A ranar Talatar da ta gabata ne Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da sanarwar nadin Alhaji Kabir Muhammad Inuwa a matsayin sabon Sarkin Rano.
Nadin nasa ya zo ne kwanaki kadan bayan da Sarkin Rano Alhaji Abubakar Tafida ya rasu.
Kafin nadin nasa, sabon Sarkin ne Hakimin Kibiya a Masarautar Rano.
Masarautar Rano dai tana cikin masarautun da Gwamna Ganduje ya daga likkafarsu zuwa daraja ta daya, sannan kuma ya kirkiro wadansu masarautun.
Sabon Sarkin dai dan Sarkin Rano Muhammadu Inuwa ne. Shi kuma dan Sarki Isah ne. Haka shi ma dan Sarkin Rano Ilu ne.
Tarihin rayuwarsa
An haifi Alhaji Kabir Muhammadu Inuwa a watan Janairun 1964.
Ya yi karatunsa na firamare a Rano Model, wacce a yanzu aka sauya mata suna zuwa Makarantar Firamare ta Abubakar Ila.
Daga nan sai ya tafi Makarantar Sakandiren Gwamnati ta Dambatta wadda ya kammala a shekarar 1986.
Bayan nan ne ya fara aiki da Hukumar Shige da Fice ta Kasa. Yana wannan aiki ne aka nada shi Dagacin Madaci a yankin Masarautar Rano.
Sarauta
Haka kuma ya zama Hakimin Kibiya.
Bayan da Hakimin Bunkure ya rasu sai aka dauki Hakimin Kibiya aka kai shi Bunkure; sai shi kuma—a lokacin yana Dagacin Madaci—aka yi masa Hakimin Kibiya Kaigaman Rano, mukamin da ya rike na tsawon shekaru takwas.
Majiyar Aminiya ta rawaito cewa sabon sarkin mutum ne mai gaskiya tare da fadinta ko a kan waye.
“Dukkan wani abu da aka zo da shi idan babu gaskiya a ciki to ba ya shiga.
“Mutum ne wanda idan mutane suna da sabani a tsakaninsu yakan yi iya kokarinsa wajen yi musu sulhu”, Inji majiyar Aminiya.