✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na ja baya daga yawon kama ’yan fashi – Ali kwara

Fitaccen mai farautar ’yan fashin nan Alhaji Ali kwara, ya ce kai farmaki a wuraren fashi da makami daga jiha zuwa jiha da a baya…

Fitaccen mai farautar ’yan fashin nan Alhaji Ali kwara, ya ce kai farmaki a wuraren fashi da makami daga jiha zuwa jiha da a baya tawagarsa ta yi suna a kai, na fuskantar tsaiko a yanzu, sakamakon yawaitar shingayen jami’an tsaro a kan manyan titunan kasar nan da tabarbarewar tsaro ta jawo.
Alhaji Ali kwara ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wasu mutum biyu ga manema labarai da ake zargi sayar da motocin sata a Abuja.
Ali kwara ya ce zama cikin damara a kowane lokaci da jami’an tsaron da ke kula da shingayen ke yi tare da dari-dari da kowace mota mai yanayin tsaro da ke bi ta inda shingayen suke, ya tilasta wa jami’ansa da suka kunshi ’yan sanda da farin kaya yin dari-dari da kai dauki a jihohin da ake nemansu, domin gudun kada su jefa rayuwarsu cikin hadari.
A ranar Talata ce Ali kwara ya gabatar da wadanda ake zargin a Abuja bayan da jami’an yaki da fashi da makami na ofishin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriaya da hadin gwiwar rundunar ta Abuja da yake jagora ta kama su.
Ya gabatar da motoci uku da aka samu mutane da su bayan an kwace su a Abuja da suka hada da Nissan Sunny mai lamba BWR380 HH mai dauke da sunan Yakubu Titus a takardunta da Honda Saloon mai lamba GWA 969 RZ mai dauke da sunan Janet Olawuwa Oyobe a takardunta, sai kuma wata Toyota Diana mai lamba dT 763 SMK tare da takardunta dauke da sunan Abdurrazak Ibrahim da aka sato daga Ibadan a Jihar Oyo.
Ya ce an kama mutanen ne a lokacin da suke kokarin sayar da biyu daga cikin motocin a kan Naira dubu 100 da Naira dubu  80 bayan sun samu bayanai a kansu.
daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Hassan Bukar wanda ya ce shi dan garin Gulak ne da ke Jihar Adamawa, ya ce ya zama dillalin ’yan fashi ne bayan da ya rasa sana’arsa ta tuki da ta aikin yuniyon da yake kula da matansa biyu da ’ya’ya takwas.
Mutum na biyu da ake zargi, Ibrahim Akawu ya ce ya shiga harkar ce bayan da ya rasa aiki a Kotun da’ar Ma’aikata inda ya ce yake aiki a shekarar 2006, saboda rage yawan ma’aikata.
Ali kwara ya ce yawanci ’yan fashi da makami sun sauya daga dadaddiyar hanyar fashi da aka sansu da ita a baya. Ya ce kuma da dama daga cikinsu sun kaura zuwa kasashe makwabta da kuma sun koma satar shanu, wasu sun zamo mayakan kabilu da sauran tashe-tashe hankula da kasar nan ke fama da su a yanzu.
Ya ce kashi 80 a cikin 100 na ’yan fashin da ya kama ya mika ga’yan sanda sun kwaci kansu daga kotu inda suke bayyana masa cewa sun tuba daga harkar. Ya ce a yayin da wasu daga cikinsu gaskiya suke fadi, wasu kuma na fada ne don tsoronsa. Game da ko me ya sa ya gaza kai dauki ga matsalar hare-haren kauyukan Jihar Zamfara, ya ce al’amarin Jihar Zamfara matsala ce ta hare-haren ramuwar gayya a tsakanin manoma da Fulani makiyaya, kuma bai son tsunduma kansa a ciki gudun kada a zarge shi da goyon bayan daya daga cikin bangarorin biyu.