✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na mayar da hankali kan wakokin al’ada – Fati Nijar

Idan za a yi duba na sosai a duniyar mawakan Hausa da suka shahara a wannan zamani, za a ga cewar tana da fadin gaske,…

Idan za a yi duba na sosai a duniyar mawakan Hausa da suka shahara a wannan zamani, za a ga cewar tana da fadin gaske, saboda dimbin mawakan da suke cikinta masu tarin basira. Don haka yin nazari a cikinsu wani aiki ne mai yawan gaske, duk da yawansu idan aka ambaci fitacciyar mawakiya Binta Labaran wadda aka fi sani da Fati Nijar mutane za su so su ji wani abu da ke tattare da ita.

Fati Nijar, daya daga cikin mawaka ne da duniyar mawaka take ji da su a fagen wakokin Hausa, domin kuwa a yanzu idan za a yi rubutu a kan mawakan Hausa, idan har ba a saka Fati Nijar ba, to za a iya cewa rubutun bai cika ba, domin kuwa ta kai matsayin da za a saka ta a sahun gaba. Mawakiya ce ta nunawa a gaban sarki ko wani muhimmin bako da ake ji da shi.

Idan ka kira Fati Nijar da mawakiyar Afirka to yanayi da matsayinta a fagen waka ya kai ga haka, don kuwa ita kadai ce a cikin mawakan Hausa take da matsayin shiga dukkan waje na alfarma domin ta yi waka  ba wai a Najeriya ko Nijar ba, Fati ta zagaya kasashen Afirka da wakokinta.

A cikin wata gajeriyar tattaunawa da Aminiya ta yi da mawakiyar, ta bayyana sirrin shahararta da kuma dalilin da ya sa ta fi mayar da hankalinta ga wakokin al’ada.

Ta ce, “Gaskiya ana gayyata ta wuraren taruka da dama, domin na gabatar da waka.  Kuma ina gode wa Allah da Ya ba ni wannan damar. Don wani wurin ma idan na gan ni sai na san kawai dai lamari ne na Allah ba don na fi wasu ba. 

Ta ce, “Don kuwa na kasance mace mawakiya da aka gayyace ni zuwa je fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda na yi waka a lokacin auren ’yarsa Zahra. A wajen ni kadai na yi waka, ga ni ga matarsa A’isha Buhari da danginta, ga matan gwamnoni da ministoci. To ka ga wannan daukaka ce daga Allah.”

Ta ci gaba da cewa, “Sannan na shiga barikin Sojoji na Jaji da ke Kaduna a tsakiyar sojoji na yi waka a lokacin da za a yi wa wani babban soja karin girma da aka gayyace ni na je na yi waka a wajen, sannan na shiga gidajen sarakuna da dama don yin waka, na shiga gidajen gwamnoni da manyan ’yan kasuwa. Don ko a ’yan kwanakin nan akwai wani nadin sarauta da aka yi a Dutse, inda aka nada Nasiru Dano a matsayin dan Amanar Dutse. Shi ma na je na yi waka, kuma daga nan aka yi bikinsa a Abuja na je can ma na yi waka.”

Ta ce, ba wai a Najeriya kawai ba, a yanzu haka tana zuwa garuruwa da dama a cikin kasarta Nijar,  inda sarakuna da masu kudi suke gayyatar ta don ta gabatar da waka, kuma har ma gidan shugaban kasa ma can ta je ta yi waka.

 “Kuma na je wasu kasashe na Afirka kamar Ghana da Kamaru da Kwatano duk na yi waka. A yanzu ma ina da gayyatar da aka yi mini a kasashen Sudan da Gabon da kuma Burkina Faso, wadanda nan gaba kadan zan fara yin zagayen kasashen Afirka don gudanar da wakokina. Kuma ina fata nan gaba na shiga har kasashen Turai.” Inji ta.

Wannan kudiri na Fati Nijar za a iya cewa ya mayar da ita mawakiyar Afirka, domin kuwa ita shahararta ta wuce Najeriya da Nijar, ta hade Afirka gaba daya.

Amma haka ba zai ba da mamaki ba, musamman idan aka duba yanayi da kuma salon wakarta, domin kuwa duk da irin yadda ta kware a kowacce irin waka, amma wakokinta da suka fi tasiri su ne wakokin da ta yi a kan al’ada, kuma duk yanayin shigarta a a cikin wakar ta bidiyo, ta yi shiga ce da take nuna ita ’yar Afirka ce mai kishin al’adun Afirka.

Ko me ya sa Fati take da ra’ayin yin shiga da kuma wakoki na al’ada? Sai ta ce, “Gaskiya ne, ina son yin shiga ta al’ada, shi ya sa za ka ga yanayin suturar da nake sakawa kaya ne na gargajiya, kamar na  Fulani da Hausawa, kuma ko a wakokin ma ina son na yin ta al’ada,  kawai saboda son na raya al’adunmu na Afirka.”

Ta ce, “Domin ko a Turai ma ai al’adunsu suke rayawa to ni ma zan raya al’adunmu don su suna ba ni sha’awa kuma su kansu  masoyana ina burge su da hakan. Kuma Alhamdulillahi, na samu nasarori da dama. Babbar nasarar da na samu ita ce arzikin jama’a da dama da Allah Ya ba ni.”

Ta ce kuma ta samu lambobin yabo da wadansu jami’o’i da kwalejoji da kuma sauran kungiyoyi suka karrama ta da su, don ko “a ’yan kwanakin nan kungiyar furodusoshi ta Arewa reshen Jihar Zamfara ta nada ni a matsayin Gimbiyar Arewa, sannan kuma akwai wani kamfani a Kaduna mai suna kueens World, shi ma ya karrama ni, kuma kada ka manta ni Gimbiyar Mawakan Masarautar Borgu ce, domin kuwa Sarkin Borgu Alhaji Muhammad Halliru dantoro da kansa ya nada ni Sarautar Gimbiyar Mawakan Masarautar Borgu.”