Ranar Asabar ne ake nadin sabon Shehun Bama, Alhaji Umar Ibn Kyari Umar El-kanemi, wanda yake darewa kan wannan kujera bayan rasuwar mahaifinsa ranar 27 ga watan Afrilu.
Ga wasu abubuwa guda hudu da watakila ba ku sani ba game da sabon Shehun:
Matashi ne
Babban abin da ya fi daukar hankali game da sabon Shehun shi ne matashi ne. An haife shi a watan Disamban 1982 wato yanzu shekarunsa 38.
Dan kasuwa ne
Wani abin sha’awa game da sabon Shehun shi ne yadda ya rungumi kasuwanci, ya zama hamshakin dan kasuwa. Duk da ya karanci aikin Akanta (Accountancy a turance) a Jami’ar Maiduguri, wadda ya kammala a 2008, ya yanke shawarar ya taya da kafafunsa. Hakan ne kuma ya sa ya tsunduma kasuwanci a matakin kasa-da-kasa,
Mai saukin kai ne
Duk da an haife shi a gidan sarauta, tun yana yaro ba ka raba shi da sauran yaran gari, tare da su yake wasa. Kuma har yanzu sauran matasan gari ne abokansa, ba ya nuna bambanci ko nuna cewa shi dan sarauta ne.
Manyan Abokanansa sun hada da Bashehu Abba Massa, Abba Abba Kyari, Bashehu Buba Galadima, Abdulmalik Muhammad, da Grema Magamas.
Haziki ne
Alhaji Babakura Bukar wani na hannun daman marigayi Shehun Bama ne; ya siffanta sabon Shehun da cewa haziki ne, mai rikon amana, mai hakuri, mara girman kai.
“Domin a iyaka sanin da na yi masa, ban taba jin an ce ya ci zarafin wani ba”, inji Alhaji Babakura.
Ya kuma ce sabon Shehun mutum ne mai kyauta wanda ba ya kyashin bayar da duk abin da ke hannunsa.
Sabon Shehun ya yi karatun firamare a Bama Central Primary School daga 1988 zuwa 1994; sannan ya je Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Maiduguri.
Bayan ya kammala aji uku a can ne ya koma Makarantar Foundation, wadda ya gama a 2000.