✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Abin da ya sa na bar tuki da dare’

Wannan direba mai suna Muhammadu Yusuf ya ce ya dade bai kunna fitilar motarsa ba, wato ba ya yin tuki bayan rana ta fadi. Aminiya…

Wannan direba mai suna Muhammadu Yusuf ya ce ya dade bai kunna fitilar motarsa ba, wato ba ya yin tuki bayan rana ta fadi. Aminiya ta gana da shi. Ga yadda hirar ta kasance:

g Muhammad Yusuf, Tudun Wada ZariyaAminiya: Wacce irin bauta ka yi ko wacce irin wahala ka sha don a koya maka mota?
Da farko dai sunana Muhammadu Yusuf, ni Bazazzagi ne. Kuma na kwashe shekara 21 ina tuki. Yadda aka yi na koyi tuki shi ne, ina tashi daga Tudun Wadan Zariya na nausa a kafa har cikin Ganuwa wato cikin Unguwar Juma da ke birnin Zazzau don in wanke motan mai gidana sannan in jira, idan ya fito mu tafi aiki. Har ta kai da ina karbar makullin motar na wanke sannan in kunna ta yi dumi kafin maigidana ya fito mu tafi aiki. Lokacin ina da shekara 16, ina bin shi ne ranakun Asabar da kuma Lahadi, ranar da ba makarantar boko. Amma saboda matsalar kudin makaranta, sai na bar makarantar sakandare ina aji biyu na koma bin mota gadan-gadan.
 Aminiya: Shekara nawa ka yi kana koyon kafin ka fara tuki?
Na shekara uku ina koyo. Na yi shekara biyar ina kare-ba-lasi, wato na iya mota amma ban da lasisi. Daga nan sai na samu motar safarar jama’a wato motar haya bas ina daukar fasinja daga dan-Magaji zuwa kasuwa a mota kirar Nissan-Datsun C20.
Aminiya: Shin a yanzu yaran da suke koyan aiki a wurinka, suna yi maka irin ladabin da kayi?
Cafdi-jam inji mata, ai ko rabin bautar da na yi ba za su yi ba. Domin kannen abokaina ne kuma abin ya hadu da zamani inda yara ke son jikinsu kamar kwai. Wani lokaci in na aike su, sai su yi ta yin guna-guni sannan in na sallame su da yamma shi ke nan sun kama gabansu.
Aminiya: Akwai wani abin mamaki da ya taba samun ka, ko na hadari a wannan aiki?
Eh, na sha wuya sosai domin na kusa rasa rai na. Abin ya faru ne a Zariya lokacin ina safarar dalibai daga Kwalejin Horar da Malamai da ke Kongo Zariya, ina tsammanin na dauki dalibai ne, ashe barayi ne. Muna tafiya sai suka sa waya wato kebur suka shake ni daga baya suka tafi da motar. Bayan ni kuma na sume a kusa da garin Dogarawa. An jima sannan na farfado a gidan mu.
Aminiya: Idan ka samu kaya da daddare za ka dauka, tun da yanzu kana da mota kirar 404 Peugeot wato a-kori-kura?
Ai wuyar da na sha ya sa na shiga taitayi na. Kullum idan karfe biyar ta yi na tashi aiki, kuma ko nawa za a biya ni, ba zan dauka ba. Ai na dade ban kunna fitilar mota ba don na yi tukki da daddare. (dariya).
Aminiya: Mene ne kirarin irin wannan mota taka wato a-kori-kura?
Ana yi mata kirari da cewa: Fijo 404, ko kin tsufa kina yiwa yaro aure.