✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa Shugaban MTN ya yi murabus

A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaban Kamfanin Sadarwa na MTN Mista Sifiso Dabengwa ya yi murabus sakamakon tarar fiye da naira tiriliyan daya…

A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaban Kamfanin Sadarwa na MTN Mista Sifiso Dabengwa ya yi murabus sakamakon tarar fiye da naira tiriliyan daya da Hukumar Sanya Ido kan Kamfanonin Sadarwa  wato (NCC) ta ci kamfanin.
A wata sanarwa da ya sanya wa hannu, shugaban ya ce ya yi murabus ne “domin kare martabar kamfanin da masu zuba jari a cikinsa”.
Mista Dabengwa ya zama shugaban kamfanin ne a shekarar 2011. Kodayake, yanzu an nada Mista Phuthuma Nhleko a matsayin shugaban-riko na tsawon watanni shida, a yayin da kamfanin zai ci gaba da neman wanda zai maye gurbin Mista Dabengwa.
Hukumar NCC ta ci kamfanin tara ne saboda ya ki amicewa ya rufe layukan mutanen da suka ki yin rijista har wa’adin yin rijistar ya wuce, inda tarar da aka ci kamfanin ta ninka ribar da ya samu a bara.
An bai wa MTN tsawon makonni biyu domin ya biya tarar, wato zuwa ranar Litinin mai zuwa.
Sai dai kamfanin yana ci gaba da tattauna wa da mahukuntan Najeriya kan yadda za a rage masa tarar. Reshen kamfanin na Najeriya shi ne mafi girma, inda yake da wadanda suka mallaki layukansa guda miliyan 28 da dubu 500.