Shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana a kan cutar Coronavirus, amma ba ta hanyoyin da aka saba ba.
A wannan karon dai Shugaban na Najeriya ya zabi ya yi magana ne ta wata makala da ya rubuta a maimakon ta gidan rediyo ko talabijin.
“A ’yan kwanakin da suka gabata, na samu cikakkun bayanai a kan halin da kasa ke ciki game da annobar COVID-19 daga hukumomin tarayya da abin ya shafa da ma Gwamnatin Jihar Legas”.
Don haka ne ma, a cewar Shugaba Buhari, “na amince” da daukar wadansu matakai.
Na farko shi ne “Sakin tallafin Naira biliyan 10 nan take ga Gwamnatin Jihar Legas, inda nan ne cibiyar wannan annoba ta COVID-19 a Najeriya” don ba ta damar kara kaimi wajen shawo kan cutar da hana ta kara yaduwa”.
Abu na biyu kuma, inji Shugaban na Najeriya, shi ne “Sakin Naira biliyan biyar na asusun musamman a kan yaki da cutar nan take ga Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yauduwa (NCDC) don ta samar da kayan aiki ga jami’anta ta kuma kara yawansu a cibiyoyinta da dakunanta na bicike a fadin kasa”.
- Coronavirus: Rundunar sojin Najeriya ta yi shirin kar-ta-kwana
- Coronavirus: Gwamnatin Neja ta dakatar da sallar Juma’a
Shugaba Buhari ya kuma ce ya umarci hukumar ta NCDC ta yi wa jami’anta da suka yi ritaya kiranye, wadanda ke kasashen waje don karo ilimi ko horo kuma a dawo da su.
“Tuni ma Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta fara aikin kwaso wasu kwararrunmu da ke Tsakiyar Afirka don ba su damar taka rawa a yunkurin da ake yi a kasa”.
Game da iyakokin kasar kuwa, Shugaba Buhari cewa ya yi, “Na ba da umarni a rufe filayen jirgin sama na kasa-da-kasa da iyakokin kasa nan take har tsawon makwanni hudu a matakin farko”, da nufin aiwatar da wasu manufofi da samar da abubuwan da suka dace don kula da wadanda ake zargin suna dauke da cutar, da wadanda aka tabbatar sun kamu, ba tare da wasu masu shigowa da ita sun rikirkita al’amura ba.
Daga nan sai ya rarrashi wadanda wadannan matakai ba su yiwa dadi ba, yana cewa, “sai dai hakan ya zama dole domin shi ne maslahar galibin al’umma”.
Bugu da kari, a cewar Shugaba Buhari, “Mun kuma dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa na fasinja da nufin hana cutar yaduwa zuwa wasu sassan kasar nan”.
Da ya juya ga batun tattalin arziki kuma, Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba da matakan da ya ce Babban Bankin Najeriya ya dauka don takaita mummunan tasirin annobar a kan rayuwar galibin ’yan Najeriya.
“A halin da ake ciki, na umarci Ministan Ciniki da Masana’antu da Zuba Jari ya hada gwiwa da Kungiyar Masu Masana;atu ta Najeriya don tabbatar da cewa an ci gaba da sarrafa muhimman abubuwa kamar abinci, da magunguna, da kayan aikin asibiti”.
Shugaban ya kuma yi kira ga ’yan Najriya su yi biyayya ga ka’idojin kiwon kafiya da hukumomin lafiya na tarayya da na jihohi ke fitarwa, musamman game da tsaftar jiki da yin nesa da juna.
“A yanzu dai ina tabbatar wa daukacin ’yan Najeriya cewa gwamnati ta kuduri aniyar kare dukkan ’yan Najeriya”.
sai dai Shugaban bai ce komai a kan ko za a ayyana dokar ta-baci ta tsayar da komai a kasar; matakin da wasu ke ta kira ga gwamnatin ta dauka.
Haka ma bai ce komai ba a kan ko gwamnati za ta bayar da tallafi kai-tsaye ga ‘yan kasa wadanda ake ta daukar tsauraran matakan hana su gudanar da harkokinsu, kamar yadda wasu suka yi kira.