A yayin da Musulmi a fadin duniya ke shugulgulan Babbar Sallar bana, malamai sun kwadaitar kan aikata wasu abubuwa domin samun dacewa.
Dokta Abdulqadir Suleiman Muhammad, malami a Sashen Ilimin Addinin Musulunci na Jami’ar Abuja, ya yi wa Aminiya bayani kan hukunce-hukuncen ranar Babban Sallar Idin Layya da wasu abubuwan da suka danganci ibadar.
Safiyar Babbar Sallah
Daga cikin muhimman abubuwa da ya kamata a aikata a safiyar ranar Sallar Idin Layya akwai rashin cin abinci har sai an sauko daga idi.
Malamin ya ce, “Yana da kyau [mutum] ya tsaftace jikinsa, ya wanke baki, ya sa tufafinsa mafi kyau — in yana da sabo ya saka, in ba shi da shi ya nemi wanda ya fi kyau a cikin kayansa ya sa, sa’annan ya fesa turare.”
Idan lokacin tafiya idi ya yi, ana so mutum ya tafi yana kabarbari har ya isa masallacin, inda ake so ya ci gaba da kabarbarin har zuwan liman.
“Yana da kyau mu sani [cewa] su wadannan kabarbari ana fara su ne tun daga farkon wannan wata (Dhul-Hijja) mai albarka, musamman bayanai da suka gabata a kan cewa ranaku guda 10 na farkon wannan wata suna da muhimmanci matuka.
“Hadisan Manzo (SAW) sun umarce mu da mu yawaita kabarbari da hailala (la’ilaha illal lah) da kuma tahmidi (alhamdulillah) ga Allah Madaukakin Sarki a wadannan ranaku.
“To Musamman ranar sallah rana ce dama ta ambaton Allah kamar yadda ranar sallar idi take da alaka da aikin Hajji.”
Haka aka so mutum ya kasance cikin ambaton Allah da hailala da kuma gode wa Allah Madaukakin Sarki, har zuwa lokacin da liman zai tayar da Sallah.
Sallar idi
Daga nan sai ya takaita kabarbarin har a idar da Sallah, inda za a saurari huduba
“Musulunci ya kwadaitar da cewa a saurari hudubar liman domin sakon da yake dauke da shi a kan al’amuran da suka shafi rayuwarmu ta yau da kullum,” inji malamin.
Yanka dabbar layya
Bayan liman ya kammala huduba, ana kuma so mutum ya shaida lokacin da liman ya gabatar da layyarsa.
Dokta Abdulqadir ya ja hankali da cewa, “Duk wanda ya yi riga malam masallaci ya je ya gabatar da layya kafin liman, musamman wadanda suke cewa za su yanka layyarsu kafin su tafi masallaci, to su sani cewa wannan layyar tasu ba layya ba ce.
“Ya tabbata a cikin Hadisin Manzo (SAW) cewa duk wanda ya kasance ya yi layya kafin ya yi sallah to ya sani cewa wannan layyar tasa ba ta karbu ba.
“Sai mutum ya tabbatar da cewa liman ya yi layya tukuna shi ma zai je ya gabatar da tasa layyar.”
Naman layya
Ga wanda ya samu ikon yin layya, an kwadaitar cewa naman layyar tasa ta kasance abin da zai fara ci a ranar.
Malamin ya ce, “Manzo (SAW) ya kasance ba ya fita ranar idi har sai ya ci abinci, idan Karamar Sallah ce ke nan.
“Idan ya kasance Babbar Sallah ce, Manzo (SAW) ba ya cin abinci kafin ya fita daga gida, har sai ya dawo daga masallaci, kuma naman layyarsa ita take kasancewa abin da ke shiga bakinsa daga fari.”
Ya ce yin hakan ba wajibi ba ne, sai idan mutum ya ga zai iya.
Game da rashin cin abinci sai bayan saukowa daga idi, Dokta Abdulqadir ya ce yin hakan arashi ne da cikon azumi 10 da aka kwadaitar da yi a kwanaki 10 na farkon watan Dhul-Hijja — “Wato daga farkon wannan wata zuwa ranar Idi.
“To ranar Idi ba a yin azumi domin rana ce da Manzon Allah Ya ce ita ranar idi ranar nuna farin ciki ce, domin haka rana ce da ake cin abinci ake shan abin sha da ake kuma ambaton Allah Madaukakin Sarki.”
Ambaton Allah
Ana bukatar a yawaita ambaton Allah a ranar Sallah da ranaku biyu da ke biye da ita (Ayyamut Tashrik).
“Ranaku ne da ake son a yawaita ambaton Allah musamman bayan gabatar da salloli na farilla, har in mutum bai samu yin ambaton Allah a kowane lokaci [ba] ke nan.
Naman layya
Malamin ya ce ana son wanda ya samu ikon yin layya ya raba naman layyarsa kashi uku.
Ya ambato Hadisin Manzon Allah (SAW) da ke cewa ku yi sadaka kuma ku ajiye kashi na ukun domin bukatarku ta yau da kullum na bayan sallah.
Daya Hadisin kuma ya ce, “Ku ci daga wannan nama, ku ba da sadaka daga cikinshi kuma ku ciyar da wasu mutane da suke bukatar wannan nama.
“Hadisan guda biyu suna nuni ne da a raba wannan nama kashi uku ta yadda za a ci da iyalai da kuma wanda ya yi layyar kansa; sannan kashi na biyu ya bayar da sadaka; kashi na uku kuma ya ajiye don bukatar yau da kullum.”
Ba da layyar kudi fa?
Shehin malamin ya bayyana cewa ba a bayar da kudi a matsayin layya ko da mutum ya tsinci kansa a wurin da ba shi da ikon gabatar da ita.
Don haka, “Madamar bai samu ikon yin layyar ba, to babu bukatar cewa zai mayar da abun kudi ya ba da sadaka da shi; Sai dai in yana bukatar yin sadaka ta musamman ya yi, amma ba da sigar layya ba.”
Cinikin naman layya
Ba a so wanda ya yi layya ya sayar da wani bangarenta “wanda ya hada da fata da kuma naman.
“Hadisin Manzo (SAW) ya ce duk wanda ya sayar da fatar layyarsa to ya kwana da sanin cewa ba shi da layya.
“Don haka dukkan abun da yake da alaka da layya na ibada ne wanda mutum zai ci, ya ba da sadaka kuma ya ajiye —hatta fatar kanta sai dai mutum ya ba da ita.”
Sharudan dabbar layya
“Ita layya ana yi ne da dabba wadda ta kasance mai lafiya sosai,” inji Dokta Abdulqadir.
Ya ci gaba da cewa, “Duk wanda ya yi layya da dabba wadda ta kasance mara ido ko kuma mai ido daya ko idonta na da ciwo — ko kuma ido daya ne ke da ciwo — to wannan layyar bai yiwu ba, madamar wannan ciwon ido ya bayyana.
Ba a yin layya da dabba wadda ciwon da ke jikinta ya bayyana. “Wanda ya yi da dabba wadda ta kasance mai karyayyen kafa, madamar karayar ta bayyana, shi ma layyar tasa ba ta yi ba.
Shekarun dabbar layya
Dabbobin da ake yin layya da su su ne tumaki, awaki, shanu ko rakuma.
“Da wadannan nau’o’i na dabbobi da ake kira bahimatul an’am, ake gabatar da layya.”
Idan da tumaki za a yi layya dole su kasance masu akalla wata shida; awaki kuma akalla shekara daya; shanu, shekara biyu zuwa sama; su kuma rakuma akalla shekara biyar.
Shagalin sallah
Dokta Abdulqadir ya bayyan abin da Musulunci ya tanadar game da shagulgulan sallah.
“Su ranakun Sallah …ranaku ne da ake so Musulmi su kyautata zumunci tsakaninsu da ’yan uwa” da kuma makwabtaka.
“Sannan kuma a yi nishadi gwargwadon iko kamar yadda shari’ar Musulunci ta shar’anta, ba yadda mutum yake so ba.
“Ya tabbata a Hadisin Manzon Allah (SAW) wanda Imam Bukhari ya ruwaito cewa ranar sallah wasu mata su uku sun shigo dakin A’isha a yayin da Manzo (SAW) yake cikin wannan daki, suna rawa suna kida suna waka; Manzo (SAW) ya kau da fuska daga gare su.
“Mu lura cewa ya kau da fuska ne daga gare su [amma] bai hana su ba.
“Sai ga Abubakar (RTA) ya shigo yana kara, yana fada cewa ya za a kasance ana kada ganga na shaidan a gidan Manzo na annabta?
“Manzo (SAW) ya ce ya bar su su ci gaba da nuna farin cikinsu, ai wannan rana ta nuna farin ciki ne.
“Kamar yadda dukkan wasu al’ummomi da suka gabata suke da ranakunsu na nuna farin ciki, mu ma Allah Ya huwace mana ranar nuna farin ciki. Wannan rana ita ce ranar idi, wanda ya hada da ranar idi na Karamar Sallah da kuma na Babbar Sallah.”
Ya bayyana cewa Hadisin ya nuna matan “Su kadai suke irin wannan nuna farin cikin nasu ba tare da cakuduwa na maza da mata ba.
“Idan maza suna da bukatar nuna irin nasu farin cikin, su ma sai su kebe kansu, su nuna irin nasu ba tare da sun cakudu maza da mata ba.”
“Wannan shi ne irin farin cikin da ya kamata a nuna, ba wai shari’ar Musulunci tana kore nuna farin ciki ba ne.”
Abin da ake bukata
A dunkule ranar sallah rana ce da ake bukatar a nuna farin ciki tare da ambaton Allah da addu’o’i, “Ba don komai ba sai don yanayin da muke ciki da rokon cewa Allah Madaukacin Sarki Ya yaye mana wadannan fitintinu da muke ciki na rashin tsaro da kuma rashin tabbas na rayuwa da kuma koma-bayan tattalin arziki.
“Ranaku ne da suke da muhimmanci, Allah Madaukaki kuma Yana amsa addu’o’in bayi a cikinsu.
Don haka kar mu shagala! Lallai a cikin wadannan ranaku masu albarka… mu karkata ga komawa ga Allah Madaukakin Sarki, a yayin da kuma muke gabatar da dukkannin farin ciki da kuma ibada da shari’ar Musulunci ta tabbatar mana da su.