✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na yi wa PDP wakar Shegiyar Uwa – Aliyu Haruna Ning

Alhaji Aliyu Haruna Abdullahi Ningi shi ne mawakin da ya fi kowane mawaki tallata Jam’iyyar PDP a farkon kafuwarta a 1998 inda ya zamanto da…

Alhaji Aliyu Haruna Abdullahi Ningi shi ne mawakin da ya fi kowane mawaki tallata Jam’iyyar PDP a farkon kafuwarta a 1998 inda ya zamanto da wakokinsa ake zuwa yawon kamfe ko bayar da talla don tallata manufofin jam’iyyar a kafafen watsa labarai cikin harshen Hausa. Sai dai kuma daga baya ya yi mata wata waka da ta zamo tamkar yi mata bakin da ta kasa farfadowa har zuwa faduwarta a zaben bana wato wakar “Shegiyar Uwa Mai Kashe ’Ya’yanta PDP.” Me ya sa ya yi mata wannan waka? Ya bayyana dalilin yi mata wannan waka da sauran batutuwan da suka shafi rayuwarsa:

Mene ne takaitaccen tarihinka?
Cikakken sunana Aliyu Haruna Abdullahi Ningi.An haife ni a kauyen Rumbu da ke karamar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi a 1972. Na yi makarantar firamare a Rumbu da Dagauda. Daga nan na tafi sakandare a Burra, kuma saboda takardata ba ta yi kyau ba, sai na sake komawa sakandaren Dagauda inda na je na sake gyara takarduna a 1992. Daga nan sai na tafi Kwalejin Kimiyya da kere-kere da ke kauran Namoda a Jihar Zamfara a 1994, inda na yi diploma a kan nazarin kudi, na kammala a 1996. A 1997 ne na fara wakar siyasa lokacin mulkin marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha.
Me ya ba ka sha’awar shiga wakar siyasa bayan a makaranta ka karanta harkokin kudi ne?
A lokacin an kafa jam’iyyun UNCP da DPN, to muna da dan takarar da muke goyon bayansa wato Alhaji danlami Garba Bara’u da yake DPN da kuma Alhaji Abdu Sule shi kuma yana UNCP. To a lokacin da aka yi wancan zabe, saboda UNCP kamar jam’iyyar gwamnati ce, sai aka yi mana karfa-karfa. Wannan abu ya sa ba mu ji dadi ba, amma ba mu da karfin da za mu iya sayen shafukan jarida ko lokaci a gidajen rediyo don mu bayyana damuwarmu, to shi ne sai na ce ya kamata mu bayyana kokenmu a cikin waka tunda ita ba wata aba ce mai tsada ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa na zauna na fara rubuta waka. Wakata ta farko ita ce:  “Mu fada mu fallasa ’yan hana Ningi ci gaba.”
To daga nan sai aka yi ina?
Daga nan sai muka tsunduma a harkar siyasa, kafin Abacha ya rasu akwai manyan mutane da na yi wa waka, kamar su marigayi Alhaji Abubakar Rimi da Alhaji Sule Lamido da Alhaji Isa Yahaya Zarewa da Alhaji Kabir dambatta duk na fara hulda da su a lokaci. To bayan Janar Abacha ya rasu, sai wadannan mutane iyayen gidana da aka kakkama su, sai aka ce za a fito da jam’iyya. To kafin a fito da jam’iyyar sai na zauna na yi nazari cewa tunda wadannan iyayen gida nawa ’yan siyasa ne duk jam’iyyar da za su fito ni ma a cikn zan fito. Sai na fara nazari na tsara wa Jam’iyyar PDP wakoki nau’o’i uku. Lokacin da aka zo kaddamar da Jam’iyyar PDP a Ningi da Wazirin Bauchi Alhaji Bello Kirfi da su tsohon Gwamna Ahmadu Mu’azu da sauran shugabannin PDP suka hallara a nan ne na fara rera wakar siyasa a gaban jama’a. Da suka ji ta yi, sai suka ce suna bukatar in buga ta, lokacin marigayi Shettiman Katagum (Alhaji Bashir Mustapha), Baraden Bauchi (Alhaji Umaru dahiru) lokacin yana Sakataren Jam’iyyar shi ya ba ni sunayen shugabannin jam’iyyar ya ce in kai masa kaset din. To daga nan aka fara baza wakar.
A cikin wakokin wacce ce kake ji ta fi karbuwa a lokacin?
A lokacin duk sun karbu wato da mai cewa:
“PDP muke so ku zo,
Ga jam’iyya.
Ku sa ta a zuciya al’ummar Najeriya.”
Da mai cewa:
“PDP jam’iyyata, abar so a zukata,
Mutanen Najeriya ku taso mu rike ta.”
To da su aka yi ta amfani a kasar Hausa wajen yada Jam’iyyar PDP.
Ko ka ci gajiyar wadannan wakoki?
A gaskiya ban ci gajiyar wakokin ba, sai bayan shekara biyu da buga wakokin. Domin na buga wakokin a 1998, a 1999 aka yi kamfe aka kafa gwamnati, to amma ban fara cin gajiyar wakokin ba sai a shekarar 2001, inda tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya ba ni mota kirar fijo sabuwa.
Daga baya sai aka ji ka yi mata wakar “Shegiyar Uwa mai kashe ’ya’yanta PDP…” Shin a lokacin ka fice daga cikin jam’iyyar ko wani abin takaici aka yi maka?
Har ga Allah a lokacin ban fita daga Jam’iyyar PDP ba, abin da ke mu da muka tallata ta, sai muka ga manufofinta da aka ba mu mu tallata ta an kauce musu. Da muka ga an kauce daga kansu sai muka ga ya kamata mu sanar da shugabannin jam’iyyar don su fahimci kura-kuran da suke yi don su gyara.
Kamar wadanne abubuwa ne kake ganin suka jawo ka yi wakar ta Shegiyar Uwa?
To abubuwan da suka faru, su ne duk jiga-jigan da suka taru suka kafa Jam’iyyar PDP ana bin su ana korarsu daga jam’iyyar da karfi da yaji. Kuma a lokacin babu ruwan PDP da zabe, duk abin da aka ga dama shi za a yi ba yadda tsarin jam’iyya ya tanada ba. Wannan shi ne abin da ya sosa min rai na yi wannan waka ta Shegiyar Uwa. Mutanen da suka kafa jam’iyyar suka yi wahalar kafa ta su ake korewa daga jam’iyyar. To ni a matsayina na dillalin da ya yi tallar ta, bai kamata in zuba ido abubuwan suna tafiya haka ba, dole in yi wani abu da zai kare jam’iyyar. Ba wanda ya sanya ni na yi wakar, a cikin jiga-jigan PDP akwai ma wanda ya yi kokarin kada in saki wakar ta Shegiyar Uwa.
Kana ganin wannan wakar ta kawo gyarar da kake magana?
Ba ta kawo gyarar da ake bukata ba, ku, a rashin wannan gyara ne ya jawo sanadiyyar da jam’iyyar ta ruguje gaba daya a yanzu. Lokacin da aka yi wadannan abubuwa shi kansa Atiku lokacin da ya dawo PDP ya kira ni, cewa in zo in nazarin wakar da za a gyara PDP. Na ce ranka ya dade ko na tsara wakar ba za ta yi wani tasiri ba, domin wadancan abubuwan da muke magana a kai gaskiya ne, kuma har yanzu ba a daina yin su a PDP ba. Kuma in ba a daina yin su ba, babu ta yadda za mu gyara. Ya ce gaskiya ne. muka yi ta kokari, gyara bai yiwu ba, daga baya shi ma ya ga cewa tabbas abin ba zai gyaru ba. Lokacin da ya sake fita ta biyu ne na yi wata waka mai cewa:
 “Jam’iyyata ciwon ajali ya kama ta,
Wane ne ya dunkufa sai ya karya ki.”
Ka ce ba ka fita daga jam’iyyar ba, shin ko ta kira ka domin kawo gyara?
Ba ta kira nib a, kai abin ma bata mata rai ya yi, suna ganin kamar cewa na hassala mutane ne su guji jam’iyyar. Maimakon su kira ni mu zauna sai suka rika kyamata ta. Kuma hakan bai san a bar jam’iyyar ba, sai da lokacin da na ga cewa tabbas lokacin mutuwarta ya zo, shi ne na yi mata wakar ciwon ajali ya kamata, sai na fita daga cikinta.
Ko ka yi nadamar yin wakar Shegiyar Uwa?
Ban yi nadama ba, domin na yi wakar ce domin a yi gyara, kuma a kokarin mayar da martani ga wakar an yi waka daidai har 11 don a goge sakon da wakata ke dauke da shi, amma duk ba a samu nasara ba, domin babu guda daya da ta doshi karbuwar tawa. Saboda kullyum gaskiya ita ke sama, kuma ban yi nadama ba.
Yanzu kana cikin wace jam’iyya ke nan?
Ina cikin Jam’iyyar APC tare da su Atiku.
Ga shi APC ta hau mulki amma ba mu ji wakarka ga jam’iyyar ba, ko ba ta yadu ba ne?
Ban yi wa Jam’iyyar APC waka ba, saboda lokacin da muka shigo akwai mawakanta. Amma na yi wakoki ga ’yan takarar jam’iyyar kuma sun yi tasiri, musamman lokacin da aka dage zabe, mun yi fitattun wakoki na jan hankalin jama’a da kara musu kwarin gwiwa cewa cewa su fito su jajirce su tsaya su zabi abin da suke so ko da za a dage zaben sau nawa. Akwai wakar da na yi mai cewa “Ko an dage zabe sai dubu.” Akwai “Ku zabi Buhari/Osinbanjo.”Akwai “Mun yasar da kwallon mangoro.” Da ta “PDP jam’iyya ce ta azzalumai.” Wadannan suna cikin wakokin da muka yi na fadakar da jama’a don su fahimci cewa canji dole saboda a baya an yi an yi a gyara abin ya ki gyaruwa.
Baya ga wakokin siyasa ko kana yin wasu wakoki?
kwarai kuwa nakan yi wakoki kamar na ilimantarwa, misali Hukumar Fadakar da Jama’a ta kasa (NOA) ta bukaci in yi waka a kan yaki da jahilci. Na yi waka a kan maleriya da kanjamau, wadanda suka shafi kiwon lafiya. Na yi waka a kan shari’a. To duk wadannan wakoki ne na fadakarwa. Har wakokin sarauta ina yi, kamar Sarkin Gandun Zazzau na yi masa waka, na yi wa Uban Dawakin Bauchi da Galadiman Yamaltu da Sarkin Dambam da sauransu. Kuma na yi wakoki na jarumta kamar wadda na yi wa fitaccen mai kama barayin nan Alhaji Ali kwara da tsohon Sufeto Janar na ’Yan sanda Hafizu Ringim.
Ko kana rike da wani mukami a kungiyar mawakan Hausa?
Akwai kungiyo na mawaka, amma kungiyarmu ta mawaka ta Jihar Bauchi ni ne shugaba. Amma ba ita kadai ce kungiyar mawaka ba, amma tamu ita ce ta mawaka zallarsu. Amma akwai wata wadda ta kunshi mawaka da ’yan wasan kwaikwayo.
Yaya harkokin kungiyar taku ke tafiya?
To har ga Allah akwai kalubale na kyautata kungiyar, domin sai mun kyautata kungiyar an tace ta ta yadda za a tantance mawaka. Domin za ka ji wakoki masu ma’ama damarasa ma’ana. Kowa ya taso sai ya ce zai yi waka shi ma mawaki ne. To muna so mu gyara kungiyar don mu rika tsabtace wakokinmu, bayan mun tsabtace ta sai mu inganta ta. Domin bai kamata mu bar ta kara zube ba ma cin gajiyarta ba.
Wace shawara za ka ba ’yan siyasa?
Shawarar da zan ba ’yan siyasa ita ce, akwai abubuwa uku da ya kamata su yi la’akari da su. Duk yadda ka kai a siyasa akwai ranar da ba kai ba ne. Na biyu duk inda ka kai da mulki ka sani akwai wani mulki a saman naka. Na uku duk yadda ka kai a girma ka tabbatar cewa na kasan kasa ya taimaka. Don haka kai ma ka rika tunawa ya taimaka maka. Wannan zai sa ’yan siyasa su rika tuna baya, suna yin adalci. Domin rashin adalci ke kawo rushewar mulki. Ga jama’ar kasa kuma su zamo masu hakuri da fatar alheri, su guji  mummunan zato ga masu mulki, su rika yi musu addu’a, sai a ga  Allah Ya juya hankalin shugaba yana yin abin da ya dace. Amma kada bambancin ra’ayi ya sa komai kyan abin da shugaba ya yi su ji cewa ba mai kyau ba ne saboda adawar siyasa.