Shugaban Kungiyar Nakasassu ta Kasa reshen Jihar Yobe, Kwamared Abba Muhammad Isa, ya share wa wata mai larurar nakasa ’yar shekara 18, mai suna A’isha Abubakar hawaye.
A’isha Abubakar, wadda iyayenta marasa karfi ne da take da nakasar gurguntaka da har ba ta iya zuwa makaranta ko ziyarar ’yan uwa saboda ba ta da keken guragu.
Da yake zantawa da Aminiya, Kwamared Abba Muhammad Isa, ya ce a matsayinsa na Shugaban Kungiyar Nakasassu, tausayin A’isha ne ya kama shi lokacin da yake hanyarsa ta zuwa hutun karshen mako daga Damaturu zuwa Maiduguri ya gan ta.
Ya ce shi ma mai nakasa ce da yake da keken guragu; kuma shi ne shugaban kungiyarsu a shiyyar Arewa maso Gabas, kuma saboda sanin muhimmancin keken ne ya sa ya taimaka mata.
Kwamared Abba, ya ce kafin ya ba A’isha keken, ba ta zuwa makarantar Islamiyya da take zuwa a baya, saboda lalacewar keken da take da shi, kuma iyayenta sun gagara gyara mata saboda rashin karfinsu.
A cewarsa da ya tambayi mahaifin A’isha Malam Abubakar, ko a kauyen Jakana akwai masu irin wannan nakasa don a taimaka musu sai ya ce akwai za su kai 10, wanda hakan ya sa ya yi kira ga shugabannin kungiyar nakasassu ta Jihar Yobe su rika bai wa nakasassu da suke kauyuka kula fiye da wadanda suke birane.
Ya ce Naira dubu 15 ya sayi keken, kuma ya hada ta da Shugaban Kungiyar Nakasassu ta Jihar Borno saboda Jakana Jihar Borno ce: don ya rika sa A’isha a duk wani taimako da za a bai wa wani mai nakasa.
Sa’annan ya kira sababbin gwamnonin jihohin Borno da Yobe, Babagana Umara da Mai Mala Buni su mayar da hankali kan taimaka wa nakasassu don jan su a jiki.