✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 7 da za a iya yi da ‘dukiyar Abacha’ $311m

Da dala miliyan 311 da gwamnatin Najeriya ta karbo daga cikin kudaden tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha, za a iya gina kananan asibitoci wadanda…

Da dala miliyan 311 da gwamnatin Najeriya ta karbo daga cikin kudaden tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha, za a iya gina kananan asibitoci wadanda ake kira primary health centres guda 5,500, ko kuma a gina gidaje na zamani masu dakunan barci biyu-biyu guda 40,333 domin magance matsalar rashin gidaje a kasar.

Za kuma a iya amfani da kudin a gina azujuwan karatu guda 35,920, wanda zai rage matsalar rashin azujuwa a kasar da kashi 15.5 cikin 100.

A yanzu a farashin gwamnati, $1 tana daidai da N390 ne.

Aminiya ta ruwaito cewa kudin Naira biliyan 121.3 ne kuma za a iya amfani da su wajen gudanar da dayan ayyukan nan da za mu zayyana.

Gidaje 40,000 ga ‘yan Najeriya

A shekarar 2019, Bankin Lamunin Gidaje na Najeriya, (FMBN) ya ce kasar na bukatar karin gidaje miliyan 22.

Bayanai daga Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje sun nuna cewa za a iya gina gida na zamani mai dakunan barci guda biyu wato two-bedroam flat da Naira miliyan 3.

Idan gwamnati ta juyar da kudaden wajen rage matsalar rashin gidaje a kasar, za a samu karin gidaje 40,333. Hakan zai rage kashi 0.2 cikin 100 na matsalar a kasar baki daya.

Kananan asibitoci guda 5,500

Bincike ya nuna cewa daga shekarar 2014 zuwa 2015, Hukumar Bunkasa Lafiya a Matakin Farko ta Kasa, (NPHCDA) ta bayar da kwantiragin gina kananan asibitoci a matakin farko wato PHC a kan Naira miliyan 21.9 kowane guda daya.

Bisa la’akari da wannan kwagilar, gwamnatin tarayya za ta iya amfani da Naira biliyan 121.3 na Abacha din da aka karbo wajen gina kananan asibitocin na matakin farko guda 5,514, su zama kari a kan guda 10,000 da ake da su a kasar.

An kaddamar da shirin sake bunkasa asibitocin matakin farkon guda 10,000 a kananan hukomomi 774 a shekarar 2017.

Gina azujuwa 35,950

Gwamnatin tarayya a karkashin Hukumar Ba da Ilimi ta Bai Daya, (UBEC), za ta iya amfani da Naira biliyan 121.2 wajen gina makarantu 8,980 masu azujuwa hudu,  wanda hakan zai bayar da jimillar azujuwa 35,920.

Hakan zai rage matsalar rashin azujuwa da kasar ke fama da ita a makarantun firamare daga 232,786 zuwa 196,866, wato ragowar kashi 15.5 cikin 100.

Hukumar UBEC ta ce azujuwa hudu za su ci Naira miliyan 13.5.

Wata kididdigar da aka fitar bara ta bayyana cewa makarantun firamare a kasar baki daya na bukatar azujuwa 639,564, amma a lokacin akwai guda 406,778 ne kawai.

Akalla ana bukatar karin azujuwa 232,786 a kasar baki daya, wato karin kashi 36 cikin 100.

Ko a cikin azujuwa 406,778 da ake da su, guda 197,938 a cikinsu wato kashi 49 cikin 100, sun lalace, kamar yadda rahoton ya nuna.

Rijiyoyin burtsatse 190,151

Da kudaden da aka karbo, za a iya gina rijiyoyin burtsatse na zamani guda 190,151 a kasar baki daya, inda za a gina guda 245 a ko wacce karamar hukuma a kan N600,000 ko wacce daya.

Bincike ya nuna cewa rijiyar burtsatse mai kyau tana kamawa daga N300,000 zuwa N600,000.

Hanya mai tsawon kilomita 480

Za a iya shimfida titi mai tsawon kilomita 480 a kan farashin Bankin Duniya na Naira Miliyan 238 kan ko wacce kilomita.

Daga Abuja zuwa Kano bai wuce kilomita 418.7 ba. Sai dai kasancewar ana kara kudaden ayyukan hanya a Najeriya, inda a wasu lokuta ake fitar da kusan Naira biliyan 1 kan ko wacce kilomita.

Amma ko a wannan farashin na Naira biliyan 1 a kan ko wacce kilomita, za a iya shimfida hanya mai tsawon kilomita 100.4, wanda zai kai daga Legas zuwa Abeokuta, sannan a samu ragowar Naira biliyan 14.

Na’urar numfashi 12,440

Da kudaden da aka karbo, za a iya sayo na’urorin numfashi guda 12,440 a kan farashin $25,000 domin masu matsananciyar jinyar coronavirus da suke fama da wahalar numfashi.

Bincike a intanet ya nuna cewa farashin na’urar numfashi yana kamawa daga $25,000 zuwa $50,000.

Motocin bas manya guda 14,261

Za kuma a iya yin amfani da kudaden wajen sayan motocin bas masu daukar mutum 18 na kamfanin Innoson guda 14,261 a kan farashin Naira biliyan 8.

Bincike ya nuna cewa ana sayar da motocin a kan Naira biliyan 8 zuwa 9.

Za a iya kai bas din guda 18 ko wacce karamar hukuma domin saukaka zirga-zirgar mutane.

Shirin gwamnati

Tuni dai gwamnatin tarayya, ta bakin mai bai wa shugaban kasa shawara a kan al’amuran yada labarai, Malam Garba Shehu, ta yi bayani a kan yadda za ta kashe kudin.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Malam Garba ya yi kwaskwarima ga bayanin da ya yi tun farko cewa za a kashe kudin ne a kan wasu manya ayyuka biyar.

A cewar shi, ayyuka uku ne dai za su ci gajiyar wadannan kudi.