear-in Olusegun Obasanjo as President, Commander-in-chief of the armed forces of the Federal Republic of Nigeria, he is a member of secret cult).
Dukkan alkalan Najeriya sun sani, Kundin Tsarin Mulkin Najeriya bai yarda dan kungiyar asiri ya yi kowace irin takara ba balle ya zama Shugaban Kasa, amma suka rantsar da Obasanjo a matsayin Shugaban Kasa, bayan su IBB sun soke zaben 12 ga Yunin 1993 (na tikitin Musulmi/Musulmi) na Alhaji MKO Abiola da Alhaji Babagana Kingibe.
Suka rusa kowa da komai, mutane suka fara galabaita.
Duba da yadda Janar Muhammadu Buhari da Tunde Idiagbon suka gudanar da yaki da rashin da’a, jama’a suka sako Buhari a gaba har sai da ya kai ga samun nasarar zabe, sai dai kash, da ya tashi fara mulki sai ya zo da Kabal a karkashin wani dan uwansa.
Tashin farko aka ce wai an sa wa Shugaba Buhari guba a na’urar sanyaya daki ta sa shi rashin lafiya kamar zai mutu, tun daga lokacin komai ya koma karkashin Kabal.
Shugaban Buhari ya zama kamar dan kurkuku, aka hana shi ya ga kowa, aka hana kowa ya gan shi, sai wadanda Kabal suka ga dama.
Babban abin mamaki shi ne hatta masu yin dokoki da aka zaba tare da Buhari har da masu hamayya da jam’iyyar gwamnati, suka kasa hada kai su kalubalanci bala’in da muke ciki na rashin tsaron rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addini da tarbiyya sakamakon rashin lafiyar Shugaba Buhari da hadarin Kabal.
Kamar hadin baki, kansu ba ya haduwa sai a kan sata ko yin cushe a kasafin kudi da ninka kudin kwangiloli da fitar da kudin aiki ba tare da an yi aikin ba.
An zarge su da hada baki da Gwamnan Babban Bankin Najeriya yana ba su bashin biliyoyin Naira ba tare da bin ka’ida ba, an zarge shi da ba su Dalar Amurka a kan farashi mai rahusa suna kusan ninkawa su sayar a kasuwannin bayan fage, abin da ya yi ta dada kara rusa darajar Naira da hauhawar farashi.
Allah kadai Ya san adadin mutanen da aka yi garkuwa da su da wadanda aka kashe ko aka yi wa fyade ko raunuka da adadin kudi da dabbobin da aka kwace musu, bayan sace kudin mai da na harajin Kwastam da sauransu.
Ni a fahimtata kowane daga cikinmu ya taimaka Buhari ya zama Shugaban Kasa ne, bisa kyakkyawan zato zai kwatanta abin da ya yi daga Janairun 1984 zuwa Agusta 1985, amma sai aka samu akasi.
Saboda haka tunda gwamnatin Buhari ta kasa, sai a fara da bincikarta, binciken kwakwaf! domin a gano abin da ya faru.
Adadin kudin gurbataccen mai nawa ta samu daga shekarar 2015 zuwa yanzu, nawa ta ciwo bashin gida da na waje, me da me aka yi da kudin, ina abubuwan da aka yi, a kan nawa aka yi?
A kwatanta da yadda ake yin irin su a wasu kasashen da suka yi da ingancinsu.
Sai kuma a bi kadin duk dukiyar da Kabal da Gwamnan CBN da Ministan Shari’a da sauransu ake zargin sun mallaka.
Albashin kowanne nawa ne? Tun daga kan Shugaban Kasa da ministocinsa da hukumar shari’a da masu yin dokoki na tarayya da jihohi da gwamnoni da mataimakansu da kwamishinoni da masu ba da shawara da iyalansu da masu alaka da su kai-tsaye ko ta karkashin kasa.
Abin da duk aka samu na jama’a a fara kwato su, a soma biyan diyyar rayuka da lafiya da dukiya.
Sannan a hukunta duk wanda aka samu da kowane irin laifi.
Sannan a koma baya tun daga 1999 zuwa 2015.
A yi kamar yadda aka yi na ita gwamnatin Buhari.
Sannan a bi kadin duk abin da ya faru game da rijiyoyin mai da bankuna da filaye da kadarorin gwamnati tun daga lokacin da aka kashe Janar Murtala Ramat Mohammed, aka rusa darajar Naira da bankuna har da CBN da NNPC da Hukumar Shari’a.
Sai a binciko kungiyoyin asiri da masu shigo da hodar Iblis da wiwi da miyagun kwayoyi a Najeriya. Idan azzalumai makiya Allah, makiya bayin Allah za su iya hada kansu domin su zalunci bayin Allah, ban ga abin da zai hana wadanda ake zalunta su hada kai su yaki azzaluman masu yin fashi da mukami ba.
Allah Ya ba mu ikon canjawa tun kafin kowace irin annoba ta duniya ko azabar Lahira.
Amin summa amin!
Abdulkarim Daiyabu, Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya, tsohon Shugaban Jam’iyyar AD na Kasa, tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Ayyukan Noma ta Jihar Kano. 08060116666, 08023106666.