✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da yasa na karba rigar Ronaldo- Harry Kane

Dan wasan Tottenham wanda tauraronsa ke haskawa a yanzu, Harry Kane dan shekara 24, ya ce ya karba rigar Cristiano Ronaldo ne saboda ya dade…

Dan wasan Tottenham wanda tauraronsa ke haskawa a yanzu, Harry Kane dan shekara 24, ya ce ya karba rigar Cristiano Ronaldo ne saboda ya dade yana shaukinsa. Sannan kuma zai adana rigar sosai.

Harry Kane ya bayyana hakan ne bayan wasan da Tottenham ta kara da Realmadrid a ci gaba da gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, inda aka yi kunnen doki.

“Na tambayeshi riga bayan an kammala wasa. Ronaldo dan wasa ne da nake kaunar zama kamarsa tun ina karami. Don haka ina matukar farin cikin samun rigar, kuma zan adana ta sosai.

“Ba za mu taba mantawa da wannan wasar ba. Muna alfahari da wasa ranar, kuma magoya baya Tottenham a duk duniya suna alfahari da mu.

“Nima kuma na ba shi rigata duk da cewa ban san mai zai yi da ita ba,” inji Kane.

Za a sake karawa a zagaye na biyu tsakanin kungiyoyin guda biyu nan da makonni biyu a filin Wembley na Ingila.