A baya-bayan nan, jaruma Hadiza Aliyu, wadda aka fi sani da Hadiza Gabon, ta karade kafafen watsa labarai, kan wata kara da wani mutum ya maka ta a gaban kotu kan kin aurensa da ta yi.
A ranar 14 ga watan Yunin 2022 wani magidanci mai suna Bala Musa ya maka jarumar a gaban wata kotun shari’ar Musulunci da ke Magajin Gari a Kaduna kan neman kadinsa saboda kin aurensa da jarumar ta yi, bayan shafe tsawon lokaci suna soyayya.
- Da Dumi-Dumi: Atiku ya zabi Okowa a matsayin abokin takararsa
- Zan sake tsayawa takarar Shugaban Kasa a nan gaba – Yahaya Bello
Bala Musa, ya bayyana wa kotun yadda Hadiza Gabon ta yi alkawarin auren shi bayan kashe mata kudi N396,000 da ya yi, amma jarumar ta musanta tuhumar da ake mata, inda ta ce ba ta ma san shi ba.
Jarumar ta kasance a masana’antar shirya fina-finai ta Najeriya; Kannywood da Nollywood tun daga 2009. Ga wasu abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da ita.
- Hadiza Aliyu na da katin shaidar zama ’yar kasa na Najeriya da kuma na kasar Gabon. Mahaifinta Malam Aliyu dan asalin kasar Gabon ne, ita kuwa mahaifiyarta ’yar Najeriya ce wadda ta fito daga Jihar Adamawa.
- Ta yi karatunta na Firamare da Sakandire a Gabon, wadda ita ce kasar da aka haife ta a can. Daga baya jarumar ta zana jarabawar shiga makarantar gaba da sakandire amma ta fasa, wanda ita ce kadai ta san dalilin aikata hakan.
Daga 2013 zuwa 2019, Hadiza Gabon lashe kanbum karramawa daban-daban da suka hada da ‘Best of Nollywood Awards’ a 2013, ‘City People Entertainment Awards’, ‘Kannywood/MTN Awards a 2014’ da kuma ‘African Hollywood a matsayin Tauraruwar Jaruma.’
Kazalika, a 2013, Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bai wa jarumar kanbum girmamawa na musamman.
3. Hadiza Gabon ta zama jakadiyar kamfanin taliyar yara ta ‘Indomie’ da kuma kamfanin sadarwa na MTN da ke Najeriya. A watan Disamban 2018, ta sake zama jakadiyar kamfanin NASCON PLC, wanda wani sashe ne na kamfanin sinadarin girki na Rukunin Dangote da ke Kano.
4. Mutane da dama sun san yadda Hadiza Gabon ta yi fice wajen tallafa wa marasa galihu, ta kafa wata gidauniya mai suna ‘HAG Foundation’ wadda take taimaka wa rayuwar mabukata kan abin da ya shafi ilimi, lafiya da kuma tallafin kayan abinci.
5. A watan Maris din 2016, fitacciyar jarumar ta ziyarci sansanin ’yan gudun hijira da ke Jihar Kano inda ta tallafa musu da kayan abinci, tufafi da sauran kayan amfanin yau da kullum ga mabukatan da matsalar tsaro ta rutsa da su a yammacin Najeriya.