Sahugaban jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce abin kunya ne ga Sahugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika ragamar shugabancin Najeriya ga jam’iyyar adawa a 2023.
A cikin wata tattaunawarsa da Sashen Hausa na BBC, Sanata Abdullahi ya ce Shugaba Buhari ya fi kowa son ganin APC ta lashe zabe mai zuwa.
- An sace basaraken Fulani a kan hanyarsa ta dawowa daga taron zaman lafiya
- DAGA LARABA: Yadda Son Mata Da Dukiya Ke Raba Zumunci
Sai dai ya musanta rade-radin da ake yi cewa Buharin ya yi watsi da harkokin yakin neman zaben jam’iyyar, inda ya ce ba zai yiwu ya kyale aikina na shugabancin kasa saboda na jam’iyya ba.
Ya ce, “Alhamdulillahi abubuwa na tafiya yadda muke so, kuma kowa a cikin tafiyarmu na ganin alamun nasara. Muna da kwarin gwiwar samun nasara, kuma dukkan sauran jam’iyyu ma sun san a gaba da su muke.
“Duk wanda ya ce maka yana son APC ta lashe zaben nan fiya da Buhari karya yake yi. Dalilina a fadar haka kuwa shi ne saboda abin kunya ne gare shi ya mika mulki ga jam’iyyar adawa wacce ba tashi ba.
“Abin da mutane da dama suka kasa fahimta shi ne Muhammadu Buhari shi ne Shugaban Kasa, kuma ya yi rantsuwar cewa ba zai nuna bambanci ba. Saboda haka ya zama wajibi ya yi taka-tsantsan don kada wasu su zarge shi da cewa yana yi wa APC aiki a maimakon Najeriya.”
Shugaban na APC ya kuma ce sam jam’iyyarsu ba ta tsorata da irin gangamin da jam’iyyun adawa suke tarawa ba a wuraren tarukansu.