✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 5 da za ki sanya a jakar kwalliyarki

Ina fatan ‘yan mata na da jakar kwalliya. Ko mece ce jakar kwalliya? Jakar kwalliya karamar jaka ce da za ki iya adana kayan kwalliyarki…

Ina fatan ‘yan mata na da jakar kwalliya. Ko mece ce jakar kwalliya? Jakar kwalliya karamar jaka ce da za ki iya adana kayan kwalliyarki kamar su; jambaki, gazal, hoda da sauransu. Akwai abubuwa da dama wadanda suka cancanta ki sanya a jakar kwalliyarki don inganta adonki. A yau mun kawo miki kadan daga ciki;

·         Hodar fandeshi: Hoda ce da za ki fara shafa ta a fuskarki kafin ki fara kwalliya. Wannan hodar takan sanya fuska ta yi haske. Ana so ki shafa hodar fandeshi da yatsun hannayenki.
·     Hodar  ‘Concealer’: Wannan hodar na taimakawa wajen boye bakaken tabon ko dabbare-dabbaren da ke fuska. Akan shafa ta ne bayan an sanya hodar fandeshi.
·         Maskara : Akan yi amfani da Maskara don taje gashin ido da kuma sanya wa gashin ido launi. Akwai sababbin kaloli na maskara a kasuwa wadanda za ki iya saya don kara wa gashin idonki kyau.
·         Gazal: Gazal na kara wa idanu haske. Idan kina son idanunki su yi haske sai ki rika sanya gazal.
·         Jan-baki/man baki: Jan-baki ko man baki suna sanya leba laushi. Ki zabi jan bakin da ya dace da launin fatarki don inganta kwalliyarki.