✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da zai hana mu biyan sabon mafi ƙarancin albashi — Inuwa

NLC ta ce tana aiki tuƙuru don ganin gwamnatin jihar ta fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi.

Gwamnatin Jihar Gombe, ta ce tana jiran tsarin yadda albashin ma’aikata zai gudana daga Gwamnatin Tarayya, kafin ta aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin Naira 70,000 a jihar.

Mataimakin Gwamnan jihar, Dakta Manassah Daniel Jatau ne, ya bayyana wannan bayan ganawa da Kwamitin Tripartite domin tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi.

Ya jaddada cewa, jihar ta himmatu wajen tabbatar da cewa ma’aikatan gwamnati sun samu sabon mafi ƙarancin albashin.

A cewarsa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya riga ya fara ɗaukar matakan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin kuma yana taka rawar gani wajen tallafa wa ma’aikatan gwamnati.

Tun daga watan Satumban 2023, jihar ta fara bayar da Naira 10,000 a matsayin tallafi domin rage tasirin cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi, wanda hakan ya sa mafi ƙarancin albashi a jihar ya koma Naira 40,000.

Sai dai kwamitin, ya bayar da shawarar ware albashin daga ƙarin Naira 10,000 har sai an cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashin.

Tun daga watan Agusta, za a fara biyan ma’aikata albashinsu, sannan a biya su tallafin bayan kwana biyu, domin fahimtar ainihin abin da suke samu.

Jihar tana jiran tsarin albashi daga Gwamnatin Tarayya kafin ta fara cikakkiyar tattaunawa kan sabon tsarin mafi ƙarancin albashin.

Shugaban ƙungiyar ƙwadago (NLC) na jihar, Kwamared Yusuf Aish Bello, ya buƙaci ma’aikatan gwamnati su yi haƙuri yayin da suke aiki tuƙuru don ganin an cimma matsaya kan sabon tsarin albashi.