✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa nake kwana a gefen titi a Abuja – Madam Nancy

Wata mata da ke kwana a bakin titi a Abuja, mai suna Madam Nancy Julie Xanladi ta ce ita ’yar asalin Makun ce da ke…

Wata mata da ke kwana a bakin titi a Abuja, mai suna Madam Nancy Julie Xanladi ta ce ita ’yar asalin Makun ce da ke karkashin masarutar Pankshin da ke jihar. Amma watanni biyu da suka wuce ta dawo Abuja domin domin tana zargin mijinta mai suna Mr. Godfrey ya sami wata mace ya yi watsi da ita da yaransu shida ba ci ba sha.

Ta ce maigidan da suke haya ya tsangwame ta da ta tashi don ana bin su kuxin haya, shi ya sa ta kwashi yaransu ta kai wa hukumar jin daxin jama’a, inda suka kira mijin suka mika masa yaran, inda ya kwashe ya kai wa danginsa. “Ni kuma na kwase kayan xakina da katifa, tukwane da sauran karikiati na bar Jos na nufo birnin Abuja. Amma sai na yi rashin sa’a domin ban yi wa kanwata waya ba, wacce take auren mutumin Berom kuma suna zaune a Titi na Huxu a Unguwar Gwarimpa domin an yi wa mijinta sauyin wurin aiki zuwa garin Jos.

“Haka ya sa na yi zaman dirshan a gaban gidan har na kwanaki arba’in, inda ak tsangwame ni sannan na kwashe kayana na komo zama bakin titi a rumfar jiran mota da ke daura da Firamare ta Jabi dab da ‘Airport Junction” a  Abuja,” a cewarta.

Ta ce wasu jama’a na ba ta kyauta don tausayawa, wanda take sayen abinci da su. Haka kuma ta ce ta na son ta samu xakin haya da keken xinki ko aikatau, ko kuma ta sami jari, domin ta fara yin cin-cin.

Ta kara da cewa tana bukatar Cocin Katolika na Saint Moses Catholic da ke Tudun Wada Jos, wanda Rabaran-Fada Manther ke jagoranta da su kawo mata xauki, domin a cewarta, saboda tana kwana a waje, ta kamu da ciwon sanyi a kafarta.