Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya ce yunkurin da wadansu gwamnonin Kudu suke yi na karbe Harajin kayan alatu (VAT) a jihohinsu wasan yara ne.
Wannan mataki ne da gwamnonin jihohin Ribas da Legas suka fara dauka, yayin da sauran gwamnonin Kudu suke kokarin koyi da su.
- ’Yan bindiga sun aike wa mutanen Shinkafi wasikar hari
- Ciyo wa Najeriya bashi zalunci ne da bautar da na baya —Sheikh Nuru Khalid
A wannan tattaunawa da Aminiya gabanin taron Kungiyar Gwamnonin Kudu, Gwamna Masari ya ce lamarin nasu wasa ne:
Ku biyo mu:
Wata 18 suka rage ka kammala wa’adin mulkinka na karshe, da me kake so a rika tunawa da kai?
Tambaya ce wannan mai tsauri duk da cewa amsarta babu wuya.
Kowane shugaba yana so a rika tuna shi a matsayin wanda ya zo ya aiwatar da abubuwan da suka kawo sauyi daga yadda ake tafiyar da mulkinsu.
Ina so a rika tuna ni a matsayin wanda ya hidimta wa al’umma ba wanda mutane suka hidimta masa ba.
Wani babban abin lura shi ne yadda muke aiki tukuru wajen ganin mun bar ofis yayin da zaman lafiya ya dawo daram cikin al’ummarmu.
Babu shakka idan har za mu yi nasarar dawo da zaman lafiya cikin al’ummarmu, to, hakika kwalliya ta biya kudin sabulu na kasancewarmu a kan mulki.
Mun zo mun tarar da matsalar tsaro kwance a kasa, ta dade tana addabar mutane amma na tabbata idan har za mu yi nasarar sauya lamarin to tarihi ba zai taba mancewa da mu ba.
Wannan shi zai nuna halin tausaya wa al’umma da nuna babu bambanci a tsakanin masu mulki da wadanda ake mulka. Mu masu hidima ne ba mashayan jini ba.
Gogewata a siyasa, musamman kasancewata a majalisa, ta tabbatar min da cewa ’yan majalisa ba kananan shugabanni ba ne.
Idan har muna kallon shugabanci a matsayin dama ta hidimta wa al’umma to an kama hanyar ci gaba mai ma’ana.
Har ila yau ina so a rika tuna ni a matsayin wanda ya zo ya dora harsashi da tubali ta yadda wadanda za su zo bayanmu su dora su yi mana zarra wajen kawo ci gaba fiye da mu a siyasance da kuma a gwamnatance.
Kamar yadda nake yawan fada ne, manufata ita ce hidimta wa al’umma.
Ina yin aiki tukuru wajen ganin na tsaya tsayin-daka a kan abin da nake fada ba wai mai cika baki ba.
Nakan furta, tare da aikata duk abin da na yi imanin shi ne daidai ko da ya bakanta wa wadansu.
Ka taba tunanin lamarin hare-haren ’yan bindiga musamman a karkara zai kai yadda yake a yau?
Ban taba tsammanin lamarin zai girma ya kai yadda yake a yau ba. Ina ganin ya kamata al’ummarmu su rika daukar darasi daga tarihi, musamman sauran kasashe.
Lokacin da muka zo mun tarar da batun satar shanu ne, a wasu lokuta hade da kisan kai.
Babu batun a ga wani Bafulatanin asali ko Bafulatana sun shigo kauyuka ko kasuwanni don yin tallar nono ko gudanar da wasu harkokinsu domin kungiyoyin ’yan sa-kai suna kashe Bafulatani ko Bafulatana a duk inda suka gan su. Wannan shi ne abin da muka zo muka tarar.
Ba mu fi wata shida zuwa bakwai da kama mulki ba, aka yi wa mutane fiye da 140 yankan rago a tsakanin kananan hukumomin Faskari da Sabuwa. An samu shawarwari da dama daga lokacin.
Daga cikin irin shawarwarin akwai mu hadu waje guda mu da muke yankin Arewa maso Yamma saboda yawancin jihohin da suke fuskantar matsalar daga yankin suke kuma suna karkashin jagoranci hukumar soji guda daya.
Mun amince da hakan kuma mun hada kudi inda aka fara aikin tsaro da su kuma komai yana tafiya daidai da jami’an tsaron; ciki har da jami’an shige-da-fice.
Daga baya kuma muka ankara cewa dole ne fa kowanenmu ya koma jiharsa.
Bayan mun dawo gida ne sai muka fara duba jagorancin kungiyar Fulani ta Miyetti Allah.
Bayan sun gudanar da zabe sai aka yi dace wanda suka zaba a matsayin shugaba tsohon ma’aikaci ne kuma mataimakin darakta.
Ta hannunsa ne muka samu damar ganawa da sauran shugabannin al’ummar Fulani.
Ta haka muka gano da yawan wadanda suka shiga daji, wadanda an tursasa musu hakan ne, sai muka fara tunanin yadda za mu gana da su mu kuma jawo su kusa.
Na tura musu da ayari mai karfi tare da shugabannin Miyetti Allah inda a hankali, da yawa daga cikinsu suka fara yarda su ajiye makamai. A wancan lokacin ’ya’yansu ne suke ba su umarni.
Wannan ne ya kai ga ajiye makamai fiye da 350 ciki har da bindigogin AK47 da gurneti-gurneti da bindigogi kirar gida, inda aka yi bikin karbar su.
Hatta kasurgumin dan bindigar nan, Buharin Daji, ya halarci bikin da aka yi a nan Kankara.
Mun samu zaman lafiya a lokacin na kimanin wata 24, in ban da ’yan hare-haren da ba za a rasa ba nan da can. Kasuwanni suka dawo ci kamar yadda suke a baya.
Daga lokacin muka fara gina makarantu; inda muka gina guda 10; da kananan asibitoci 10.
Mun kuma fara bude labin shanu; inda muka kashe kimanin Naira miliyan 100 don bude labin shanu.
Sannan mun yi kokarin bude sauran labin shanun da makiyaya ke bi yayin kaura.
Mun mika wa Gwamnatin Tarayya bukatarmu tare da kokon bararmu, sai dai abin takaici, sai aka siyasantar da lamarin.
Sai aka cim ma cewa za a raba kudin ne daidai wa daida tsakanin dukkan jihohi, inda Jihar Katsina ta samu kason Naira miliyan 200 kacal.
Yayin gabatowar shekarar 2019, abin da muka yi a Jihar Katsina ko Jihar Zamfara ba ta yi irinsa ba.
Jihar Zamfara ta ba da gudunmawa na matsalolin da muke ciki da kusan kashi 70 domin yadda muke fuskantar lamarin ya sha bamban da nasu, haka ma na Jihar Kaduna.
Hakan ya sa aka bar mu mu kadai gab da zaben 2019.
Kusan duk yawancin shugabannin ’yan bindigar da muka yi yarjejeniya da su a Katsina an kashe su a Zamfara.
An bar su da kananan yara, inda wadansunsu suka ji tsoron ci gaba da hakan.
Kadan da kadan sai dukkansu suka sake komawa ruwa, suka koma daji tare da sake daukar makamai.
A daidai lokacin kuma harkar sata da yin garkuwa da mutane ta fara zama ruwan-dare.
Daga nan lamarin ’yan bindiga ya yi kamari, harkar satar shanu kuma ta hadu da kashe-kashe.
A haka dai muka yi ta lallabawa har zuwa zaben 2019. Bayan zuwan sabon Gwamna sai ya zo da salon son tattaunawa da ’yan bindigar, kuma ya samu goyon bayan ’yan sanda da sojoji.
Wannan shi ne gurbin da muka bi amma saboda rashin samun goyon bayan makwabtan jihohinmu sai lamarin ya lalace.
Mun sake gwada yin haka, inda kusan dukkan gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma da shugabannin sojoji da Shugaban ’Yan Sanda suka zo nan, hatta gwamnonin Filato da Taraba da Neja sun zo don tausaya mana, shi kuma Gwamnan Kogi ya turo da wakilinsa.
Dukkanmu mun cim ma matsayar sake gwada tattaunawa da sulhuntawa da ’yan bindiga.
Mun yi haka ne a karkashin kulawar Shugaban ’Yan sandan Najeriya na lokacin.
Hakan ya sa muka gayyato shugabanninsu zuwa nan Katsina inda muka gana da su har sau biyu.
Daga nan na tashi takanas, na ziyarci wuraren da suka sanya da kansu.
Na kwashe kwana uku ina kewaya wuraren da suka zaba da kansu a cikin kananan hukumomin da suke gaba-gaba wajen fuskantar hare-haren.
Abin da suka bukata shi ne a sako dukkan mutanensu da suke tsare, su ma za su dawo da dukkan shanun da suka sace, za su ajiye makamansu kuma za su taimaka wajen shiga dazuka don aikin tsaro.
Idan mun koma baya kadan, a sulhun farko da muka yi, sun dawo da shanu dubu 36 da jakuna da rakuma.
Sai muka ce tunda an samu nasara a lamarin, bari mu sake gwada su. Sai dai daga baya lamarin bai haifar da da mai ido ba.
Mun yi iya kokarinmu amma a lokacin hakikanin harkar bindiga-dadi ta samu gindin zama yayin da sauran ayyukan ta’addanci suka fara kunno kai.
Don haka, duk yunkurin da muka yi a dunkule ya ci tura. An samu rashin hadin kan gwamonin da wadanan dazukan suka ratsa game da matakin da za a dauka. Wannan shi ne hakikanin gaskiyar abin da ya faru.
Babu ta yadda za a samu nasara a lokacin. Mu gano daruruwan sansanoni a cikin dajin kuma kowane yana cin gashin-kansa ne.
A lokacin burbushin Boko Haram da ISWAP a dajin kawai ya tsaya.
Babu wani a dajin a daidai wannan lokaci da za a tattauna da shi domin dajin ya koma hannun zallar ’yan bindiga ne kawai, domin duk wadanda ba su hada kai da su ba, to sun bar dajin sun koma jihohin Bauchi da Gombe, yayin da wadansu suka gudu zuwa Jamhuriyar Kamaru.
Zuwa yanzu dai kashi 90 na wadanda suke zaune a dajin ’yan bindiga ne kawai.
Ina ganin batun a tattauna da su ya riga ya wuce don haka kada mu yaudari kanmu.
Abin da kawai ya rage mana yanzu shi ne taimaka wa jami’an tsaro.
Wadansu suna ganin tattaunawa da ’yan bindiga tamkar yabawa da ayyukansu ne; tun farko me ya sa ka yi tunanin daukar wannan mataki?
Ina ganin mutane ba su fahimci yadda lamarin yake ba ne a ganawar da muka yi da su a karon farko.
Mun bayyana karara a lokacin cewa duk wanda kotu ta yanke masa hukunci batun afuwa ba zai shafe shi ba.
Na samu ziyartar kurkuku har sau biyu a nan Katsina kuma na tarar yawancinsu da aka kama kuma ake tsare da su a lokacin ba a ma kai su kotu an karanta tuhumar da ake yi musu ba kuma a lokacin babu hukuncin satar shanu a kundin shari’a.
Na samu babban kalubale da na zo ina sabo. Dole a matsayina na shugaba in fara tunanin zakulo mafita a kai domin ya zama dole a kaina.
Wani lokaci akan iya daukar mataki a bisa kuskure, wanda ina ganin ya fi, da a ce ba a dauki mataki ba kwata-kwata.
Na dauki matakin tattaunawa da yin sulhu ne ala tilas domin ina kokarin gano hakikanin abin da yake faruwa ne a dajin.
Me ya sa mutanen da suka zauna lafiya da iyaye da kakanninmu shekaru aru-aru a dare daya kuma a ce sun zama makiyanmu?
Abu ne da yake bukatar karatu a kai, kuma mun gano abubuwa da dama.
Ba na ganin batun wanda zai yi garkuwa da mutum ya samu Naira miliyan 10 ya zama yana da alaka da wanda zai sayar da saniya a kan Naira dubu 100 kawai.
Bari mu dawo kan batunmu. Ni ban taba yin da-na-sani a kan wancan matakin da na dauka ba, domin na dauke shi ne daidai da irin rahotannin da suke kasa a lokacin.
Sai dai kawai zan iya cewa wasu tattaunawar da damammakin da muka ba su ba su dace ba.
Da ya kamata ne mu kama su mu dauki mataki a kansu, amma ba batun gazawa ba ce ko kuma jahiltar lamarin.
Ba mu san gaibu ba, amma hakan ya kamata ya taimaka wa wadansunsu ficewa daga dajin.
Wadansu daga cikinsu sun bar jihar suna zaune lafiya a wasu wuraren a matsayin ’yan kasa nagari.
Wadansunku da suke cewa Fulani an manta da su, idan an manta da kai, kai kadai ne mutumin da ba ya farin ciki?
Shi ke nan duk wani da ba ya jin dadi a Najeriya sai ya dauki makami? Wannan ai bai dace ba.
Tunda aka fara samun man fetur akwai matsalar rashin kulawa da aka rika nuna wa yankuna musamman yankunan karkara. Shugabanni ba su yi abin da ya dace ba, kuma ba za ka zargi mutun daya ba.
Wannan hakkin shugabanni ne su magance matsalar shekara 40 da suka wuce.
Misali muna da tsarin kananan hukumomi wanda ya samar da gibi inda ya nuna hakimi ba ya da wani tasiri.
Kuma su ne mutanen da suke zaune a kauyuka tare da jama’a suna tabbatar da bin doka amma an rage musu daraja.
Daukar nauyin da idan ba ka ikon tabbatar da shi ba ya da wani amfani. Mai unguwa ne amma ba ya da iko. Wadannan ne matsalolin da aka fuskanta.
Niyyar sauya kananan hukumomi manufa ce mai kyau amma hanyar zartar da ita ce ba ta dace ba. Wannan ne ya kawo yanayin da muke ciki a yanzu.
Me ya kawo rashin nasarar kafa Hukumar Kula da Arewa maso Yamma?
Ina tunanin akwai dalilai da yawa da suka kawo hakan, Shugaban Kasa ya ba da goyon baya har ya yi alkawarin biyan kudin da za a kashe.
Har sun fara biyan wani kaso daga cikin kudin da aka kashe lokacin aikin.
Wadansunmu har mun fara murna, amma sai dai ta’addanci da satar shanu sun fi yawa a Katsina da Zamfara da Kaduna da Neja. Idan ka kawo batun sauran jihohin da abin bai shafe su sosai ba, ba za ka samu hadin kai ba.
Idan da mun tsaya ne a iya jihohin da abin ya shafa kila da mun yi nisa. Amma duk da haka an samu nasara.
Batun samar da tsaro hakki ne na bangaren zartarwa, hakan ya sa aka bar wa gwamnonin jihohi, sai dai ba ka ganin akwai bukatar a kara wa jihohi karfi domin su magance wannan matsala?
Ina ganin a yanzu mun zama masu kula da kayyaki ne a maimakon shugabannin tsaro.
Gaskiya ce cewa akwai bukatar a raba karfi ba a hukumar ’yan sanda kadai ba har da sauran bangarori.
Dole ne a yi haka idan har muna son samar da ci gaba. Sai dai kuma ko da za a raba iko kada a yi shi ta yadda zai shafi karfin ikon Gwamnatin Tarayya, saboda ita take da alhakin kare dukkan iyakokin kasar nan.
Akwai wasu bangarori da hakkinta ne amma kuma akwai wadanda za a iya rabawa.
Gwamnatin Tarayya tana iya ci gaba da kula da samar da tsaron kasa amma kuma sai a ba jihohi damar samar da ’yan sandan jiha.
An yi zamanin da ’yan sandan kasa suke aiki tare da ’yan sandan kananan hukumomi.
Akwai hanyoyin tsaro da suke bukatar dubawa. Ba mu muke tallafa wa ’yan sandan a yanzu ba?
Ya kamata ka gane yanayin kafin ka san yadda za ka taimaka.
A nan Katsina a kidayar 2006 akwai mutum miliyan 5.7. A yau, shekara 15 da suka wuce idan muna karuwa da kashi 3 ai za mu kai miliyan 8 ko? Shin yawan ’yan sandan da suke Katsina sun kai 3,000, sun kasa haka?
Ina san ka raba 3,000 da miliyan 8 daidai zai nuna maka yawan ’yan sandan da ya kamata a ce akwai a jihar idan aka yi la’akari da yawan al’ummarmu.
Da muka nemi mutane su taimaka wadansu mutane da suke zaune a gidajensu sai surutai kawai suke yi.
Je ka kauyukanmu ba mu taimaka wa ’yan sanda ba? Ba su da yawa da kayan aiki, wannan shi ne gaskiyar abin da yake faruwa, me ya sa muke tsoron fada?
Za mu iya taimakon ’yan sanda, ta zuwa Majalisan Dokoki ta Kasa mu nemi a kara musu kudaden da ake ba su tare kuma da daukar karin ’yan sanda.
Idan kana son gyaran albashin gwamnoni da ma’aikata a matsayina na Gwamna ba zan yi tsammanin samun albashi daidai da na abokin aikina na Kano ba, ballantana na Jihar Legas saboda hanyoyin samun harajinsu ba daidai yake da nawa ba.
Amma kuma wannan ba zai dauke matsayina na Gwamnan Katsina ba.
Hakan yake ga kansila ko wani shugaban karamar hukuma.
Kana tsammanin in hada kaina da jihar da ke karbar harajin Naira biliyan 450 a matsayin kudin shiga, alhali abin da kawai zan iya samu shi ne Naira biliyan 12 zuwa biliyan 15?
Wasu jihohin ma sun dogara ne da kudin da Gwamnatin Tarayya take ba su.
Katsina ta dogara ne da noma da kiwo abin da kawai muke so shi ne shugabanci.
Ya kamata mutane su gane dole sai an sadaukar da kai kuma mu rika yin abu daidai da samunmu.
Mene ne ra’ayinka a kan kokarin da jihohin Legas da Ribas suke yi na fara karbar Harajin VAT don kauce wa dogaro da Gwamnatin Tarayya?
Daga farko wannan magana tana gaban kotu, don haka ba zan ce komai a kai ba kai-tsaye, sai dai zan ba ka misali, mene ne Legas ba tare da sauran ’yan Najeriya take yi ba? Kasuwancin da take takama da shi ya dogara ne da sauran sassan kasar nan.
Jamhuriyyar Benin tana da tashar ruwa, kasar Togo tana da tashar ruwa amma suna da yawan mutane da za su amfana da ruwan ba tare da mu ba?
Me aka yi aka yi Legas da Fatakwal? Batun maganar VAT yana amfanar mu da su baki daya. Mu ke samar musu da ciniki.
Duk jihar da take tunanin za ta iya tsayawa da kanta ita kadai wasa take. Mu muka mayar da Legas matsayin da take alfahari da shi.
Kwanakin baya ka dauki wasu matakai a kan yaki da ’yan bindiga ta hanyar rufe wasu hanyoyi da kasuwanni, hakan ya yi amfani kuwa?
Wannan dokar ta kwana bakwai ce kuma ta yi amfani amma za mu duba ainihin nasarar da aka samu ne da kyau bayan wata daya.
Ka san mataki ne da zai shafi tattalin arzikinsu sannan zai shafi wasu al’amura nasu.
Daga ciki shi ne zai hana su samun damar mallakar makamai sannan zai hana su damar sayen kayan abinci da kwayoyi. Wannan zai taimaka wajen sanya sauran yaran da suka diba daga kauyuka su fito su dawo gida.
Ina ganin idan muka hada kai abin zai taimaka. Idan ka yi garkuwa da mutum ba za ka iya kiran ’yan uwansa ba, don haka babu maganar kudin fansa ke nan.
Wace hanya ce mafita daga wannan hali da ake ciki?
Ba matsala ba ce da ba za a iya magance ta ba, kamar yadda nake fadi ne, hakan zai yi wuya ne da a ce suna fada ne a kan wata akida ta addini ko neman ’yancin kai.
Amma su ’yan bindiga ne kuma barayi. Idan har muna son kawo karshen matsalar dole Gwamnatin Tarayya da na jihohi da na kananan hukumomi su gudanar da ayyuka a irin wadannan wurare.
Sannan dole mu sani cewa ilimi ne zai kawo karshen wannan matsalar a wuraren.
Ba tare da ilimi ba gaskiya wani bam ne da zai iya fashewa a kowane lokaci.
Dole mu sa dokar ta-baci a kan harkar ilimi kuma mu ba su ilimin addini da na boko wadanda za su ba su damar ba da gudunmawarsu a cikin al’umma.
Wa’adin mulkinka ya kusa karewa, ka fara tunanin wanda zai gaje ka?
Jam’iyyata tana da tsarin fitar da wadanda za su fito takara, daga kansila har Shugaban Kasa.
Bukatarmu a jihar ita ce mu bi tsarin doka. Allah Ya kawo mutumin kirki da zai fito ya yi abin da muka yi.
Amma mafi yawan tsofaffin gwamnoni da na yanzu suna da ra’ayin zabar wanda zai gaje su?
Daga 1999 zuwa yanzu mutun nawa ne aka sa wanda karshe ya yi nasara?
Ni burina in bayar da dama kowa ya fito na bar wa Allah zabi ba a hannun wani ba.
Ba na so in zabi wani yana jirana. Ina son wanda zai gaje ni ya yi abin da ban yi ba.
Burina Katsina ta ci gaba saboda Katsinar ce a gabana, domin Katsina ta dade da kafuwa sannan kuma za ta ci gaba da kafuwa ko bayan jikokinmu.
Don haka, ina da babbar manufa ga jihar.
Kana daya daga cikin wadanda ke son mulki ya koma Kudu a 2023, amma wadansu mutane suna adawa da tsarin karba-karba, me za ka ce kan haka?
Me dimokuradiyya take nufi, gwannatin mutane da yawa.
Kamar mai sayar da dankali ne ya sa manya a sama, kanana a kasa.
Dimokuradiyya ga mutanan da suke tunanin har yanzu tsari ne da ya dogara da mai yawa ya dauka abin ba haka yake ba.
Tsari ne da ya ba duk wani dan kasa damar tsayawa takarar kowace kujera a kasar nan.
Dimokuradiyya ba hauka ba ce. Dama ce ga shugabanni su yi abin da ya dace.
Me ya sa wadansunmu suka ki yarda a canja tsarin mulki saboda a ba Shugaban wancan lokaci damar ci gaba?
Saboda wadansu mutane suna ganin lokacin Arewa ne kuma Obasanjo yana kokarin kashe niyyar haka. Wadannan mutane suke surutai daban-daban.
Ni ina ganin ta koma Kudu, amma wannan bai hana ka fadin ra’ayinka ba.
Bai kuma hana ni a matsayina na Aminu Ballo Masari ba in bayyana ra’ayina ba.
Me za ka ce game da yawon kiwon dabbobi da wadansu suke sukar yin hakan?
Ina cikin siyasa ne don a kalubalance ni, kuma na yarda da ni ba dole ba ne duk abin da zan fada kowa ya amince da shi ba.
Me ya kawo wannan fitina ta manoma da makiyaya da muke fama da ita?
Ba kiwo ba ne, tunda mun gane damuwar me ya sa ba za mu tsai da abin ba?
To Amma kafin mu tsaida ya kamata mu sa tsari a kasa.
Ba zan rufe bakinka ba, ba tare da na bude maka wata hanyar cin abinci ba.
Ni ba na goyon bayan yawon kiwo a ko’ina, to amma ya kamata mu samar da wata mafita.
Ban kuma ce dole ne kowa ya yarda da ni a kan hakan ba, amma kuma ba zai hana ni fadin ra’ayina ba.
Shi ya sa muka gode wa Gwannatin Tarayya da ta ba mu Naira biliyan 6.25.
Za mu saka kudin domin samar da wurin kiwo da gyara dam-dam na ruwa da gina sababbi da kirkirar rugage da wuraren kiwo na zamani da gina hanyoyi da mutanenmu ba za su yi tafiya mai nisa, don neman abincin dabbobi da ruwan sha.
A matsayinmu na mutanen wannan yanki masu addini, yaya Khalifa Umar ya magance matsalar kiwo a fili?
Shi ya sa na ce yin kiwo a ko’ina ba addini ba ne hakki ne da shugabanni za su dauka don magance shi.
Daga: Abdul’aziz Abdul’aziz da Tijjani Ibrahim da Ahmed Ali da Mohammed Yaba