Aminiya ta samu zantawa da fitaccen dattijon nan, Malam Ahmed Joda wanda ya cika shekara 90 kwanan nan, inda ya bayyana cewa duk da shekarunsa, yana iya yin abubuwa da dama da sa’o’insa ba za su yi ba, kamar yadda yake iya cin duk abincin da ya samu. Sannan ya tabo abubuwan da suka faru a tarihin Najeriya da yadda abubuwa suke tafiya a yanzu, inda ya bayyana abubuwan da ke jawo rikicin makiyaya da manoma:
A kwannan ka cika shekara 90 a duniya, yaya ka ji?
To abin babu wani canji da lokacin da na cika shekara 70 da 80. Idan zan iya tunawa har yanzu abubuwan da nake yi na yau da kullum ba su canja ba; ina tashi da sassafe don gudanar da abubuwan da ya kamata na yi a kowace rana. Idan ina Yola, nakan tashi misalin karfe 5:30 na safe, zan je gona, bayan haka zan dawo in yi karin kumallo, sannan idan na ci abincin rana in huta. Sai kuma in koma gona inda ba zan dawo ba sai karfe 6 na yamma, nakan kwanta barci da karfe 10 na dare. Wannan shi ne yadda nake gudanarda rayuwata a kullum.
Shin kana jin zuwa yanzu ka cimma burinka na rayuwa?
Ban san yaya zan amsa wannan tambayar ba; ina yawan jin irin wannan tambayar. Ban yi zaton rayuwata za ta yi tsawo haka ba, saboda yawanci a kasar nan ba a fiye samun tsawon rai kamar haka ba, amma gani a raye kuma cikin koshin lafiya. Ina rayuwa mai dadi; ina cin duk abin da na samu kuma ina zuwa wurare da dama. Babu wasu ka’idoji da aka sa min, haka ne ya sa nake kara godiya ga Allah. Idan na dubi Najeriya wacce ita ce kasar da aka haife ni, tabbas an samu sauyi da ci gaba. A nan Kaduna na yi karatun sakandare. Nakan shafe mako guda kafin na zo Kaduna daga Yola. Amma yanzu tafiya ce ta wuni daya kacal, don haka Najeriya ta ci gaba.
Sa’ar da aka sa ni a makaranta a Adamawa a 1939, lokacin makaranta daya ce kacal a Yola, yayin da gaba daya yankin, wanda ya kunshi Adamawa da Taraba ke da makarantu bakwai. Amma a yanzu akwai akalla jami’o’i biyar a wannan yanki. Ban san adadin makarnatun sakandare da ke yankin ba yanzu, amma dai na san akwai firamare da sakandare a kowane kauye ko birni.
A wancan lokacin asibiti daya ne, amma a yanzu akwai asibitoci da yawa da kuma likitoci da masu jinya. Abubuwa sun canja a gaskiya, sai dai abin takaici shi ne ci gaban da aka samu bai kai yadda na yi tsammani ba a lokacin da na kammala karatun sakandare, a matsayina na matashi a wancan lokaci.
Na taba yin aikin jarida a baya. Na yi rubuce-rubuce masu matukar tasiri da muhimman rahotanni a gidajen rediyo da jaridu. Na samu karuwa da kwarin gwiwa sosai daga wadannan rubuce-rubuce saboda tunanina da hangen nesa sun karu matuka, sannan sun sa abubuwan da nake ganin ya kamata kasar nan ta cimma. Har yanzu ba a cimma wadannan abubuwan ba. A matsayina na dattijo dan shekara 90, ina ganin kasar nan tana da matukar muhimmanci da tarin arziki kuma dukkanmu muna da gudunmawar da za mu iya bayarwa wajen kawo sauyi domin samar da ci gaba da hadin kai fiye da wadanda muke da su a yanzu.
A matsayinka na Bafulatani kuma manomi, me ka fahimta game da fadan manoma da makiyaya a kasar nan?
Tun farkon rayuwa akwai manoma da mafarauta da makiyaya da masunta da sauransu. Dukkan wadannan jama’a suna rayuwa tare; kansu a hade yake, kuma suna taimakon juna domin a samu amfani gona da dabbobi da sauransu. A bangaren kiwon dabbobi, Fulani ko Baroro su aka sani da kiwo kadai. Lokacin da ina yaro na yi kiwo kafin in shiga makaranta. A lokacin ina karatu na san cewa wadannan mutane kansu a hade yake.
To me ya faru yanzu suka zamo makiya juna?
Babban abin da ya faru shi ne, zan iya tunawa a shekarun 1950, an yi kidaya a kasar nan, kuma mutanen Najeriya ba su kai miliyan 40 ba. A yau kuwa an kiyasta cewa mun kai miliyan 200. Wannan ya tabbatar da cewa akwai karin miliyoyin mutane da suke bukatar abinci da wurin zama, kuma suna bukatar kayayyakin more rayuwa kamar tituna da kamfanoni da sauransu, kuma duk wadannan abubuwa ana bukatar su ne a wannan wuri da a da mutum miliyan 40 ba kara fadin kasar aka yi ba.
Adadin mutane yana karuwa, kuma suna amfani da wannan wuri da aka sani a da. Gonaki suna karuwa, inda yawan wuraren da za a yi kiwo yake raguwa. Amma kuma har yanzu muna amfani da tsohon tsarin da a da muke a kai na noma da kiwo, saboda wajen ba zai isa ba.
Fulani makiyaya da suka saba su tashi da safe su kora shanunsu daji domin kiwo, ba za su yi haka ba a yanzu ba tare da sun shiga gonar wani ba. Ka sani cewa su fa ba su da wajen kiwo; suna amfani da daji ne wajen da yake da ciyawa. Don haka a hanyarsu ta zuwa shan ruwa ko neman ciyawa za su iya yin barna a gona.
Me kake tunanin manomi zai yi idan har an bata masa shukarsa?
Zai kai kara wajen ’yan sanda ko kotu. Idan ’yan sanda suka karbi cin hanci daga wajen wannan makiyayi suka sake shi, ka ga manomi ba ya da wata mafita ke nan; zai fi ganewa ya koma ya samu ’yan uwansa su hadu su kai wa makiyaya hari. Watakila a kashe shi a wannan wuri ko kuma fada ya barke a tsakanin bangarorin biyu, wanda zai haifar da kashe-kashe. Wannan shi ne abin da ke faruwa.
Na shugabanci wata kungiya mai zaman kanta mai kawo mafita kan rikicin makiyaya da manoma domin samun zaman lafiya. Tsawon shekara 20 a wannan kungiya tamu muna ta jawo hankali gwamnatoci cewa akwai wani rikici fa wanda yake bukatar a magance shi kafin ya zo ya fi karfin kowa. Babu wata gwamnati da ta saurari wannnan kira ko yanzu da ake cikin rikicin ka taba jin Majilisar Tarayya ta yi magana a kai don kawo karshen abin? Ka taba jin wani Gwamna, musamman a Arewa inda abin ya fi kamari, ya zo da wani tsari domin warware matsalar?
Abu daya da nake ganin shi ne maganin matsalar, a samar wa makiyaya wurin da zai dauke su duka. Musamman wajen da za su rayu don kawo ci gaba. Idan ba haka ba za mu yi ta bata lokacinmu ne kawai.
Yaya za ka bayyana kokari da sadaukarwar ’yan jaridar kasar nan a yau?
Ba za mu kira shi sadaukarwa ba. Gudunmawar dan jarida ita ce samar da bayanai da ilimantarwa da nishadantarwa. Wadannan matakai suna da matukar muhimmanci ga zamantakewar dan Adam da ci gaba a dunkule. Na samu horo na zama dan jarida kuma na yi bita kan samar da labarai na gaske da kuma sharhi a kan abubuwan da suke faruwa a lokacin. Na sa a raina cewa aikinmu shi ne samar da bayanai na gaskiya da kuma isar da sakonnin al’umma. Ba zan ce wai mun yi komai daidai ba, amma dai a matsayinmu na ’yan jarida a wancan lokaci mun san cewa muna da wani babban aiki a kanmu. Duk da cewa akwai ’yancin furta albarkacin baki. Amma a yadda muke bayyana ra’ayinmu a rubuce-rubucenmu dama ra’ayin su kansu jaridun yakan kayatar da wadansu, ta wani banganren kuma yana kawo sabani da rabuwar kawuna.
Najeriya kasa ce da ke da kabilu da addinai daban-daban, amma muna da wani tsari na zama tare wanda muka samo daga Turawan mulkin mallaka. Idan ka dubi kasar Birtaniya za ka ga suna da kabilu hudu; akwai Ingilishi akwai Scottish da Wales da Irish. Dukkansu suna da harsunansu daban da kuma yadda suke gudanar da rayuwarsu. Wadannan rabe-rabe suna nan amma duk da haka ba za ka ji jaridunsu suna kawo rahotannin da suka shafi batanci ga wata kabila ko addini ba kamar yadda muke yi a Najeriya.
A yanzu muna fama da rikicin rashin tsaro a kasar nan, musamman a Arewa. Muna fama da rikicin Boko Haram da na manoma da makiyaya ga garkuwa da mutane da fashi da makami ga fyade da abubuwan da suka jawo tabarbarewar iyali da sauransu. Wannan rikici ya shafi kusan dukkan al’ummar da ke wannan yanki.
Mutane da dama suna da ra’ayin cewa Arewacin Najeriya na samun koma baya, sakamakon yadda ’yan siyasar yankin suka kauce daga turbar magabata.
Mene ne ra’ayinka game da haka, lura da yadda ka ga jiya kake ganin yau?
Tambaye ce wannan mai wuyar amsawa. A Jamhuriya ta Farko lokacin da muka samu ’yancin kai muna da shugabannin da suka samu kyakkyawar tarbiyya daga gida, wadanda suka yi fadi-tashi tun daga farko har suka kai ga wani mataki a rayuwa kuma suke da hikimar ririta dan abin da ake da shi wajen samar da kyakkyawan sakamako kuma suka yarda cewa za su bi doka da oda sau-da-kafa.
Ga yankin Arewa mutane irin su Sardaunan Sakkwato da Sa Kashim Ibrahim da Dan Mahmudu Ribadu da Isa Kaita da Peter Achimogu sun kasance wadanda suka fahimci yadda ake jagorancin al’umma a siyasance. Ire-irenmu da muka kasance masu biye da su mun koya daga gare su, muna musu kallon mutane ne da Allah Ya zaba don haka muka amince cewa ai su shugabanni ne na kwarai. Kuma ina ganin kusan haka abin yake a yankin Yarbawa. Sai dai yankin Ibo ya sha bamban ta yadda ya habaka, amma idan ka kira sunan Zik; to dukkansu za ka ga suna girmama shi ainun.
Abin bakin ciki da ya faru a shi ne na kutsen soja a ranar 15 ga watan Janairun 1966 wanda ya sauya dukkan wadannan abubuwa. Mutanen da a da ba a taba jinsu ba; kuma ba a ma sansu ba, kwatsam suka taso suka samu kansu a shugabanci. Ina ganin wannan yana da nasaba da yadda jama’a suka fara tunanin kowa idan dai har yana da rediyo da kuma bakin bindiga to zai iya zama shugaba a dare daya.
Ina ganin wannan shi ne dalilin da ya sa har yanzu muke cikin matsaloli a Najeriya. Sai dai kuma hanzari ba gudu ba, mun ma yi sa’a da ya kasance sojojin da suka yi juyin mulkin a ranar 15 ga Janairun, sun samu kyakkyawan horo. Sun san makamar aikinsu kuma sun iya ririta arziki. Sun fahimci nauyin da ya rataya a wuyansu a lokacin; kuma suka taki sa’ar samun kwararrun ma’aikatan gwamnati da suka dafa musu.
Abin da muka rasa yanzu shi ne rashin kyan hali da rashin tarbiyyar sanin makamar aiki. Amma ina ganin idan muka fadada batun, to sai mu zargi ’yan jarida. Muna da tunanin cewa da zarar an zabi mutum a matsayin siyasa; to za ka iya yin duk abin da ka ga dama da kai da jam’iyyarka. Amma abin ba haka yake ba, domin kuwa ai gwamnati kullum tana nan; ba zai yiwu ka rusa tsarin a daren daya ba.