Duk lokacin da kakar amfanin gona ta zo, ana sa rai da saukin farashin kayan abinci a kasuwanni, sakamakon shigowar sabo.
Sai dai a bana ba haka abun ya kasance ba a wasu wurare a jihohin kasar nan, ciki har da Arewa.
A Jihar Bauchi, Hukumar Sa-ido da Kare Hakkin masu Cinikayya (FCCCP) ce ta ɗauki gabar yin bincike ta hanyar kai ziyarar ji da kuma gani kan dalilan da suka haddasa hauhawa da ci-gaba da tsadar kayan amfanin gona a kasuwanni.
Wannan lamarin na zuwa ne a lokacin da ake tsaka da girbe amfanin gona da shigo da sababbi kasuwanni.
Kasuwar da jami’an suka ziyarta ita ce ta Muda Lawal da ke garin Bauchi, babban birnin jihar.
Haka kuma, wasu daga cikin dillalan hatsi a kasuwar da suka tarbe su, sun bayyana cewa, kamfanonin sarrafa abincin dabbobi da manyan dillalan sayar da shinkafa da kuma ’yan kasuwar da ke saye kayan abinci, su boye a kasuwannin kauye ne ke haddasa tsadar kayan abinci a kasuwannin jihar.
Aminiya ta ruwaito Shugaban Dillalan Hatsi na Jihar Bauchi, Alhaji Nasiru Adamu, lokacin da yake amsa tambayoyi daga jami’an Hukumar FCCPC da na ’yan jarida.
Ya ce, “Babban abin da ke kawo karancin amfanin gona ta fuskar hatsi, musamman a Bauchi shi ne kwararowar masu sarrafa abincin dabbobi, suna saye hatsi da gyada da waken soya a farashi mai tsada daga manoma.
“Maganar da nake da ku yanzu, akwai kamfanoni da dama daga Kano da Legas da suka mamaye kasuwanninmu na ƙauye, suna saye shinkafa da wake da gyaɗa daga manoma zuwa jihohinsu.
“Kuma farashin da suke saye ya fi wanda muke sayarwa a nan garin Bauchi, domin idan ka sayi tirela ɗauke da masara, za ta ɗauke ka fiye da wata guda kafin ka sayar a kasuwa, amma kamfanonin a shirye suke, su sayi tirela 10 ko fiye da haka ta hatsi a farashi mai tsada kuma cikin kankanin lokaci,” inj i shi.
Ya ce, a halin da ake a jihar, al’umma sun fara nuna damuwarsu a kan yadda farashin abinci ke ci gaba da tashi a kasuwannin jihar babu kakkautawa.
Kasancewar a yanzu haka da yawa daga cikin ’yan kasuwar hatsi a garin Bauchi sun koma Azare da Katagum, saboda manoman noman rani a can sun girbe amfanin gona, sannan ’yan kasuwa na saye hatsin a hannun manoma, suna kai wa kamfanoni a jihohin Kano da Legas.
Ya ce, tsadar mai da haraji barakatai da hukumoni daban-daban suke dora wa masu harkar saye da sayar da amfanin gona sun taimaka wajen ta’azzara lamarin a jihar, baya ga wadanda suke saye su boye don cin kazamar riba.
“Duk da cewa manoman na kara farashinsu, amma wani kalubalen shi ne, manyan dillalai da ke sayen kayan, su ajiye su a shaguna na daga cikin wadanda suke haddasa tashin farashin kayan abinci.
“Baya ga tsadar mai da kuma yawaitar haraji daban-daban daga hukumomin gwamnati a jihohi.
“A makon jiya, mun sayi masara a daya daga cikin shagunan manyan dillalan a kan Naira 51,000 a kan kowane buhu, amma a wannan makon buhun masara ya sake tashi, inda farashinsa ya kai Naira 65,000 (mako biyu da suka gabata).
“Muna ba da shawara ga Hukumar FCCPC da gwamnatin jiha da su fito da wata hanya, ta duba shigowar kayayyaki da fitar su a jihar, yadda kasuwar za ta iya zama hanya daya tilo da irin wadannan kamfanoni ko manyan dillalan da ke tara kayayyaki za su iya saya,” in ji shi.
A jawabinsa ga jami’an hukumar, Shugaban Kasuwar Muda Lawal, Mikail Abubakar Garba, damuwa ya nuna kan yadda ake fitar da amfanin gona daga jihar zuwa makwabtan ƙasashe da wasu mayan kamfanonin da ke zuwa daga makwabtan jihohi da Kudu ke yi, wanda hakan ba zai haifar wa jihar da mai ido ba.
“Wani abin da ke damun mu shi ne fitar da hatsi da sauran kayayyaki daga Nijeriya zuwa kasashen waje, alhali mu ma ’yan kasa abincin bai ishe mu ba.
“Don haka ya kamata gwamnati ta hana fitar da kayan abincin da ake nomawa a Nijeriya zuwa kasashen waje, har sai kasar nan ta iya samar da abinci mai yawa da kanta’’, in ji shi.
Malam Usman Musa, wani mai sayar da hatsi a Kasuwar Muda Lawal, a nasa bayanin dora laifin kacokam ya yi a kan masu saya, su boye.
Ya ce, “Hauhawar farashin hatsi ya samo asali ne daga yadda masu saya, su boye da kuma yawan bukatar kayan abincin a duk karshen wata, sakamakon yadda magidanta ke sayen abinci, wanda hakan ke kara taimakawa wajen hauhawar farashin kayayyakin abincin a karshen wata a Bauchi.”
A bangaren Shugaban Hukumar FCPCC a shiyyar Arewa maso Gabas, Dauda Amadu Waja cewa ya yi, sun ziyarci Kasuwar Muda Lawal da Kasuwar Reliwai da ke birnin na Bauchi ne domin tattara bayanai kai- tsaye daga majiyoyi da masu ruwa-da-tsaki a kasuwannin, musamman shugabannin kungiyoyin kasuwa da ke saye da sayar da kayayyakin abincin.
“Kokarin sa-ido na Hukumar FCCPC ya nuna cewa, ana zargin masu shiga ɓangaren abinci da rarraba shi da suka haɗa da dillalai, da haɗa baki wajen ƙara farashi da tara dukiya da sauran dabarun da ba su dace ba don takaita yawaitar kayayyakin abincin.
“Wannan lamari kan kara haifar da hauhawar farashin kayan abincin, ta hanyar da ba ta dace ba, kuma wannan mugun aiki ne karkashin Dokar Hukumar FCCPA,” in ji shi.
Shugaban ya ce, “Bayan wannan aiki, hukumar za ta samar da takaitaccen rahoton bincikenta, tare da bayar da shawarwari ga gwamnati kamar yadda Sashe na 17 (b) na Dokar Hukumar FCCPA ya tanada.
“Za mu yi hakan ne domin bullo da manyan tsare-tsare da nazari kan harkokin tattalin arziki a Nijeriya, da nufin ganowa da magance matsalar domin tabbatar da daidaita farashi ga al’umma.”
Ya yi nuni da cewa, daya daga cikin ayyukan hukumar shi ne ba da fiffiko wajen saido a kasuwanni don samun daidaiton farashin kayayyakin masarufi da suka shafi abinci don kare muradun masu saye da sayarwa.
“Duk da cewa wannan ziyara a Bauchi aka yi ta, amma sakamakon abubuwan da aka gano ba za su bambanta da na sauran kasuwannin jihohin Arewa ba. Idan ma akwai bambanci kalilan ne.
“Hakika akwai bukatar hada karfi da karfe a tsakanin al’umma da hukumomin da abin ya shafa, wajen kawo karshen lamarin baki dayansa a Arewa da dukkan jihohin kasar nan.