✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Abin da ya sa na kai tsohon mijina kotu kan tura ’ya’yana almajiranci’

Malama Jamila Abubakar da ke zaune a Unguwar Rido a Jihar Kaduna ita ce matar da ta kai tsohon mijinta Isah Aliyu kara a gaban…

Malama Jamila Abubakar da ke zaune a Unguwar Rido a Jihar Kaduna ita ce matar da ta kai tsohon mijinta Isah Aliyu kara a gaban kotun Shari’ar Musulunci domin a karbo mata ’ya’yanta biyu da ya kai su almajiranci. Ta ce so take ’ya’yan su dawo gida su ci gaba da karatun firamare tare da Islamiyya da suka fara. Kotun ta amince da kararta inda a yanzu haka aka mika mata ’ya’yan kuma tuni suka ci gaba da karatunsu. Ta bayyana wa Aminiya cewa mata na da rawa da za su iya takawa wajen rage yawon almajiranci a Arewacin kasar nan.

 

Me ya sa kika kai tsohon mijinki kotu?

Abin da ya sa na kai tsohon mijina kotu shi ne saboda kai ’ya’yana biyu da ya yi zuwa almajiranci. Na yi haka ne saboda in kare mutunci da rayuwar ’ya’yana domin su samu ilimin boko da na addini a gida. Ina matukar kaunar in ga ’ya’yana sun yi ilimi.

Me ya ba ki sha’awa a kan ilimi?

Ilimi ai haske ne, kuma hanya ce ta samun ingantacciyar rayuwa ga dan Adam. Kuma shi ne babban abin da za ka iya ba ’ya’yanka su samu rayuwa ingantacciya a nan duniya da Lahira.

Shin ko kin yi karatu?

Karatun firamare kawai na yi amma na yi imani cewa ilmi na da kyau kuma abin sha’awa ne. Ina fata insha Allahu wata rana zan ci gaba da karatuna.

Me za ki ce game da ilimin zamani ko boko?

Ilimin boko, ilimi ne na zamani kuma wani makami ne da ke da amfani ga dan Adam wanda zai iya amfani da shi wajen cudanya da sauran al’umma idan ba ka da wannan ilimi rayuwa takan dan yi wa mutum wuya.

To me za ki ce game da almajiranci?

Almajiranci tsohon hanyar neman ilimi ne na addini wanda a yanzu ya zama wani abu na daban. Kum a ganina ba hanya ce da ta dace yaro ya bi wajen neman ilimin Kur’ani ba. Yanzu kusan duk yaran da ke zuwa almajiranci yawo kurum suke yi cikin gari ba tare da sun samu wani ilimin Kur’ani ko sun koyi wata sana’a ba. Ina ganin ya fi dacewa yaro ya koyi karatun addini ko na zamani a gaban iyayensa. Wato ya rika zuwa yana dawowa gida. Don haka a ganina ya fi kyau yaro ya rika zuwa makaranta a gaban iyayensa.

Wace rawa kike ganin iyaye mata za su iya takawa domin magance tura yara almajiranci?

Ina ganin iyaye mata na da gagarumar gudunmawa da za su iya badawa wajen canja ra’ayin mazansu a kan almajiranci. Mata su rika yin addu’a sannan su tashi tsaye domin ni tsohon mijina bai fahimci muhimancin ilimi ba, amma wadansu maza ko iyaye kila sun sani. Saboda haka canjin na iya farawa ne daga gida cikin lumana da tattaunawa ba tare da rigima ba.

Mace na iya canja tunanin mijinta a kan tura yaro almajiranci kuma ba dole sai sun je kotu ba amma idan ya kama a yi hakan shi ke nan. Akwai bukatar mata su bi duk hanyayoyin da suka kamata wadanda ba su saba al’adu da addininmu ba domin canja ra’ayin mazansu daga tura yara almajiranci tare da nuna musu hadarin yin haka. A kuma nuna musu amfanun ilimin zamani ga yara.

Ka san muna da al’adu da suka hana ma’aurata yin rigima da junansu. Ni kuma ba cewa nake neman karatun Kur’ani ba ya da amfani ba, amma ni ina ganin akwai hanyoyin zamani na yin karatun ko neman ilimin addini wanda za a iya yi a gaban iyaye. Akwai hakki da ya rataya a kan mata na su taimaka wa ’ya’yansu wajen wayar wa jama’a kai a kan batun almajiranci.

Mata za su iya farawa da tattaunawa a matakin iyali kafin su fita zuwa titi ko cikin al’umma. Wannan matsala da cin zarafin ’ya’yanmu za ta iya raguwa idan matan aure da zawarawa suka fahimci hanyoyin da suka dace na tsabtace al’ummarmu. Muna da babban rawa da za mu iya takawa wajen rage matsalar almajiranci a yankin Arewa.

Menene burinki ga rayuwar ’ya’yanki?

Burina ga ’ya’yana shi ne su samu rayuwa mai inganci nan gaba su samu aiki mai kyau kuma su kasance ’yan kasa nagari. Ina da burin ganin sun zama likitoci ko injiniya ko soja ko dan sanda ko kuma su samu wani aiki da zai sa su zama abin sha’awa cikin kasa.

Yanzu da kotu ta mayar miki da ’ya’yan wane taimako kike bukata domin ilimantar da su?

Na gode da Allah Ya taimake ni kotu ta karbo min ’ya’yana zan kuma ci gaba da neman kariya da taimakon Allah. Ina ci gaba da neman aiki domin in taimaki kaina. Ina rokon masu hannu da shuni ko wata kungiya ko gwamnati ta taimaka min in samu wani aiki da zan yi domin ilimantar da ’ya’yana.

Naira dubu shida da kotu ta umarci tsohon mijinki ya rika ba ki zai ishe ki kula da ’ya’yan?

Wannan kudi ba zai isa in rika ciyar ’ya’ya uku ba a duk wata, amma ba ni da zabi a yanzu. Ina neman taimako wajen gwamnati da masu hannu da shuni a kasar nan su kawo min dauki domin taimaka min tare da yaran nan. Na san tsohon mijina yana da wuyar sha’ani. Kwanaki na aika masa cewa karamin yarona ba ya da lafiya don haka ya aiko da kudi domin a saya masa magani amma bai aiko da ko sisi ba.

Kuma bai zo ya duba jikin yaron ba, shi ya sa na ce kudin wata-wata din ma da wuya ya rika aikowa a kan lokaci duk kuwa da an ce masa zai rika kaiwa ne duk ranar 28 na kowane wata a kotu. Nabar wa Allah komai.

 Kina da wata sana’a da za ki rika yi da za ta taimaka miki wajen kula da ’ya’yanki?

A’a ba na komai a yanzu amma zan ci gaba da nema domin in rika taimaka wa ’ya’yana. Bayan haka kuma idan har na samu aiki zan daure in ci gaba da karatuna a sakandare insha Allahu.

Ina mafita a yanzu tunda ba ki komai kuma ga shi kina zaune ne da mahafiyarki?

Zan nema daga wajen Allah Wanda shi ke bayarwa sannan zan nema wajen ’yan uwa da sauran jama’ar Allah masu tausayi a cikin al’umma domin su taimaka min.