✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sumar da ni a wurin tantancewa —Ministan da ya maye gurbin El-Rufai

Majalisa ta amince da ministoci uku da Tinubu ya mika mata sunayensu

Ministan Jihar Kaduna, Balaraba Abbas Lawal ya bayyana dalilin da ya yanke jiki ya ya fadi a lokacin da tsaka da tantance shi a Majalisar Dattawa. 

Bayan farfadowarsa daga suman da ya yi, Balarabe wanda ya maye gurbin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shaida wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio cewa, tsananin gajiya ce ta sa ya sume.

Ya shaida wa Akpabio cewa ya shafe kwanaki uku yana aiki babu hutawa kafin ranar tantancewar da hakan ta faru da shi a gaban majalisa.

A ranar Laraba ne sanatoci suka tantance Balarabe tare da Dokta Jamila Ibrahim Bio daga Jihar Kwara da kuma Ayodele Olawande daga Jihar Ondo a matsayin ministoci a gwamantin shugaba Tinubu.

A ranar Talata ne Tinubu ya mika wa Majalisar sunansa a gurbin El-Rufai daga Jihar Kaduna wadda aka ba wa Ma’aikatar Muhalli, kwanaki bayan shugaban kasan ya mika sunan Jamila a matsayin ministar Matasa da kuma Oluwande a matsayin karamin minista a ma’aikatar.

Kimanin mintoci 15 bayan hawansa kan mimbarin domin jawabin gabatar da kansa da kuma amsa tamboyin sanatoci, ne yanke jiki ya fadi a daidai lokacin da Sanatan Kaduna ta Kaduna ta Kudu, Sunday Marshall Katung, yake tsokaci kan kwarewar ministan da irin ayyukan da ya yi a matsayin jimi’in gudarwa a Jihar Kaduna.

Sunday Marshal Katung ya sanar da amincewarsa da kuma ittifakin duk sanatocin Jihar Kaduna da nadin minista Balarabe.

Sai dai bai kai ga rufe baki ba ministan ya yanke jiki ya fadi, nan take Shugaban Majalisar Godswill Akpabio ya bukaci a farfado da shi, inda ya manema labarai su fice daga zauren, aka dakatar da tantancewar.

Daga baya wani sanata ya shaida mana cewa Balaraba ya farfado, kuma an tantance da aikin tantancewar bayan kimanin awa guda, inda bayan dawowar ya bayyana dalilin sumewar tasa.

Bayan an kammala da shi ne aka tantance Oluwande, inda daga karshe sanatocin suka amince da nadin su ukun

Akasarin sanatocin da suka halarci zaman tantancewar ne suka amince da nade-naden, jim kadan bayan tantancewar da ta gudana a ranar Laraba.