Da sunan Allah, Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya. Bayan haka, yau cikin yardar Allah za mu fara gabatar da wani abu kan tarihin daya daga cikin fitattun sahabban Manzon Allah (SAW), Sa’adu bin Abu Wakkas wanda shi ne ya jagoranci rundunar da ta ruguza Amurkar zamaninsu wato Farisa. Wane ne wannan sahabi kuma mece ce alakarsa da Manzon Allah (SAW), kuma yaya rayuwarsa ta kasance? Idan kuka biyo mu za mu ga amshoshin wadannan tambayoyi da sauransu daga littafin da dan uwanmu Malam Aliyu Muhammad Sa’idu Gamawa ya rubuta kan wannan babban sahabi mai suna “Tarihin Rayuwar Sa’adu Ibn Abi Wakkas). Bismillah:
Daga Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa
Wane ne Sa’adu bin Abu Wakkas:
Cikakken sunan Sa’adu shi ne Sa’adu bin Malik, Abu Wakkas bin Uhaibin bin Abdulmunaf bin Zahrah, Al’amir Abu Is’hak Alkuraishiy Almakkiy. Kuma an haife shi ne a shekara ta 32 kafin Hijirar Manzon Allah (SAW) daga Makka zuwa Madina.Ya hada dangantaka da Annabi (SAW) ta wajen mahaifiyar Manzon Allah, Aminatu bintu Wahab, domin mahaifinta dan uwan Kakan Sa’adu ne. Domin haka ne Jabir (RA) ya ce: “Wata rana muna zaune tare da Manzon Allah (SAW), sai Sa’adu ya doso mu, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ga kawuna, wane ne a cikinku zai nuna min kawunsa?” Hakim ya ruwaito. Ana yi wa mahaifin Sa’adu wato Malik alkunya da Abu Wakkas, wanda shi ne dalilin da ake kiran Sa’ad da Sa’adu dan Abu Wakkas
Yadda Sa’adu ya karbi Musulunci:
Sa’adu bin Abu Wakkas ya riga sahabban Manzon Allah da dama karbar Musulunci. Kuma ya bayyana abin da ya sa ya karbi Musuluncin cikin fadinsa: “Wata rana cikin mafarki na ga kaina a wani wuri mai matukar duhu inda ba na iya ganin komai da ke kusa da ni, sai wani haske na farin wata da na hango daga nesa. Na nufi inda wannan haske yake domin in fita daga duhun da ya rufe ni, ina matsawa kusa da wannan haske, sai na hango Abubakar da Aliyu dan Abu dalib (Allah Ya yarda da su) tuni sun riga ni isa wurin wannan haske. Lokacin da na farka sai na yi tunanin wannan mafarki nawa a karshe na tafi ga Abubakar na nemi fassarar da mafarkina yake nufi. A nan Abubakar ya bayyana mini cewa ai Muhammad dan Abdullahi, amintacce shi ne (ya bayyana) yana kiran mutane zuwa ga wani sabon addini, wanda yake kore bautar gumaka.” Nan take Sa’adu ya yi imani da sakon da Manzon Allah (SAW) ya zo da shi, ya nufi gidansa (SAW) don don karbar Musulunci.
Sa’id bin Musayyib (RA), ya ce, na ji Sa’adu (RA), yana cewa: “Ba wanda ya Musulunta ranar da na karbi Musulunci, kuma har na yi mako guda. Ni ne na uku (a bayan Abubakar da Aliyu) cikin wadanda suka Musulunta.” Buhari ne ya ruwaito.
Wannan ya nuna su Sa’adu ne suka sha tsangwamar kafirai tun farkon bayyanar Musulunci, kuma a gabansu duk hukunce-hukuncen Musulunci suka sauka, (Allah Ya kara masa yarda da sauran sahabbai).
Adawar mahaifiyarsa ga shigarsa Musulunci:
Mahaifiyar Sa’adu mai suna Hamnah ta fito ne daga kabilar Bani Umayya, kuma tana da daraja da shahara a cikin danginta da mutanen Makka. Wata rana sai ta riski Sa’adu (RA) yana karatun Alkur’ani cikin sauti mai sanyi, sannan ta gan shi ya tashi yana yin wata ibada bakuwa a gare ta. Don haka sai ta tambaye shi abin da yake yi. Sa’adu ya ce, ya karbi addinin da Annabi Muhammad (SAW) ne ya zo da shi. Kuma yana bukatar ita ma ta shigo wannan addini, duk da cewa a lokacin a cikin sirri ake karbar Musulunci.
Wannan al’amari ya fusatar da mahaifiyar Sa’adu, don haka nan take ta ce, ya yi watsi da wannan sabon addini ya koma zuwa ga abin da iyayensa suka yi imani da shi kuma suke bauta mawa. Sa’adu ya shaku da mahaifiyarsa sosai kuma yana matukar girmama ta tare da kyautata mata, amma da ya dubi matsayin da ya samu kansa a ciki na zamansa Musulmi, kuma ya dubi umarnin mahaifiyarsa na ya kafirce, sai ya yanke shawarar ya bijire wa umarninta na ya koma bautar gumaka, alhali ya gamu da hasken Musulunci, imani ya ratsa shi. Mahaifiyar ta yi bakin kokarinta wajen maganganu da lalama da hikima, amma ta gaza shawo kansa kan ya fita daga Musulunci.
Da ta ga ta gaza shawo kansa ta hanyar lalama da jawo ra’ayi, sai ta fito masa ta hanyar barazana domin ta girgiza zuciyarsa. Ta ce, ba za ta sake cin abinci ba ko shan wani abin sha ba, har sai Sa’adu ya fice daga sabon addininsa. Idan kuma bai fita ba, to haka za ta ci gaba da zama cikin yunwa da kishin ruwa har ta mutu! Ganin mahaifiyar Sa’adu ta fara aiwatar da kudirinta na daina cin abinci ko shan abin sha, kuma hakan ya fara barazana ga rayuwarta, sai mutane suka fara surutai ga Sa’adu kan rashin damuwa da halin da mahaifiyarsa take ciki. Sai jama’a suka dauke shi zuwa ga mahaifiyar tasa domin ya ga matsanancin halin da ta shiga, ko ganinta zai karkato da hankalinsa ya bar Musulunci a warware wannan matsala.
Sa’adu ya gan ta ya nuna tausayarsa da damuwarsa a kan halin da mahaifiyarsa take ciki, amma sai karfin imaninsa ga Allah ya rinjayi wani tausayin na dan Adam. Don haka, sai ya ce: “Na yi imani da Allah, ya mahaifiyata! Da za ki samu rai guda dubu, kuma ki rika rasa ran nan daya-bayan daya (ta bin irin wannan hanya da kika dauko), ba zan sauya ra’ayina in fita daga addinin Allah ba! Saboda haka ko ki ci abinci, ki sha abin sha, ko ki ci gaba da kauracewa, wannan ba zai sauya ni ba!”
Da mahaifiyar ta ji wadannan kalamai na Sa’adu ta san cewa ba ya da niyyar rabuwa da imaninsa, tilas ta hakura ta ci gaba da cin abinci da shan abin sha kamar yadda ta saba. Wannan abin da ya faru ya yi daidai da fadin Allah (SWT) cewa: “Kuma Mun yi wasiyya ga mutum (wasiyyar) kyautatawa ga iyayensa, kuma idan suka tsananta maka domin ka yi shirka da Ni game da abin da ba ka da ilimi gare shi, to kada ka yi musu da’a. Zuwa gare Ni makomarku take, sannan in ba ku labari ga abin da kuka kasance kuna aikatawa.” (Ankabuti: 8).
Duk da cewa Hamnah mahaifiyar Sa’adu ta koma ci da sha kamar yadda ta saba, amma ba ta hakura baki daya ba, game da kudirinta na ganin Sa’adu ya yi watsi da addinin Musulunci.
Domin haka sai ta yi gayyar mutane masu yawa a kan su taimaka su kama mata Sa’adu idan ya zo gida domin ta daure shi, a hana shi fita har karshen rayuwarsa. Sai dai da Sa’adu ya gano wannan shiri, sai ya kaurace wa gidan ya koma inda ya fito domin kauce wa tarkon dauri da aka shirya masa. Haka dai ta yi ta yin yunkuri domin raba Sa’adu da imaninsa da addininsa, wani lokaci cikin ruwan sanyi, wani lokacin kuma cikin barazana da tsanantawa, amma duk da haka Sa’adu bai yi watsi da addinin Musulunci ba, inda ya ci gaba da jure duk take-takenta da musgunawarta.
Ustaz Aliyu Gamawa yana zaune ne a garin Gamawa da ke Jihar Bauchi, kuma za a iya samunsa ta tarho kamar haka: 08023893141, 08035829071.