Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Chanchanga a Jihar Neja Alhaji Mohammed Umaru Bago ya ce yana neman kujerar Shugaban Majalisar Wakilai ne domin yankinsa na Arewa ta Tsakiya ya cancanci samun kujerar.
Mohammed Bago ya bayyana haka ne lokacin da ya kawo ziyara ofishin Media Trust a Abuja, inda ya ce tun 1999 da aka dawo mulkin siyasa, yankin Arewa ta Tsakiya bai taba samun shugaba ko mataimakin shugaban majalisar ba, amma duk sauran sun taba samun akalla daya daga cikinsu.
Alhaji Bago wanda yanzu zai koma majalisar a karo na uku ya ce yanzu haka ya yi nisa wajen neman goyon bayan ’yan majalisa, kuma ya ce suna goyon bayansa sosai bisa la’akari da kwarewarsa da kuma tsare-tsaren da yake da su.
Bago wanda ya samu rakiyar Dokta Ibrahim Dooba da ’yan Majalisar Wakilai Bimbo Daramola da Bictor Afam Ogene ya ce, “Mun taimaka matuka wajen tabbatar da nasarar Jam’iyyar APC, amma duk da haka kawai muna kira ne a yi adalci. Tun 1999 ba a taba ba wani dama daga yankin Arewa ta Tsakiya ba a Majalisar Wakilai.
“Kamar misali ne a ce kana da ’ya’ya shida, kuma kana da yankan nama shida, sai ka ce za ka ba wani daga cikinsu yanka biyu shi kadai, hakan zai sa wani ba zai samu ba. Abin da muke cewa shi ne, tunda ana maganar adalci ne da canji, to ya kamata mu nuna wa duniya cewa jam’iyyarmu daban ce. Idan muna so a samu daidaito musamman a wannan lokaci da kasar ke fama da matsalar kabilanci da tabarbarewar tattalin arziki da matsalar tsaro, to ya kamata a yi daidaito wajen raba kujerun nan.
“Yankin Arewa maso Yamma na da Shugaban Kasa, Kudu maso Yamma na da Mataimakin Shugaban Kasa. Sauran yanki hudu ke nan. To kuma jam’iyya ta ce Shugaban Majalisar Dattawa ya fito daga Arewa maso Gabas, Mataimakinsa kuma daga Kudu maso Gabas ko Kudu maso Kudu. Sauran matsayi biyu ke nan ya rage.
“Ke n an zai zama rashin adalci idan ka yi tunanin kara wa yankin Kudu maso Yamma Shugaban Majalisar Wakilai kuma ga shi yankinmu na Arewa ta Tsakiya mun fi su samar wa APC kuri’a, kuma sun taba fitar da Shugaban Majalisar sau biyu da kuma mataimaki sau daya.”
Da aka tambaye shi ko zai yi amfani da ’ya’yan sauran jam’iyyun da suke majalisar wajen cimma burinsa, sai ya ce, “Kuskure ne babba ka ce za ka tafiyar da majalisa ba tare da hannun jam’iyyar adawa ba. Su ma ’yan majalisa ne zababbu, kuma suna da murya. Yanzu haka sun kai 149, kuma suna tsammanin samun kari. Don haka suna da yawa da karfi.”
A karshe ya kara da cewa ya kamata a yi amfani da dokar nan ta sanya matasa cikin harkokin mulki, sannan ya ce idan ya zama shugaban majalisar, zai taimaka wajen tabbatar da cewa Jam’iyyar APC ta cimma burinta na samar da ci gaban ga kasar nan.