Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato ya ce salon mulkin Shugaba Muhammadu Buhari da mutanen da ke kewaye da shi ne suka sa ya dawo daga rakiyar Shugaban Kasar a 2017.
A wata hira da ya yi da Malam Kabiru Yusuf, Shugaban Hukumar Daraktocin kamfanin Media Trust – kamfanin da ya mallaki kafofin yada labarai na Daily Trust da Aminiya da Trust TV – Gwamna Tambuwal ya kuma ce tun farkon hawan Buhari aka fara saka da mugun zare.
- An Yi Wa Ministar Buhari Ihun ‘Ba Ma So’ A Abuja
- Hada-Hadar Kwayoyi: Hantar Manyan ’Yan Sanda Ta Fara Kadawa Kan Binciken Abba Kyari
“Na tari aradu da ka na yanke shawarar sauya sheka zuwa PDP ne saboda tun 2017/2018 na yanke kauna da yadda Shugaba Buhari yake tafiyar da al’amuran Najeriya”, inji Gwamna Tambuwal.
Gwamnan ya ce a lokacin ya bayyana matsayinsa a kan haka ga al’ummar Jihar Sakkwato, kuma a kan hakan ya yi yakin neman zabe.
Idan ba a manta ba, gabanin zabukan 2019 ne dai Gwamnan na Jihar Sakkwato kuma tsohon Shugaban Majalisar Wakilai ya tsallaka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP, inda har ya nemi yin takarar shugaban kasa, amma Atiku Abubakar ya kayar da shi da wasu a zaben fitar da gwani.
Saka da mugun zare
Gwamna Tambuwal ya kara da cewa yanayin hadakar da ta kai Shugaba Buhari kujerar Shugaban Kasa, wanda ya haifar da rikita-rikita, musamman a tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa, ya kawo wa Gwamnatin APC cikas.
Ya kuma ce jinkirin da Shugaban Kasar ya yi wajen nada ministoci ya taimaka wajen nakasa shugabancin Buhari.
“Ya hau [kujerar Shugaban Kasa] da kyakkyawan fata da sauransu, ga dimbin goyon baya, amma wannan jinkirin bai yi rana ba.
“Tunanin [al’umma] shi ne zai nada wata majalisar ministoci ta gani ta fada, amma daga karshe da aka fitar da sunayensu, sai mutane suka rika tambayar dalilin jinkirin”, inji Tambuwal.
Har ila yau, game da mutanen da ke kewaye da Buhari, Tabuwal ya ce bai ma kamata Shugaban Kasar ya hada hanya da su ba.
“Me Shugaba Buhari yake yi da wasu mutane a APC? Yaya ma aka yi har suka hada hanya?
“Ba zan fadi sunan kowa ba, amma suna nan [tare da shi]; wasu daga cikinsu ma a Majalisar Ministocinsa alhali shi (Buhari) ya san cewa babu abin da ya hada su ban da kasancewarsu mutane”.
Tsohon Shugaban Majalisar dai ya furta wadannan kalamai ne lokacin da yake amsa tambaya a kan dalilan da suka sa ya yi ta sauya sheka har kusan sau shida.
Ba kare bin damo
A cewarsa, galibi yana tsallakawa daga inda yake ne saboda ya yi amanna zai iya cin zabe a kowacce jam’iyya.
“Yanayi ne yake sawa [na sauya sheka] saboda amannar da na yi cewa zan iya cin zabe a karkashin kowacce tuta.
“Kuma cikin yardar Allah Madaukaki, sannan tare da godiya ga mutanen mazabata da na Jihar Sakkwato, sau biyar a jere ina cin zabe: 2003 da 2007 da 2011 da 2015 da 2019.
“[Ina sauya sheka ne] saboda amannar da na yi cewa zan iya cin zabe, kuma saboda yanayin da ya sa ake kin ba ni takara a jam’iyyata, ko kuma yanayin da ya sa muka samu sabani, kamar a 2015, da PDP.
“A wancan lokacin mun samu sabani da Shugaba Goodluck Jonathan a kan yadda ya kamata a tafiyar da Najeriya, don haka na cika rigata da iska na koma APC”, inji shi.
Wasu ’yan Najeriya dai na ganin rashin akida da son mulki ta kowane hali ne ke sanya ’yan siyasa sauya sheka, ko da yake Gwamna Tambuwal ya kare kansa da cewa jam’iyyun Najeriya kaf ba su da akida.