’Yan Najeriya sun bayyana bacin ransu kan sabon karin farashin man fetur da gwamnatin kasar ta yi.
’Yan kasar da dama na ganin karin da Gwamnatin Tarayya ta yi bai dace ba musamman a irin wannan yanayi na matsain tattalin arziki da kasar ke ciki
- An tsinci gawar matashi a cikin kwata a Kano
- Duk da sukar takarar Musulmai 2, an ga malaman coci a wurin kaddamar da Mataimakin Tinubu
- Wahalar man fetur da ake fuskanta a yanzu somin tabi ce —Dillalan Mai
Suna kuma caccakar gwamnati ta kowacce fuska da nuna gazawarta musammna a shafukan sada zumunta.
Benson Olayemi na ganin ganin ba a yi wa ’yan Arewa adalci ba a karin man da aka yi, ba duba da irin kokarin da suka yi na ganin sun kafa gwamnatin amma kuma yanzu a sabon jadawalin karin farshin man nasu ne ya fi yawa.
“Wannan rashin adalci ne ga ’yan Arewa kamata ya yi su biya kadan… su ya yakamata su saya a kan farashi mafi kankanta. Suke da mafi yawan masu jefa kuri’a lokacin zabe,” a cewarsa.
A ranar Talata ne gwamnatin ta sanar karin kudin man fetur fiye da Naira 165 a hukumance.
Karin dai an karkashi duba da yanayin kudin da za a kashe wajen dakon man zuwa wurin da za a sayar bayan shigo da shi Najeriya.
Jadawalin kafin farashin da ya fara aiki a ya nuna za a rika sayar da man fetur Naira N184 zuwa N189 a yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin Najeriya — Karin na N24 kuma shi ne mafi yawa.
A yankin Arewa ta tsakiya dkuma za a rika sayarwa N179, yankun Kudanci kuma N165 zuwa N179 ko da yake ana sayarwa N169 a Legas, a Abuja kuma N174.
An kuma kara farashin daga a gidajen mai da ke yankin Legas daga N148.17 zuwa daga N160 zuwa 162.
Manyan rumubuan mai a yankin Warri/Ogbarra sun kara farashinsu zuwa tsakanin N162 da N165 a Fatakwal kuma an kara zuwa tsakanin N165 zuwa N167.
Sai dai kuma tu kafin karin akan sayar da man a wasu gidajen man fiye da hakan, amma ranar Talata ne aka kara farashin hukumance.
‘Karin kudin fetur ya zama dole’
Sai dai wasu ’yan kasar kuma na ganin sabon karin kudin fetur din da na gwamnati ya yi daidai duba da yadda kudin dakon man fetur din ya yi tashin gwauron zabo.
Masu irin wannan ra’ayi na ganin karin kusan wajibi ne duba da abin da wasu masana ke fada tun a baya cewa ya kamata talakawa su yarda a janye tallafin man gaba daya;
Amma aka yi kokarin zanga-zanga wanda ya tilasta gwamnati fasa yunkurin daga farashin man kamar yadda Sheikh Muhammad Abba Ari ya bayyana a yayin da yake tsokaci a kan batun a shafinmu na Facebook.