✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abubuwa 8 da Abba Kyari ya yi a kwanaki 10 da suka wuce

Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Najeriya, Malam Abba Kyari, yana cikin mutanen da aka tabbatar suna dauke da cutar Coronavirus, wadda mai yiwuwa ya kamu…

Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Najeriya, Malam Abba Kyari, yana cikin mutanen da aka tabbatar suna dauke da cutar Coronavirus, wadda mai yiwuwa ya kamu da ita yayin ziyarar da ya kai Jamus.

Tun bayan dawowarsa dai, Malam Abba Kyari ya halarci wasu wurare ya kuma gana da wasu mutane yayin gudanar da ayyukansa.

Ga abubuwa takwas da Shugaban Ma’aikatan ya yi a wadannan kwanakin tun bayan dawowarsa ranar 14 ga watan Maris:

  1. Jim kadan bayan dawowarsa a ranar ta 14 ga watan Maris, Malam Abba Kyari ya halarcin daurin auren dan Sufeto Janar na ’Yan Sanda Muhammad Adamu. Wasu daga cikin manyan mutanen da suka hallara a wurin su ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, da hamshakin dan kasuwa Alhaji Aliko Dangote.

 

  1. Ranar 16 ga watan Maris ya halarci ganawar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi da gwamnoni ’yan jam’iyyar APC, har ma suka dauki hoto. Gwamnoni 16 ne suka halarci ganawar: Babagana Zulum na jihar Borno, da Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas, da Dapo Abiodun na Jihar Ogun, da Godwin Obaseki na Jihar Edo, da Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, da Muhammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa. Sauran su ne Abdulrahman Abdulrazaq na Jihar Kwara, da Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, da Abubakar Sani Bello na Jihar Neja, da Simon Lalong na Jihar Filato. Sai kuma Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo, da Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, da Adegboyega Oyetola na Jihar Osun, da Aminu Bello Masari na jihar Katsina, da Hope Uzodinma na Jihar Imo, da kuma Inuwa Yahaya na Jihar Gombe.
Malam Abba Kyari (na uku daga dama) da wasu daga cikin mahalarta taron gwamnonin APC da Shugaba Muhammadu Buhari
Malam Abba Kyari (na biyar daga dama) ya dauki hoto da wasu daga cikin mahalarta taron gwamnonin APC da Shugaba Muhammadu Buhari
  1. Kafin taron gwamnonin na APC da Shugaba Buhari kuma, Malam Abba Kyari ya gana da Shugaban Jam’iyyar Adams Oshiomole.

 

  1. Ranar 17 ga watan Maris, Shugaban Ma’aikatan na Fadar Shugaban Kasa ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa garin Okene don yin ta’aziyya ga iyalan Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda mahaifiyarsa, Hajiya Hauwa’u Ozoho, ta rasu. A cikin tawagar akwai Ministan Ayyuka na Musamman George Akume, da Minsitan Yada Labarai da Al’adu Lai Mohammed, da Minista a Hukumar Yankin Babban Birnin Tarayya Ramatu Tijjani, da Minsita a Ma’aikatar Harkokin Waje Zubair Dada, da Babban Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara a kan Yada Labarai Garba Shehu.
Malam Abba Kyari da Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi
Malam Abba Kyari yana hannu da Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi lokacin da ya jagoranci wata tawaga suka yi wa gwamnan ta’aziyya
  1. A wannan ranar dai ya halarci wata tattaunawa da Majalisar Masu Bai wa Shugaban Kasa Shawara a kan Tattalin Arziki, a karkashin jagorancin Farfesa Doyin Salami, har ma ya dauki hoto tare da su. Sauran mambobin majalisar su ne Dokta Mohammed Sagagi, da Farfesa Ode Ojowu, da Dokta Shehu Yahaya, da Dokta Iyabo Masha, da Farfesa Charles Chukwuma Soludo, da Dokta Bismarck rewane, da Dokta Mohammed Adaya Salisu.

 

  1. Ranar 18 ga watan Maris, Malam Abba Kyari ya halarci zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC). A zauren majalisar dai kujerarsa na kusa da ta Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha wanda kan zauna tsakaninsa da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo.

 

  1. Ranar 19 ga watan Maris, Malam Abba Kyari ya halarci kaddamar da Kwamitin Gudanarwa na Ayyukan Jinkai na Kasa, wanda Ministar Al’amuran Jinkai da Agajin Gaggawa Sadiya Umar Farouq ke shugabanta, ya kuma dauki hotuna a wurin. Mambobin kwamitin sun hada da Mai Ba Shugaban Kasa Shawara a Kan Al’amuran Tsaro Babagana Monguno, da shugaban Kungiyar Gwmanonin Najeriya, da Ministan Tsaro, da Ministan Harkokin Cikin Gida, da Ministan Shari’a, da Minista a Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsare-tsare, da Babban Hafsan Rundunonin Tsaro, da Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa, da Babban Hafsan Rundunar Sojin Ruwa, da Babban Hafsan Rundunar Sojin Sama, da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, da gwamnonin jihohin Borno, da Yobe, da sauransu.

 

  1. A ranar 20 ga watan Maris, an ga Shugaban Ma’aikatn na Shugaban Kasa a masallacin Juma’a.

Zuwa yammacin ranar Talata dai an ba da rahoton cewa ya killace kansa a gidansa dake Gundumar Maitama, amma wasu majiyoyi sun ce akwai yiwuwa za a komar da shi wata cibiyar kiwon lafiya inda za a bas hi cikakkiyar kulawa.