✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Abubuwan da muke so Buhari ya mayar da hankali’

Bayan dawowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga jinyar wata uku da ya yi a birnin Landan da ke kasar Birtaniya a ranar Asabar da ta…

Bayan dawowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga jinyar wata uku da ya yi a birnin Landan da ke kasar Birtaniya a ranar Asabar da ta gabata, daidakun jama’a da kungiyoyi suna ci gaba da bayyana irin abubuwan da suke so Shugaban kasar ya mayar da hankali a kai.

Najeriya dai tana fama da manyan matsalolin da suke yi wa kasar barazana. daya daga cikin matsalolin shi ne rashin tsaro da zaman lafiya a kusan kowane bangare na kasar, inda a yankin Arewa maso Gabas kungiyar Boko Haram ta kara kaimi wajen kai hare-haren kunar bakin wake da na kwanton bauna musamman a Jihar Borno.

Sai kuma matsalar masu neman a raba kasar nan da kungiyar neman kasar Biyafara ta IPOB ke jagoranta, wadda a baya-bayan nan ta sha alwashin yin amfani da makami domin cimma burinta. Sannan ta shiga yin kalaman batanci domin tunzura jama’ar kasar nan. Wannan ya sa wata kungiyar da ta kira kanta gammayar kungiyoyin matasan Arewa bai wa ’yan kabilar Ibo wa’adin zuwa ranar 1 ga Oktoba su bar yankin Arewa. Sannan an rika samun wadansu ’yan siyasa da suke son a sake fasalin kasar nan cikinsu har da toshon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar. Wadannan baya ga batun yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Buhari ta sa a gaba ne wanda yake neman yin awon gaba da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Babachir Lawal. 

Kuma akwai kiraye-kirayen cewa Shugaban kasar ya yi garambawul ga majalisar ministocinsa domin kara mata karsashi, ganin an riga an ci fiye da rabin zangon gwamnatin.

A ranar Litinin da ta gabata, kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF), ta yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari a kan matsayin da ya dauka kan masu neman a raba kasar nan. 

Kakakin kungiyar ACF ta kasa, Malam Muhammad Ibrahim Biu, ya fadi a wata sanarwa cewa, wannan matsayi na Gwamnatin Tarayya a kan batun neman a raba kasa matsayi ne da ACF ta dade tana nanatawa.  “ACF na goyon bayan wannan matsayi na Gwamnatin Tarayya, musamman a kan batun hadin kan kasa. Muna fata jama’a masu neman canja tsarin kasar za su mika koke-kokensu ta hanyoyin da suka dace,” inji shi. 

Game da kalaman batanci ga kabila ko yanki da suka zama ruwan dare a shafukan sada zumunta, kungiyar ACF ta ce, “Yanzu da gwamnati ta dauki shawarar hukunta duk wanda aka kama da yin batanci. ACF tana kira ga jama’a su kauce wa irin wadannan dabi’u su rika mika kokensu ta hanyayoyin da doka ta amince da su.” kungiyar ACF ta yi kira ga gwamnatoci su rika janyo hankalin jama’a kan su runguni zama lafiya domin kwantar da hankalin jama’a. 

Shi kuwa Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir kira ya yi ga Shugaba Muhammadu Buhari ya cigaba da abubuwan da ya fara na ceto kasar nan daga mawuyacin halin da ta shiga. 

Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya kan dawowar Shugaban kasar daga jinya, inda ya ce “Muna yi wa Allah godiya da Ya bai wa Shugaban kasa lafiya  kuma Ya dawo mana da shi gida lafiya. Kuma ina kira a kara tsaurara matakan tsaro a fadar Shugaban kasa.” 

Ya yaba wa Gwamnatin Buhari kan yadda ta samu nasara a fannin tsaro da harkokin noma da bunkasa tattalin arziki da dawo da mutumcin Najeriya a idon duniya.

Shugaban Kasuwar ’Yan Tumatir da ke Farar Gada a Jos fadar Jihar Filato Alhaji Aminu Yahaya Yunusa ya bayyana Shugaba Muhammadu Buhari da garkuwar mutanen Najeriya. 

Alhaji Aminu Yunusa ya ce Buhari  garkuwar mutanen Najeriya ne, domin kafin zuwansa kasar ta shiga mawuyacin hali. “A kullum bama-bamai suna tashi a Najeriya ana kashe daruruwan mutane. A wannan kasuwa kawai mun sayi na’urorin gano bama-bamai na dubban nairori,” inji shi.

Alhaji Aminu ya ce, “Mun yi matukar farin ciki da dawowar Shugaba Buhari, kuma za mu ci gaba da yi masa addu’ar Allah Ya kara masa lafiya. Muna kira kan ya ci gaba da abubuwan da ya faro na tabbatar da tsaro da inganta noma da yaki da cin hanci da rashawa, domin sakamakon wadannan abubuwa da ya kawo yanzu Najeriya ta yi kyau, wadannan abubuwa suna da matukar alheri ga Najeriya.”

Ya yi kira ga ’yan Najeriya su ci gaba da bai wa Shugaban kasar goyon baya da hadin kai kuma su  rungumi harkokin noma, domin a magance halin matsin da ake ciki.

Daga Bauchi kuwa dubban magoya bayan Shugaba Buhari ne suka gudanar da jerin gwano don nuna murnarsu kan dawowar Shugaban gida. Masu gangamin sun zagaye manya da kananan tititunan cikin garin Bauchi, bayan da suka fara daga kofar Wunti suka nufi Titin Ahmadu Bello zuwa Gidan Gwamnatin Jihar suka zarce ta Titin Nasarawa zuwa Fadar Sarkin Bauchi, suka wuce Kasuwar Santaral zuwa Titin kofar Ran zuwa Tashan Babiye a karshe suka dawo Titin Wunti inda suka soke rakumi aka raba namasa sadaka domin godiya ga Allah da nuna murna kan samun saukin da Shugaban ya yi da kuma dawowarsa gida lafiya.

Jagoran gangamin Alhaji Nasiru Umar Gwallaga, wanda shi ne Shugaban Matasan Jam’iyyar APC ta jihar ya shaida wa manema labarai cewa “Wannan fitowar da muka yi mun yi ne domin nuna soyayyarmu ga Shugabanmu Buhari. Buhari yana sanya kafarsa a Najeriya, yana fitowa daga jirgi muka fara gangamin muka zagaye cikin garin Bauchi domin nuna wa jama’a soyayyarmu gare shi.” 

Nasiru Gwallaga ya ce  gangamin ya yi armashi sosai, kuma a karshe sun soke rakumin da suka yi zagayen da shi ne, domin nuna godiyarsu ga Allah bisa wannan ni’ima ta ba Shugaba Buhari lafiya, inda suka roki Allah Ya kara wa Shugaba Buhari lafiya da kwarin gwiwar ci gaba da ayyukan da yake yi na ceto Najeriya daga matsalar tattalin arziki da samar da zama lafiya mai dorewa da niyyarsa ta kawo sauki da walwala ga talakawa. 

A yayin gangamin matasa sun rika maimaita baitocin wakokin Rarara na tsoho ya sauka da kwari da sauran wakokin murnar dawowar Buhari.   

Wani malamin makaranta sakandare Malam Tijjani Kolo ya roki Shugaba Buhari ya mai da hankali kan matsalolin talaka kai-tsaye ta hanyar ba shi ilimi kyauta da kula da lafiya kyauta da samar da guraben ayyukan yi ta yadda za a fito da dimbin kudaden da ya tara wajen farfado da masana’antu da samar da kayayyakin noma cikin sauki domin talaka ya amfana. 

Malam Tijjani ya kara da cewa tunda talakawa su ne suka kawo wannan gwammnati bai dace a ce suna fama da talauci da matsananciyar tsadar rayuwa ba, “Akwai bukatar Shugaba Buhari ya dubi karin kudin fetur da ya yi da matse kudaden kasashen waje da ya yi wadanda suka taimaka wajen kara tsadar rayuwa,” inji shi.

Sai dai ’yan kabilar Ibo sun ce suna nan a kan bakarsu ta neman a raba kasar nan. Wani jagoran masu fafutukar kafa Biyafara mai suna Kwamared Uchenna Madu ya shaida wa BBC cewa kasar ta wuce matakin ci gaba da kasancewa a matsayin kasa guda.

Kwamared Uchenna Madu na kungiyar MOSSOB, wanda ya mayar da martani ga jawabin Shugaba Buhari, ya ce wajibi ne a tattauna matsalar zamantakewar Najeriya.

Kwamared Uchenna ya ce ba a isa a yaudare su ba. Kuma jawabin Shugaban kasar na bad-da-bami ba za a iya yaudararsu ba. “Abin da duk (Buhari) ya fada, mu a wajenmu shirme ne kawai,” in ji shi.

Ya ce jawabin Shugaban kasar ya gaza tabo ainihin matsalar da ta shafi batun hadin kai da dunkulewar kasar wajen guda. “Ba za mu taba yin kasa a gwiwa ba, kan gwagwarmayar tabbatar da kasar Biyafara. Kuma ba za a taba karya mana gwiwa ba, don haka za mu ci gaba da matsin lamba bisa tsarin da muke bi ba tare da tashin hankali ba,” inji shi. 

Wani malami a sashin ilimin addinin Musulunci na Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato, Dokta Abdullah Alhaji Shehu Sakkwato wanda aka fi sani da Baba Sakkwato , cewa ya yi, abubuwan da yake son Shugaba Buhari ya aiwatar don ci gaban kasar nan su ne  “Ina son ya kama dukan azalumman kasar nan da barayi da tsofaffin shugabannin kasa masu laifi. Kuma ya saki marasa laifi da aka tsare ya bar wadanda suka bar kasa su dawo, ya cire wadansu ma’aikatansa da ba su da alaka da canji kuma suna cin hanci. Sannan  ya biya wa malaman jami’o’i na kasar nan hakkokinsu kuma ya cika alkawarin da kungiyar malaman jami’o’in ta yi da gwamnati,” inji shi. 

Wani mai sharhi a kafafe watsa labarai mai suna Nasiru Kainuwa Hadeja a sakon da ya aiko wa Aminiya bayan ya yi addu’a ga Shugaba Buharin sai ya ce: “Baba muna fatan za ka kawar da dila da birrai da ke hana gwamnatikinka ci gaba. Baba mun san kana sane da hannunka mai sanda da uwargidanka ta yi lokacin da ta mayar da jawabi ga rubutun da Sanata Shehu Sani ya yi. Baba Allah Ya kara maka lafiya Ya kuma ba ka ikon sauke nauyin da ke kanka na shugabanci ba tare da gargada ba.”

Shi kuwa Nura Muhammad Mai Apple, Gusau a sakonsa ga Aminiya, cewa ya yi: “Kuraye da su dila da sauran danginsu ciki ya duri ruwa, bayan da suka ga zaki sarkin dawa ya sauka, kuma ya sauka da kwari. Yanzu fatanmu shi ne mu ga yadda sarkin dawa zai yi da kuraye nan da sauran danginsu domin kasa ta samu sukunin ci gaba a samu albarka ta kara sauka a kasa. Allah Ya sa mu ji alheri, amin.”