✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa nake neman taimakon al’umma – Umar brahim

Wani magidanci mai suna Umar Ibrahim mazaunin Unguwar Hayin Banki da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna ya bayyana cewa ya shiga…

Wani magidanci mai suna Umar Ibrahim mazaunin Unguwar Hayin Banki da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna ya bayyana cewa ya shiga neman taimako ne domin samun kudin jinyar kafarsa saboda abin ya fi karfinsa.

Umar wanda ya yi hadari a babur inda ya samu karaya biyu a kafarsa, da kuma wani a hannunsa tun a shekarar 2015, ya ce har yanzu yana fama da jinyar ce domin bai samu damar yin magani yadda ya dace ba.

“Tun a shekarar 2015 a makon da aka daga zaben shekarar Allah Ya jarabeni da hadari a babur dina da nake aiki da ita. Tun wancan lokaci nake ta fama da jinya. Na je wasu gyaran kafa a garuruwa da dama, amma har yanzu ban samu waraka ba. Na dai dan samu sauki yanzu domin nakan taka kafar, amma an ce min an goya kashin ne kawai kafin a samu kudin da za a min aiki.

“Yadda abin ya faru shi ne na kasance ina achaba da babur dina a Barikin NDA da ke Kaduna, inda nake samu nake ciyar da iyalina da taimakon wasu ’yan uwa. Cikin ikon Allah watarana sai na yi hadari a cikin Barikin, abin kamar wasa aka kira mi gyara a nan Kaduna , ashe gyaran bai yi ba. Muka gama kashe kudade amma abin kullum jiya a yau. Daga baya sai aka ce mana akwai wani mai gyara a Gonin Gora da ke Kaduna, can muka je muka kashe wasu kudaden, amma kafar dai sai a hankali. Daga nan kuma sai muka dunguma muka tafi Sakkwato, inda muka je wajen masu gyara a kauye muka gwada amma sai dai kawai mu ce an samu sauki.

“Daga nan ne muka je Asibitin Kashi na Dala da ke Kano, inda bayan an gwada ni aka dauki hotuna, sai aka bukaci in kawo Naira 451,080.05 domin za a min tiyata da sauransu. Tun nan ne na shiga fadi tashin inda zan samu kudin kasancewar kusan shekara 4 ina fama da jinyar kuma ina zaune babu sana’a, na buga duk nake zaton zan samu, amma abin ya ci tura. Wannan ne ya sa yanke shawarar in nemi taimakon al’umma domin in samu sauki in ci gaba da ayyukan da nake yi domin ciyar da iyalina da rufin asirina.”

Aminiya ta samu ganin takardun asibitin Malam Umar, inda ta tabbatar da kudin da ake bukata daga gare shi, kuma yanzu haka yana zaune ne a gida yana jiran agajin mutane domin ya koma asibiti a masa tiyata.